Aminiya:
2025-11-14@14:04:43 GMT

Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin Tarayya

Published: 14th, November 2025 GMT

Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa ci gaba da cin ganda da ake samu daga fatar shanu na barazana ga masana’antar fata ta Najeriya wadda darajarta ta kai kusan Dala biliyan biyar.

Yayin jawabi a taron ƙaddamar da yaƙi da cin ganda da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja, Darakta-Janar na Hukumar Bincike da Ci gaban Kayan Masana’antu, Farfesa Nnanyelugo Ikemounso, ya ce wannan dabi’a tana hana masana’antu na cikin gida samun muhimman kayayyakin da ake buƙata wajen samar da fata da kuma fitar da ita ƙasashen waje.

Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030

Ikemounso ya ce kasuwar kayan fata ta Najeriya ta kai darajar dala biliyan 2.79 a shekarar 2024, kuma ana hasashen za ta haura zuwa dala biliyan 4.96 nan da shekarar 2033.

Sai dai ya yi gargadin cewa ci gaba da karkatar da fata zuwa yin ganda na iya kawo cikas ga wannan ci gaban.

Ya ce, “Daga mahangar tattalin arziki da masana’antu, fatar shanu na ɗaya daga cikin muhimman kayan masarufi a Najeriya. Ƙasarmu na da masana’antar fata mai ƙarfi wadda ke da babbar damar samar da ayyukan yi, samun kuɗaɗen waje, da kuma ƙara gudummawa ga GDP.”

“A shekarar 2024, kasuwar kayan fata ta Najeriya ta kai darajar dala biliyan 2.79, tare da hasashen ta kai dala biliyan 4.96 nan da 2033.”

“Abin takaici, ci gaba da karkatar da fata zuwa cin ganda yana hana masana’antunmu samun ingantattun kayan masarufi, yana raunana sashen yin fata da sarrafa ta, kuma yana rage matsayin Najeriya a kasuwar fata ta duniya.”

A cewarsa, darajar sarkar fata ta duniya ana kiyasta ta tsakanin dala biliyan 420 zuwa dala tiriliyan 1, kuma idan aka yi kyakkyawan tsari sannan aka inganta kayan aiki, Najeriya na iya ƙara samun kaso mai yawa daga wannan kasuwa.

Shugaban ya ce amma wannan gangami ba ya nufin hana ’yan Najeriya cin ganda, sai dai don tabbatar da cewa fatar shanu da ta sauran dabbobi ana karkatar da su zuwa amfani na masana’antu domin amfanin ƙasa baki ɗaya.

Ana ɗaukar masana’antar fata ta Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan sassan tattalin arzikin da ba na man fetur ba, wadda ke da damar zama babbar hanyar samun kuɗaɗen fitar da kaya da kuma samar da ayyukan yi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: fata ta Najeriya dala biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aiwatar da harajin shigo da man fetur da dizal na kashi 15, wanda a baya aka amince da shi domin daidaita farashin shigo da kayayyaki da yanayin kasuwa.

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NMDPRA) ce, ta sanar da hakan a wata sanarwa da Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a, George Ene-Ita, ya sanya wa hannu.

Yadda na yi asarar N120m a gobarar Singa — Ɗan Kasuwar Kano MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC

Harajin ya janyo cece-kuce, inda wasu ke ganin zai kare matatun gida, yayin da wasu ke cewa hakan zai ƙara tsadar kayayyaki sannan ya tsauwala wa talakawa.

“Hukumar na shawartar ’yan kasuwa da su guji ɓoyewa ko sayar da mai da tsada ba bisa ƙa’ida ba.

“Harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal ba zai ci gaba da aiki ba,” in ji sanarwar.

NMDPRA ta tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da dizal a faɗin ƙasar nan, kuma babu ƙarancin mai da zai sanya dogayen layuka a gidajen mai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA
  • Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal
  • Gwamna Nasarawa Ya Ce Za Su Samar da Masana’antu Don Ayyukan Yi
  • Kenya: An gano tarin zinari da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 a yammacin kasar
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya
  • Jihar Jigawa Za ta Kashe Sama da Naira Biliyan Daya Domin Inganta Ayyukan Wutar Lantarki
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Ka’idoji Ga Samar da Injinan Noma a Najeriya
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Filin Jirgin Sama Na Kano
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar