Tanzania: MDD Ta Yi Kira Da A Yi Bincike Akan Daruruwan Mutanen Da Aka Kashe Sanadiyyar Rikcin Zabe
Published: 12th, November 2025 GMT
A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a watan karshe.
Wannan kiran na MDD ta zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Tanzania su ka tuhumi wasu daruruwan mutane da cin amanar kasa saboda Zanga-zangar kin amincewa da zabe da su ka yi.
Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama a karkashin MDD Volker Turk ya ce; Da akwai Alamar cewa gwamnatin kasar ta Tanzania tana kokarin batar da dalilai abinda ya faru.
Da akwai rahotanni da suke nuni da cewa jami’an tsaro suna kokarin dauke gawawwakin wadanda aka kashe daga dakunan ajiyar gawawwaki na asibitoci domin batar da su.
Turk ya kira yi jami’an gwamnatin kasar ta Tanzania da su mika gawawwakin wadanda aka kashe a sanadiyyar rikicin zaben ga iyalansu domin binnewa.
Turk ya ce; Da akwai rahotanni da suke nuni da cewa iyalan wadanda aka kashe suna yawo ko’ina,a tsakanin ofisohin ‘yan sanda da asibitoci domin gano gawawwakin dangi da ‘ya’yansu.
Jam’iyyar adawa ta Chadema ta ce adadin wadanda aka kashe din sun kai 2,000 a cikin kwanaki uku da su ka biyo bayan zabe.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Zama Memba A Kungiyar Tattara Bayanai Na Ilimomi Da Kere-kere Ta Duniya ( ISKO) November 12, 2025 Iran: Ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin November 12, 2025 Araghchi: Matsalar Yammacin duniya ita ce ci gaban kimiyyar Iran ba makaman nukiliya ba November 12, 2025 Sheikh Qassem: Kawar Da Hizbullah Ne Babban Burin Isra’ila A Lebanon November 12, 2025 Masar Da Sudan Sun Jaddada Wajabcin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin November 12, 2025 Venezuela: Maduro Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tsaron Kasa Mai Cikakkiyar Kariya November 12, 2025 UNICEF: Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza November 12, 2025 Ministocin harkokin wajen kasashen yamma sun yi Allah wadai da ta’asar RSF a El Fasher Darfur November 11, 2025 Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya November 11, 2025 Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wadanda aka kashe
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar NLC A Najeriya Ta Shirya Zanga-Zanga Kan Matsalar Rashin Tsaro A Fadin Kasa
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) a najeriya ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar kasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga sakon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar a ranar 4 ga watan. Kungiyar ta nuna damuwarta kan karuwar hare-haren ƴan bindiga da satar mutane da ke ci gaba da addabar al’umma.
NLC ta mayar da hankali musamman kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana da ke Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, inda ta bayyana mamaki cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin.
Ta ce wannan lamari ne mummunan kuma abin takaici da ya kamata a bincike shi sosai tare da gurfanar da duk masu hannu a ciki. Ƙungiyar ta zargi gwamnati da gaza daukar matakan da suka dace wajen kare rayukan dalibai a makarantu.
NLC ta ce dole ne gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa ta kammala bincike game da janye jami’an tsaro daga makarantar da aka kai harin, tare da ladabtar da masu laifi. A cewarta, rashin tsaron da ake fuskanta ya zama barazana ga rayuwa, da ilimi da ci gaban kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Duniyarmu A Yau: Iran Da Kokarin Juyin Mulkin Amurka A Yakin Kwanaki 12, Wa Ya Sami Nasara? December 12, 2025 Pezeshkian: Duniya Tana Bukatar Amintaccen Madogara, Zaman Lafiya Da Kuma Hadin Kai December 12, 2025 Iran Zata Dauki Bakoncin Taro Dangane Da Kasar Afganistan Da Tsaron Yankin December 12, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut December 12, 2025 Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba December 12, 2025 Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026 December 12, 2025 Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa December 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci