Amfani da jami’an tsaro:

Abu na farko dai dole ne kungiyoyi su yi aiki tare da yansanda, NSCDC, da jami’an tsaro na sirri wajen tsara tsare-tsaren tsaro a ranar da za su buga wasa, domin kuwa Bahaushe na cewa, “tun za a, ake shiri ba sai an dawo ba”, hakazalika yana da mahimmanci a tura isassun masu aikin kwantar da tarzoma (ba yansanda kawai ba) don sa ido kan magoya baya, lura da wuraren shiga/fita, da kuma taimakawa wajen rage turmutsitsi yayin wasa.

 

Amfani da CCTV:

Yawancin filayen wasa na gasar NPFL ba su da isasshen tsarin kyamarar CCTV, a cikin filayensu cewar bincike, samar da kyamarori masu sa ido na iya rage tashin hankali a cikin filayen wasa domin idan an ga wani motsi da ba a yarda dashi ba sai akai dauki da wuri.

 

Shingaye:

A tabbatar da cewa akwai shingen tsaro tsakanin yan kallo da cikin filin wanda ke hana saurin shiga filin wasa, bincike ya nuna wasu filayen gasar NPFL ba su da wani shamaki tsakanin yan kallo da filin wasa, hakazalika akwai bukatar raba magoya bayan kungiyoyin dake buga wasa zuwa mabanbantan wuraren zama, wannan yana rage rikici kai tsaye.

 

Matakan Ladabtarwa Masu Tsauri:

Hukumar NPFL ta riga ta sanya takunkumi mai tsanani ga Kano Pillars bayan wani tashin hankali da aka yi a wasanta da 3SC inda akaci kungiyar tarar Naira miliyan 9 da rabi, rage maki da kwallaye, da kuma rufe filin wasansu na gida a yanzu.

 

Hukunta Laifuka:

Ya kamata a gano wadanda suka mamaye filin wasa ko suka kai hari ga yan wasa da jami’ai (ta hanyar CCTV) kuma a gurfanar da su a gaban kuliya, wannan zai rage rikici a cikin filayen wasa.

 

Wayar Da Kai:

Akwai bukatar ci gaba da ilmantar da magoya baya kan halaye masu kyau, hatsarin tashin hankali, da kuma girmama jami’an wasa, kungiyoyi da NPFL za su iya gudanar da bita na magoya baya, amfani da kafofin sada zumunta, da kuma amfani da kungiyoyin magoya baya.

 

Rahoton Wasanni:

Bayan kowace wasa da aka buga akwai bukatar a gabatar da cikakken rahoto akan yadda wasan ya gudana, ta hakanan Za’a iya gano wuraren da suke bukatar gyara domin gyarawa kafin buga wasan gaba, hakazalika za a iya gano wanda ya nuna halayen rashin da’a a wasan domin a hukunta shi.

 

Jawo Hankalin Matasa:

Yawancin abubuwan tashin hankali suna faruwa ne da saka hannun matasa, saboda a cikinsu ne ake samun magoya baya masu zuciya da saurin fusata, akwai bukatar a nuna masu wasan kwallo WASANE BA FADA BA, mahukunta su shiga makarantu, majalisun matasa, da shugabannin al’umma domin sanar dasu ilimin kwallon kafa don koyar da girmamawa, wasa mai kyau, da kuma nusar dasu illolin tashin hankali.

 

Inganta Tsarin Shiga Filin Wasa:

Ayi amfani da hanyoyin zamani musamman na dijital wajen bayar da tikitin shiga filayen wasa da kuma guje wa cunkoso, idan da hali ana iya saka bayanan duk wanda ya shiga filin wasa wanda zai sa idan wani ya aikata laifi zai yi saukin kamawa ga hukuma.

 

Sakon Neman Afuwa Ga Jama’a Da Jagoranci:

Shugabannin kungiyoyi (kamar Ahmed Musa na Pillars) ya kamata su ci gaba da yin kira ga jama’a game da illar tashin hankali, amma kuma suyi hakan ta hanyar da magoya baya zasu gamsu kuma su fahimci abinda ake bukatar su Sani, Musa ya riga ya nemi afuwa a bainar jama’a kuma ya yi alkawarin daukar mataki.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nazari Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna? November 16, 2025 Wasanni Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca November 15, 2025 Wasanni Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi November 15, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta gwabza da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a wasan ƙarshe na tantance wakilin Afrika a share fagen Gasar Cin Kofin Duniya na 2026. Wasan zai ɗauki hankali zai gudana ne a ranar Lahadi a sabon filin Prince Moulay Abdellah da ke Rabat, Morocco, inda za a tantance ƙasa ta ƙarshe daga Afrika da za ta shiga matakin share fagen gasar Kofin Duniya.

Nijeriya ta samu gurbin wasan ƙarshe bayan da ta lallasa Gabon da ci 4-1 a ranar Alhamis, sakamakon da ya ƙarfafa matsayin tawagar wajen sake samun martabarta a nahiyar. A ɗaya ɓangaren, DR Congo ta samu nasarar da ta ba ta gurbin wasan ƙarshe ne bayan da ta doke Kamaru da ci 1-0, inda kyaftin Chancel Mbemba ya zura ƙwallo a mintoci na ƙarshe.

Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

A yanzu za a fafata ne tsakanin ƙasashen biyu waɗanda ke neman damar ƙarshe ta wakiltar Afrika a gasar share fagen shiga Kofin Duniya da za a yi a Mexico, Amurka da Kanada. Duk wata gazawa zata ƙare burin kowace tawaga, yayin da nasara za ta buɗe musu ƙofar shiga manyan gasannin duniya.

ADVERTISEMENT

Wasan na Lahadi zai kasance mai cike da zafi da taka tsantsan, domin dukkan ƙungiyoyin sun shiga Morocco da burin tabbatar da cewa su ne za su samu tagomashi a wasan share fagen, wanda zai zama matakin farko na zuwa babban gasar ta 2026.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati November 14, 2025 Manyan Labarai Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 November 13, 2025 Wasanni Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25 November 13, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
  • Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi
  • Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika
  • EU ta bukaci Isra’ila ta dauki mataki don kawo karshen tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan
  • Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe
  • Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati
  • Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana
  • Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya
  • Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25