2025-11-12@18:21:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4703
«sauran kasashen»:
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka tana shirin kafa sanssanin soji don aikewa da dubban dakaru zuwa iyakar Isra’ila da yankin Gaza, adaidai lokacin da ake fargabar wata sabuwar kasada da kuma sha’awar taimakawa gwamnatin mamaya wajen karbe ikon kula da yankin a nan gaba. Masharhanta na ganin wannan shirin yana zuwa ne saboda irin bakin jini da Isra’ila ta yi a duniya bayan kisan kare dangi da ta yi a yankin Gaza, da ta fara tun daga watan Oktoban shekara ta 2023, wannan yasa telaviv ta bukaci abokiyarta ta ci gaba da aiwatar da aniyarta. Ana sa bangaren jami’an gwamnatin falasdinu sun yi gargadin cewa duk wani mataki da zaa dauka na kokarin canza wani dan mamaya da wani,...
Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Mohammad Bin Salman a wata ziyara da suka kai birnin Riyadh a baya bayan nan. Wannan sakon yana nuna irin kokarin da ake yi ne na ganin an daidaita da kuma kara yin aiki tare tsakanin Riyadh da Tehran, bisa la’akari da irin tattaunawa da aka yi a shekarar bara, diplomasiya ta addinin dake kewaye da aikin hajji na shekara –shekara ta kasance mai muhimmanci don samar da zaman lafiya . Ali reza Rashidiyan shugaban hukumar aikin hajji ta kasar iran ya kai ziyara kasar saudiya ne domin rattaba hannu kan shirye- shiryen jerjejeniyar aikin hajji da zaa yi a...
Kasashen Iran da Pakistan sun yi kira da a yi aiki tare da ya hada da kara dankon zumunci tsakanin yan majalisar domin tunkarar babban makiyinsu, kuma sun yi tir da matakin kai hare-hare da Isra’ila ke yi da kuma ta’adanci a yankin A wani bayani da suka fitar a wata ganawa da suka yi a bayan taron yan majalisu da aka gudanara a yau laraba a birnin Islam Abad, mataimakin kakakin majalisar dokokin kasar iran Ali Nikbad da takwaransa na kasar Pakistan sardar ayaz sadiq sun jadda game da matsayin kasashen na irin gudunmawa da suke badawa a yankin dakuma lammuran da suka shafi kasashen musulmi Nikbad ya bayyana gamsuwarsa game da sanin ya kamatan kasar Pakistan kuma yayi...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da twakaransa na kasar Rasha Sergei lavrov inda suka mayar da hankalin kan batutuwan da suka shafi yankin dama na kasa da kasa Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta bayyana cewa Iraqchi ya jaddada game da muhimmancin zaman lafiya a yammcin Asiya lokacin da yake ishara game da rikicin baya bayan nan da ya faru tsakanin Pakistan da Afghanistan, Da ya koma bangaren batun falasdinu kuma Araqchi ya soki matakin da Amurka da kasashen turai suka dauka a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na gabatar da daftarin kuduri na neman a tilasta tura dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza na falasdinu, yace wannan kuduri yayi hannun...
Babban abin lura a nan shi ne irin alfanun da Nijeriya za ta samu tare da sauran kasashen Afrika daga wannan bikin baje koli. Na farko dai Nijeriya da sauran kasashen Afirka za su kara kaimi wajen noman irin waɗannan amfanin gona domin fitar da su zuwa Sin, hakan kuwa zai kara samar da aikin yi ga dubban ‘yan Nijeriya, abin da zai habaka kudaden shiga ga kasa. Alfanu na biyu kuma shi ne fadada damar ingantawa da kara daga darajar irin wadannan amfanin gona da Nijeriya ke samarwa. Sannan kuma akwai batun bunkasa dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka. Sabo da haka wannan irin lamari na bude kofar cudanya tsakanin Sin da sauran kasashen...
Mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da jawabi yayin taron kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu da aka gudanar jiya Talata, inda ya yi kira da a inganta mika mulki cikin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu. Sun Lei ya ce, Sin ta bukaci dukkan bangarorin kasa da kasa da su mayar da hankali kan yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, kana su dakatar da ayyukan da ka iya haifar da tashe-tashen hankula, musamman ma a hana amfani da karfin tuwo da kuma guje wa karuwar rikice-rikice. Sun Lei ya kara da cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, mabudin warware matsalolin kasashen Afirka yana hannun Afirka. Duk wata mafita ya kamata ta...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar. Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse. Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada da samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da ruwan sha. Sauran sun hada da kewaye asibitocin domin inganta yanayin aiki da al’amuran tsaro. Dakta Kabiru Ibrahim ya kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa kokarinta na tallafawa harkokin kiwon lafiya a jihar.
Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki,...
Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya. Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu An shigar da ƙarar ne mai lamba FHC/ABJ/CR/610/2025, dangane da wasu rubuce-rubuce da matashin ya wallafa a shafinsa na X a watan Oktoban 2025. A cewar DSS, waɗannan rubuce-rubuce sun nemi a kifar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki tare da nuna goyon baya ga sojoji su karɓi mulki a ƙasar. Lauyan...
Daga Khadijah Aliyu Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Jagorancin Shirin Ilimi da Ƙarfafa Matasa a Arewa maso Yammacin Najeriya (EYEPINN) wanda kungiyar Tarayyar Turai ke daukar nauyinsa domin fadada damar samun ingantaccen ilimi da kuma karfafa gwiwar matasa a yankin. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Kano, karkashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda. Yayin jawabinsa, Dakta Makoda ya bayyana shirin EYEPINN a matsayin “Alƙawari mai Manufa”, yana mai cewa manufar shirin ita ce cike gibi a fannin ilimi, karfafa haɗin kai, da kuma baiwa matasa kwarewar da ta dace domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Ya ce sabon kwamitin da aka kaddamar zai yi jagoranci kan dabaru,...
A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a watan karshe. Wannan kiran na MDD ta zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Tanzania su ka tuhumi wasu daruruwan mutane da cin amanar kasa saboda Zanga-zangar kin amincewa da zabe da su ka yi. Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama a karkashin MDD Volker Turk ya ce; Da akwai Alamar cewa gwamnatin kasar ta Tanzania tana kokarin batar da dalilai abinda ya faru. Da akwai rahotanni da suke nuni da cewa jami’an tsaro suna kokarin dauke gawawwakin wadanda aka kashe daga dakunan ajiyar gawawwaki na asibitoci domin batar da su. Turk ya kira...
A yau Laraba ne aka sanar da zaman Iran memba a cikin wannan kungiyar ta ( ISKO) wacce aka bude reshenta a cikin kasa tun a 2011. Farfesa Rahmatullah Fattahi ne ya bude reshen kungiyar ta ” Ilimomin Tattara Bayanai Da Kere-Kere” wacce kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa 2019. An sami tsaiko a yadda kungiyar take tafiyar da ayyukan nata, saboda bullar Korona, amma ta ci gaba da aiki a karkashin wani tsari na musamman ( IranDoc.). Aikin wannan cibiyar shi ne tsara gudanar da nazarori da bincike na ilimomi mabanbanta da kuma hana yin maimaici akansa. A halin yanzu da akwai mutane 20 da suke aiki a karkashin wannan kungiyar daga asalin su 20...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025 Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025 Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan Trump November 3, 2025
Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka. Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne domin haɓaka inganci a ayyuka da ƙarfafa ƙwararru da tabbatar da bin ƙa’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata. A jawabinta, Manajiyar Darakta ta KNUPDA, Arc. Hauwa Hassan Tudun-Wada, ta bayyana horon a matsayin muhimmiyar hanya ta gina al’adar ladabi da biyayya da nagarta a cikin ma’aikatan gwamnati. Ta yaba da jajircewa da himmar ma’aikata wajen halartar shirin, inda ta jaddada cewa fahimta da bin dokokin...
Pars Today – Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, yana Allah wadai da fashewar da ta faru a babban birnin Pakistan, ya ce ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin kuma fuskantar wannan mummunan lamari yana buƙatar haɗin gwiwa, ƙuduri, da haɗin kai daga dukkan ƙasashe. Reza Amiri-Moqaddam, Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, a ranar Talata, yayin da yake Allah wadai da fashewar ta’addanci a birnin Islamabad – wanda ya kashe mutane 12 tare da raunata aƙalla wasu 30 – ya ce: “Ta’addanci makirci ne na matsorata waɗanda ke neman wargaza yankinmu da kuma sanya cikas a hanyarsa ta zuwa ga ci gaba mai ɗorewa.” A cewar jaridar Pars Today, jakadan Iran a Pakistan ya jaddada cewa: “Wannan...
Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyed Abbas Araghchi, ya ce masana’antar nukiliya yanzu ta zama babban fanni kuma tana kara samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban-daban. Sabanin yadda ake ganin cewa wannan masana’antar ta takaita ne ga tace uranium, ya kara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannoni daban-daban na rayuwar mutane, ciki har da maguguna, fannin kiwon lafiya, muhalli, noma, da masana’antu a cibiyoyin Makamashin Nukiliya ta Iran. A lokacin ziyarar da ya kai wa Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Araghchi ya jaddada cewa fasahar nukiliya tana nan a dukkan fannoni tana ba da gudummawa ga ci gaban fannoni daban-daban. Ya kara da cewa wannan ilimi da fasaha suna hanzarta ci gaban kimiyya...
Babban Sakataren Hezbollah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa “Amurka, ta hanyar wakilanta na Isra’ila, tana neman kawar da karfin gwagwarmayar Lebanon da kuma ba sojojin kasar makamai don fuskantar Hezbollah,” yana mai jaddada cewa manufar wannan matakin shine “kawar da karfin soja da duk wani karfi fadin Lebanon domin Isra’ila ta ci gaba da cin karenta babu babbaa duk inda ta ga dama a cikin kasar.” Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa “An kafa Hezbollah ne bisa ka’idojin jihadi, kare mutunci mutunci, da alfaharin Lebanon, da goyon bayan Falasdinu,” yana mai cewa “daga 2000 zuwa 2023, mun kasance cikin yanayi na tsoro.” Ya bayyana cewa yakin baya-bayan yana a matsayin shinge ga mamayar Isra’ila, wanda ya tsayar da...
UNICEF ta yi gargadin cewa Isra’ila na hana shigar da muhimman kayan aikin da ake buƙata don allurar rigakafi a Gaza, wanda hakan ke kawo cikas ga ƙoƙarin isa ga yara a yankin da yaƙi ya daidaita. Hukumar ta ce kayayyakin, ciki har da sirinji da ake amfani da su don allurar rigakafi na yau da kullun da kwalaben madarar jarirai, har yanzu suna nan a wuraren bincike, duk da ci gaba da tsagaita wuta da kuma ƙaruwar buƙatun jin kai. UNICEF ta bayyana cewa a halin yanzu tana gudanar da Shirin allurar rigakafi ga yara ‘yan ƙasa da shekara uku, waɗanda da yawa daga cikinsu sun rasa allurar rigakafi na yau da kullun a cikin shekaru biyu da suka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar. A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu. Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu daidaikun mutane maimakon tsaron alummar kasa gaba daya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga...
Ban da wannan kuma, game da batun cewa kasashen kungiyar EU suna shirin cire na’urorin kamfanonin sadarwa na kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin suna aiwatar da ayyukansu bisa doka a nahiyar Turai na dogon lokaci, wadanda suka samar da kayayyaki da hidimomi masu inganci ga jama’ar Turai, tare da samar da muhimmiyar gudummawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da samar da ayyukan yi a nahiyar. Kasar Sin ta kalubalanci kungiyar EU da ta samar da yanayin gudanar da ciniki cikin adalci da rashin nuna bambanci ga kamfanonin kasar Sin don magance wargaza amannar da kamfanonin suka yi wa nahiyar Turai kan zuba jari. (Zainab Zhang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin...
Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kyautata harkokin masana’antu. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta ba da taimako wajen shigar da mambobin WTO su 130 cikin yarjejeniyar samar da sauki a ayyukan zuba jari domin neman ci gaba, ta yadda kowa zai cimma moriyar sakamakon dunkulewar duniya cikin adalci. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Ya...
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Najeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda)”, inda aka haɗa...
Shugaban tsaron kasar ta Iran ya yi watsi da rahotannin da ake yayatawa cewa iran ta bude wasu hanyoyin tuntuba da Washington, yana mai jaddada cewa ba a isar da wani sabon sako ga Amurka ba. Ali Larijani ya jaddada cewa fifikon Iran a koyaushe shi ne dage takunkumin da aka kakaba mata, wanda ya bayyana a matsayin kokarin diflomasiyya na gwamnatin kasar. Duk manufofin gwamnati da kokarin diflomasiyya suna mai da hankali ne kan kawo karshen takunkuman,” in ji shi. Ya bayyana ce sakon da ake yayatawa ya samo asali ne daga shawarwarin da akayi a baya, amma Amurka ba ta nuna sha’awar cimma yarjejeniya ba. Wannan bayanin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da...
Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita. Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu sama da 620, wanda hakan ya zama keta dukkan ka’idoji da kudurori na kasa da kasa da aka amince da su. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna Allah wadai da karya wannan yarjejeniya da aka yi akai-akai kuma muna daukar ‘yan mamayar da alhakin sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro da na jin kai. Muna jaddada cewa ci gaba da wannan lamari yana barazana ga yarjejeniyar...
‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Kimanin ‘yan kasar miliyan 21 ne aka tantance domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar dokoki 329, Wadannan za su zabi shugaban kasa kuma su amince da sabuwar gwamnatin, wadda sabon firaminista zai kafa. A cewar jami’an zabe, za a sanar da sakamakon cikin sa’o’i 24 bayan kammala zaben. Firaminista Mohammed Shia al-Soudani ya bayyana zaben a matsayin wanda ya gudana “a cikin yanayi mai aminci da kwanciyar hankali,” yana yabon jami’an tsaro saboda kiyaye tsarin. Al-Soudani, wanda aka zaba a shekarar 2022, yana neman wa’adi na biyu kuma zai bukaci samun rinjaye a majalisar. A Iraki,...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi a karatu na farko da wani kudiri da aka gabatar mata na yin hukunci kisa kan wadanda aka kama da laifin ta’addanci a kasar. Dan majalisar kasar mai tsattsauran ra’ayi, Itama Ben Gvir ne ya gabatar da kudirin, inda ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyarsa idan har ba a amince da kudurin ba. Hukumomi a Falasdinu sun kira kudurin dokar da wani matakin zalunci da ake yunkurin dauka kan falasdinawa. Matakin a cewar Hamas wani yunkuri ne na halatta kisan gillar da aka yi wa al’ummar Falasdinawa da ke zaune a karkashin mamayar Isra’ila,” in ji Hamas a cikin wata sanarwa da ta...
Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500. Wannan shi ne karo ba adadi da wannan gidauniyar ta Kogunan Kasar Hausa kuma shugaban hukumar Samarda Lantarki a yankunan Karkara Alhaji Abba Aliyu ta gudanar. An raba kayan Solar guda 500 da kuma kudin fara sana’o’in hannu ga wadanda suka sami horo a karkashin wannan gidauniya. Mataimakin Shugaban wannan gidauniya Suleiman Aliyu Abubakar ya bayyana cewa sama da shekara suna rana kyayyakin sun hada da solar domin kawo karshen matsalar wutar lantarki. Suleiman Aliyu Abubakar wanda ya wakilci MD Abba Aliyu a wajen taron yace Kayayyakin sun hada da fanka da kayan caji da na...
Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya. Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi Sojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin...
Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya. Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi Sojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin...
Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa. Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron dan adam , kuma ya bayyana cewa an shirya harba tauraron dan adam guda uku na: Zafar, Paya, da Kowsar a farkon hunturu. A cewar Pars Today, ya yi Ishara da hadin gwiwar da Iran ke yi da wasu kasashe a fannin sararin samaniya, yana mai ambaton ayyukan hadin gwiwar da China kan ayyukan hadin gwiwar bincike da kasashen mambobin ECO. Wannan ayyukan hadin gwiwar...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori. Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin yana cikin shirin “Gwamnati da Jama’a” wanda ke karfafa al’umma, rage matsalolin sufuri da kuma karfafa harkokin kasuwanci. Ya ce shirin ya kunshi gina manyan hanyoyi guda shida a sassan jihar, masu tsawon kilomita 179 gaba daya, a kan kudin da ya haura Naira Biliyan 81. Hanyoyin sun hada da Mallam Madori zuwa Gari Uku zuwa Kanya Babba zuwa Malorin Kasim, ta ratsa ta...
Tawagar lauyoyin Trump ta ce an ɓata masa suna da mutunci, inda ta bayyana cewa BBC ta yi hakan ne don siyasa. Trump ya taɓa shigar da ƙorafe-ƙorafe makamantan wannan a kan wasu manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka, ciki har da ABC, CBS, da The New York Times, bisa zargin yaɗa labaran ƙarya a kansa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kasashen Ketare An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga October 16, 2025 Kasashen Ketare Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto October 7, 2025 Kasashen Ketare Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa? October 4, 2025
Shugaban kasar Amurka ya yi wa ma’aikatan filayen jiragen sama masu sa idanu akan sauka da tashin jirage, barazana. Ma’aikatan da suke sanya idanu a cikin hasumiyoyin dake filayen jiragen sama da dama ne a Najeriya su ka dakatar da ayyukansu saboda rufe ayyukan gwamnati da aka yi a kasar, domin ba za su sami albashi ba. Shugaba Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta “Truth Social” cewa:, Ba ni jin dadin mutanen da ba su yin wani aiki sai korafi,alhali suna sane da cewa za a basu dukkanin hakkokinsu.” Trump ya kuma yi wa ma’aikatan da ba su dakatar da ayyukansu ba alkawalin ba su kyautar kudi Dala 10,000 kowanensu. Rufe ayyukan gwamnatin kasar ta Amurka wanda ake...
Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba. Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike. Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da...
Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni 9 Da Aka Zartarwa Da Hukuncin Kisa Shekaru 30 A Baya
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa. “Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da kamfanin man fetur na Shell yake yi. Wannan kiran daga kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron kare muhalli na duniya a kasar Brazil. Shugaban kungiyar ta “Amnesty International” a Nigeria, Isa Sunusi ya bayyana cewa; Duk da cewa afuwar da gwamantin ta yi musu ci gaba ne,amma masu rajin kare muhallin na...
Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR, ta rasu tana da shekaru 89 a duniya. Iyalai sun tabbatar da cewa ta rasu ne da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Litinin, bayan fama da doguwar jinya. Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jallo Ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa kuma Hakimin Shagari, Kyaftin Bala Shagari (mai ritaya), shi ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da aka fitar daga Sakkwato. Sanarwar ta ce: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Muna baƙin cikin sanar da rasuwar Hajiya Sutura Shehu Shagari, mata ɗaya tilo da da ta rage wa tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa November 10, 2025 Daga Birnin Sin Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin November 10, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo November 10, 2025
Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji da aka kai mata. Kakakin yayi suka mai tsananin ga kamalan da shugaban Amurka yayi dake tabbatar da hujjoji dake nuna cewa yana da hannun dumu dumu wajen kai mata harin soji, wannan yana daya daga cinkin bayyanannun hujoji dake tabbata da taka rawar Amurka wajen kai mata hari. Haka zalika ya nuna cewa iran ta mikawa kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya wadannan kalaman...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar, inda ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen kara inganta nukiliyar masana’antu, kuma yace kasarsa ba za ta taba yin watsi da shirin ta na nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba. Haka zalika ya jinjinawa iran game da irin gagarumin ci gaban da suka samu a fasahar nukiliya, inda suka shiga bangare masana’antu da ya yadu zuwa wasu bangarori daban daban. Hukumar kula da makamashin nukiliya...
Bisa goron gayyatar da gwamnatocin kasashen Guinea da Saliyo suka ba shi, Liu Guozhong, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda kuma shi ne mataimakin firaministan gwamnatin kasar, zai kai ziyara kasashen Guinea da Saliyo daga yau Litinin 10 zuwa 16 ga watan da muke ciki. Sannan, bisa gayyatar shugaban kasar Guinea Mamady Doumbouya, Mr. Liu Guozhong zai kuma halarci bikin kaddamar da mahakar karafa ta Simandou a kasar ta Guinea, a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping. (Lubabatu Lei) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Ya Taya Ouattara Murnar Sake Lashe Zaben Shugaban Cote D’Ivoire November 10, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Halarci Bikin Bude...
Kamaru: Jagoran ‘yan Hamayya Chiroma Ya Bai Wa Gwamnati Sa’o’i 48 Da Ta Saki Dukkanin Wadanda Aka Kama Bayan Tsabe
Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.” Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira ” Nuna wariya ta kabilanci.” Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.” A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%. Shi dai...
Kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinawa ta sanar da cewa; sojojin mamayar HKI sun kashe ‘yan jarida 44 da suke a cikin sansanonin ‘yan hijira mabanbanta a yankin Gaza. Sanarwar ta ce, wannan adadin, yana a karkashin jumillar ‘yan jarida 254 da su ka yi shahada a tsawon lokacin yakin da ya fara daga watan Oktoba na 2023, zuwa watan Oktobar wannan shekarar ta 2025. Kwamitin dake kare ‘yancin aikin jaridar dake karkashin kungiyar ‘yan jaridar ta Falasdinawa, ya ce; Kashe ‘yan jarida da HKI take yi wani shiryayyen tsari ne da ya hada kai hare-hare akan sansanon ‘yan hijira da suke a kusa da asibitoci da sauran cibiyoyin da hukumar ‘yan hijirar Falasdinawa ta MDD, Unrwa take kula da su....
Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya ambaci cewa, Mutum daya ya kwanta dama, sadaniyyar harin wani jirgin sama maras matuki na HKI akan wata mota a garin al-yasariyyah,dake gundunar Saida, a kudancin kasar. Majiyar tsaro ta fada wa kafafen watsa labaru cewa, jirgin saman maras matuki ya harba makamai masu linzami guda 3 ne akan motar da hakan ya yi sanadiyyar konewarta baki daya. Dama dai ma’aikatar lafiya ta Lebanon din ta sanar da shahadar wasu mutane biyu sanadiyyar hare-hare biyu da Isra’ilan ta kai a kudancin kasar, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Tun da aka tsagaita wutar yaki a watan Nuwamba 2024, HKI take ci gaba da keta ta, ya kai dubbai. A wani labarin daga...
Pars Today – Kimanin masu jefa ƙuri’a miliyan 1.3 na Iraki sun je rumfunan zaɓe jiya, Lahadi (9 ga Nuwamba). An gudanar da wannan zaɓen na musamman kwanaki biyu kafin babban zaɓen ‘yan majalisar dokoki na Iraki, wanda za a gudanar a ranar Talata ta wannan makon (11 ga Nuwamba). An ci gaba da gudanar da zaɓen har zuwa ƙarfe 6 na yamma agogon ƙasar, bayan haka aka rufe akwatunan zaɓe ta hanyar lantarki. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar da cewa an shirya cibiyoyin zaɓe 809, ciki har da akwatunan zaɓe 4,501, a faɗin ƙasar don ranar zaɓen musamman. A wannan zagayen zaɓen, ‘yan takara sama da 7,744 daga ƙungiyoyin zaɓe 31 sun tsaya takarar kujeru...
Pars Today – Jakadan Iran a Rasha ya sanar da cewa Tehran da Moscow sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Kazem Jalali, jakadan Iran a Rasha, ya rubuta a ranar Lahadi a dandalin sada zumunta na X cewa an cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Rasha don kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Ya kara da cewa wannan yarjejeniya ta samo asali ne daga tarurrukan da aka gudanar a ranakun 6-7 ga Nuwamba a Makhachkala tsakanin shugabannin tashoshin jiragen ruwa da na ruwa, manyan jami’an gwamnati, da daraktocin manyan kamfanonin kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen biyu. A cewar Pars Today, ya kara da cewa a lokacin wannan taron, an amince da tsarin da tsarin hadin...
An ƙara rage kuɗin kujerar aikin hajjin bana zuwa aƙalla Naira miliyan 7.5 ga maniyyata daga jihohin Arewacin Nijeriya. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai. Ya ce an rage kuɗin ne sakamakon umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na yin hakan da kuma tattaunawar da suka yi ta baya-bayan nan da kamfanonin Saudiyya. A ƙarƙashin sabon farashin yanzu jihohin da ke shiyyar Borno/Adamawa za su biya Naira 7,579,0202 maimakon Naira 8,327,125 da hukumar ta sanar a baya. Mahaifiyar Minista Balarabe Lawal Abas ta rasu NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci Sauran jihohin Arewa kuma sabon farashinsu shi ne Naira 7,669,769 maimakon Naira 8,457,685 da aka sanar da...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu na musulmi. Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada muhimmancin inganta hulda da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da rabon ruwa daga kogin Harirud. Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza a watan da ya gabata, inda aka kashe mutane da dama a tashin hankali mafi muni tun bayan da Taliban ta kwace iko...
Allah Ya yi wa Hajiya Ɗayyabatu, mahaifiyar Ministan Muhalli, Balarabe Lawal Abas, rasuwa tana da shekara 93. Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da jinya, a gidanta da ke unguwar Bambale da ke birnin Zariya. Ta rasu ta bar ’ya’ya hudu da jikoki da dama. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci Ana sa ran gudanar da Sallar jana’izarta a safiyar Litinin daina nan da misalin ƙarfe 11, a gidan nata da ke Bambale, Birnin Zariya.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar a ranar Lahadi cewa adadin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen da aka gudanar ya kai kashi 82.42%, wanda ya tabbatar da sahihanci da kyakkyawan tsarin gudanar zaɓen, a cewar hukumar. Shugaban Hukumar Omar Ahmed, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa hukumar ta nuna daidaito da adalaci ga dukkan ‘yan Takara. Ahmed ya bayyana cewa hukumar ta sa ido kan tsarin zaɓe a duk faɗin jihohin ƙasar ta hanyar ƙungiyoyin da ke aiki, yana mai jaddada cewa sakamakon ya nuna jajircewar masu kaɗa ƙuri’a da kuma tafiyar da harkokin zaɓe cikin sauƙi da kuma sahihin tsari. A cikin wannan yanayi, mai ba da shawara kan harkokin shari’a na hukumar...
A taron CELAC na biyar tare da Tarayyar Turai a Colombia, shugabannin Latin Amurka sun yi Allah wadai da karuwar jibge sojojin Amurka a yankin Caribbean, suna gargadi game da tsoma bakin kasashen waje da kuma yin kira da a hada karfi da karfe wajen kare ‘yancin kai da zaman lafiya. Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya aika wa kasashe mambobin CELAC wasika yana mai kira da su yi tir da abin da ya bayyana a matsayin tsokana da neman tyar da zaune tsaye da Amurka ke yi a yankin Caribbean. Da yake magana kan hare-haren da aka kai kwanan nan kan jiragen ruwa na kamun kifi da kuma tura sojojin Amurka kusa da iyakokin ruwa na Venezuela, Maduro ya bayyana...
Ministan Lafiya na Lebanon Rakan Nasser Eddine ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, musamman a kudancin kasar, sunakara tsananta, yana mai jaddada cewa rikicin ba wai kawai ya takaita ga wani yanki ɗaya ba ne, lamari ne da ya shafi kowace gida a Lebanon.” A lokacin ziyararsa a birnin Hermel da ke arewa maso gabashin Lebanon, Nasser Eddine ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi shahada ya karu daga 23 zuwa 28 a cikin watan da ya gabata, yana mai jaddada cewa waɗannan shahidai suna da iyalai da dangi da ‘yan uwa, kuma dole ne ƙasa ta tsaya musu. Ya ƙara da cewa: “Dangane da wannan hari na Isra’ila a kan ƙasarmu, sojojin Lebanon ba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma. Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar. Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani. Ranar Foliyo Ta...
Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin da ke tsakanin Pakistan da Afghanistan wanda ya kara ta’azzara kwanan nan bayan fadan kan iyaka mai muni da ya faru. Abass Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, Mohammad Ishaq Dar, yau Lahadi, inda suka tattauna dangantakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Mista Araghchi ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yanzu tsakanin Afghanistan da Pakistan, yana mai jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, tare da taimakon kasashen yankin masu tasiri, don sasanta takaddamar da rage tashin hankali. A watan da ya...
A Labanon akalla mutane uku ne suka mutu sannan goma sha daya suka jikkata a hare-haren jiragen sama marasa matuka na Isra’ila a kudancin Lebanon, wanda ya sake nuna yadda Isra’ilar ke keta yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin suka cimma. A cewar kamfanin dillancin labarai na kasa na Lebanon (NNA), an kashe ‘yan’uwa biyu lokacin da wani jirgin saman Isra’ila mara matuki ya kai hari kan motarsu kusa da garin Shebaa. Harin ya faru ne a kan wata hanya da ta hada Ain Ata da Shebaa, a kan gangaren yammacin Dutsen Jabal al-Sheikh, wanda ya sa motar ta kama da wuta, kamar yadda NNA ta ruwaito. Wani hari na danban ya afka wa wata mota a Barashit, inda ya...
Daga Usman Mohammed Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta sake jaddada kudirinta na cigaba da horas da matasa maza da mata sana’o’in hannu domin su kasance masu dogaro da kai. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan lokacin bikin yaye matasa 160 da suka sami horo akan sana’o’in dogaro da kai, wanda kungiyar hadin kai ta kafin Hausa ta gudanar. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta bullo da shirye-shirye da nufin mayar da matasan jihar masu dogaro da kawunansu. A don haka, Gwamnan ya godewa Kungiyar bisa bada horan, tare da yin kira ga matasan da suka amfana da shirin su yi amfani da ilmin da suka samu domin zama masu dogaro da kai. A jawabinsa na marhabun...
A wani kwarya-kwaryar biki da aka yi a nan birnin Tehran an kafe Mutum-mutumin tarihi na sarkin daular Roma Velarian wanda aka kamo shi a matsayin fursunan yaki a zamanin Daular Sasaniyawa, ya kuma durkusa a gaban sarki Shahpur 1. Kafe Mutum-mutumin da aka yi, yana a karkashin jaddada matsayar Iran na cewa, al’ummarta ba ta rusunawa a gaban abokan gaba sai dai su rusuna a gabanta. A shekarar miladiyya ta 260 bayan haihuwar Annabi Isa ( a.s) ne aka yi yaki a tsakanin tsohuwar daular farisa ta Sasaniyawa da kuma daukar Roma ta gabasa, a Edessa, wanda ya kare da murkushe sojojin Romawa 70,000 sannan kuma aka kama sarkinsu Velarian aka kawo shi Iran a matsayin furusunan yaki. Har...
Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati
Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar. Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su karbi albashi ba, idan su ka yi aiki alhali ayyukan gwamnati suna a rufe. Hukumar filayen jiragen sama ta tarayyar Amurka ce ta sanar da cewa masu aikin kula da zirga-zirgar jiragen sama a hasumiyoyin dake cikin filayane jiragen sama 25 sun dakatar da aiki. Daga cikin garuruwan da tsaikon aikin ya shafa da akwai Chicago, Sanfarancisco, New York, New Rock da kuma Atalanta. Tashar...
Babban mai tattara zaɓe da hukumar ta turo, Farfesa Edogah Omoregie, kuma shugaban jami’ar Benin, shi ne ya karanta sakamakon na karshe a hedkwatar zaɓe da ke Awka. Nasarar Soludo ta nuna cewa APGA na ci gaba da daƙile siyasar yankin, tare da samun cikakken goyon bayan jama’ar jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9, 2025 Labarai Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza November 8, 2025
Charles Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA, ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba. Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi. Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445. George Moghalu na jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401. Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban...
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana. Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin...
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu. Da yake magana bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan ranar Juma’a, ya ce, “Idan aka habaka kasuwannin kan iyaka kuma ciniki da Pakistan ya ci gaba da bunkasa, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da kalubalen kan iyaka tsakanin kasashen biyu, domin mayar da yankunan kan iyaka zuwa cibiyoyin manyan ayyukan tattalin arziki zai rage fasa-kwauri da rashin tsaro, haka nan kuma zai share fagen...
Hare-haren daukan fansa da Iran ta kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi sanadiyyar janyo hasarar dala miliyan 200 Harin da aka kai wa matatun mai na Haifa na ɗaya daga cikin ayyukan da Iran ta yi a matsayin ramuwar gayya ga harin da Isra’ila ta kai a lokacin yaƙin kwanaki 12. Shirin “Lambar” a cikin ɓangarensa na “Sa ido”, ya magance wannan aikin. Waɗannan matatun mai suna daga cikin muhimman wurare na dabaru a Isra’ila, waɗanda ke cikin ɗaya daga cikin muhimman tashoshin jiragen ruwa kuma suna aiki a matsayin babbar cibiyar jiragen ruwa da ke jigilar mai zuwa ƙasar. A cewar ƙididdiga da ƙayyadaddun fasaha, matatun mai na Haifa suna da ƙarfin samar da tan miliyan 9.8 a...
Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da masu ƙara suka zayyana sun haɗa cewa, ya danganta halittar Annabi SAW da ƙasƙantun halittu (‘Ya’yan Tumkiya, da Karya, da Ƙwarƙwata), sannan kuma ya taɓa alfarmar iyayen Annabi SAW wanda a cewarsu, hakan bai dace ba a alfarmarsa fiyayyen halitta. Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba tare da ɓata lokaci ba, ta miƙa koken ga Majalisar Shura ta jihar domin fayyace gaskiyar lamari. Majalisar Shura, ta bakin Sakatarenta, Shehu Wada Sagagi, a wani taron manema labarai da ta gudanar, ta tabbatar da cewa, za ta gudanar da cikakken bincike akan zargin da aka yi wa Malamin (Abubakar Triumph). Sannan kuma, za ta gayyaci masu ƙorafe-ƙorafe da kuma Malamin domin sauraron bayanansu....
BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”. Somalia (1992–1994) Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s. A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya. Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida. Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025
Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi ya zo na daya a duniya da maki 170.80 kuma yana mataki na 4 a bangaren Olympic, A gefe...
Prime ministan kasar Iraki shiya Al-sudani ya sanar a birnin bagadaza cewa sun fara shirin kula wata yarjejeniya a hukumace da kasar Amurka, da zai kai ga ficewar sojojin kasashen waje daka kasar, daga nan zuwa wata satumbar shekara ta 2026, wanda wannan wata ishara ce ta bude wani sabon shafi a kasar na zaman tabbaci da tsaro mai dorewa. Kasar iraki na kokari wajen ganin an kawo karshen zaman sojojin mamayar Amurka dake kasar fiye da shekaru 20 da kuma tsoma bakin kasashen wajen, da ya fara daga lokacin da Washington ta shiga kasar a shekara ta 2003 domin kaddamar da hare-hare da dukkan duniya ta yi tir da shi da kuma bayyana shi a matsayin wanda ya sabama...
Rahotanni sun bayyana cewa a kasar Turkiya an fitar da hukumci kama prime ministan Isra’ila banjamin Natanyaho da wasu jami’an Isra’ila guda 37 da laifin keta hakkin bil adama da kuma yin kisan kare dangi kan alummar Gaza a lokacin yaki, Wannan yana nuna irin mataki mai tsauri na doka da aka dauka kan jami’an Isra’ila a baya bayan nan, kan laifuka yaki da suka tafka kan bil adam a yakin Gaza, da kuma karfafa kasashen duniya daukar matakin da ya dace kan zargin da ake mata na kai hare-haren kan fararen hula. Sabanin tsakanin Ankara da tel aviv ya kara tsananta ne tun bayan da ta fara kai hare-haren kan fararen hula a yankin gaza a shekara ta 2023...
Xi ya jaddada cewa, domin lardin Guangdong ya samar da sabbin damammaki da cimma sabbin nasarori, ya zama dole a ci gaba da himma wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa, da aiki da ruhin yankunan tattalin arziki na musamman, da kuma karfafa samun ci gaba mai inganci ta hanyar zurfafa gyare-gyare da bude kofa. Ya yi kira da a yi kokarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Guangdong, Hong Kong da Macao, da kuma tallafa wa inganta hadewar Hong Kong da Macao da kuma hidimta wa ci gaban kasar baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025 Daga Birnin Sin Cinikin...
Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida. Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri. Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu A yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu. Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta...
Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi. Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.” Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...
Kotun koli ta tarayyar Najeriya ta tsayar da ranar 20 ga watan nan na Nuwamba domin zama shari’ar shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara Nnamdi Kanu. Zaman shari’ar da za a yi zai mayar da hankali akan tuhumar ayyukan ta’addanci da ake zargin shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara din da aikatawa. An bai wa Kanu kwanaki shida a jere domin ya kare kansa akan zargin ta’addancin, sai dai bai iya yin hakan ba. A jiya Juma’a Kanu ya gabatar da nashi bayanin akan cewa; Ai daina daukar ta’addanci a matsayin laifi a Najeriya, domin an yi wata sabuwar dokar da ta maye gurbin tsohuwar da ake da ita akan hakan. Har ila yau Kanu ya ce babu wata madogara ta doka...
Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ne ya bayyana cewa da akwai ‘yan asalin kasashen Afirka 1,400 da suke cikin rundunonin Rasha suna tayata yaki. Ministan harkokin wajen kasar ta Ukraine, Adriy Sabiha ya ce; Moscow tana jan hankalin ‘yan Afirka akan su rattaba hannu akan wata yarjejniyar aiki, wacce take daidai da yankewa kansu hukuncin kisa. Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar na Ukraine, ya rubuta a shafinsa na X cewa; ‘yan kasashen wajen da ake dauka a cikin sojojin Rasha, ana aike su zuwa inda za a yi saurin kashe su.” Jami’an gwamnatin kasar ta Ukraine sun sha yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su hana ‘yan kasarsu yi wa Rasha aikin soja da hakan yake da...
A yau Asabar ne jirgin kasa na dakon kaya na farko daga Rasha ya iso tashar jiragen ruwa ta “Abrin” na Iran. Zuwan jigin kasan dai yana a karkashin bunkasa alakar kasuwanci ne a tsakanin Iran da Rasha. Jirgin kasan yana dauke ne da hajar kasuwanci saboda kasuwannin Iran da kuma Iraki, yana kuma dauke da kwantena 62 masu girman kafa 40. Shi dai wannan jirgin kasan ya taso ne daga wani yanki mai nisan kilo mita 900 daga Arewacin birnin Moscow, ya kuma ratsa ta kasashen Kazakhstan da Turkmenistan, sannan ya shigo Iran. Kwanaki 12 jirgin ya dauka akan hanya kafin a karshe ya yada zango a cikin Iran. Gabanin tashin jirgin, sai an cimma yarjeniya da kasashen da...
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; Da safiyar yau Asabar ne jiragen yakin HKI su ka kai hari a garin Bint Jubail dake kudancin kasar. Harin na jiragen Sahayoniya dai ya kasance ne a kusa da aibitin Salah-Gandur da hakan ya yi sanadin jikkatar wasu mutane biyu. Wasu yankunan da jiragen sama marasa matuki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai wa hare-hare sun hada Jan’am dake gababsin Shaba’a, da Rashiyal-Wadi. Sai kuma kusa da garin Balida. A jiya Juma’a ma dai ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a kudancin Lebanon da su ka hada da Jabalus-Salihin,da Sahalul-Kiyam, sai Tallatul-Hamamis. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ita ce babbar tushen rashin zaman lafiya a yankin Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi, yayin da yake magana kan kalaman Fira Ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya ce: “Gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya ita ce babbar tushen rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.” A shafinsa na Twitter, Araqchi ya rubuta cewa: Wannan abin da ake kira “tushen tsaro a Gabas ta Tsakiya” ana nemansa ne saboda kisan kare dangi da laifukan yaƙi. Yana sanya tsarin wariyar al’umma ga Falasdinawa miliyan 7.5, ya jefa bama-bamai a ƙasashe bakwai a bara, kuma ya mamaye yankunan Falasdinawa, Lebanon, da Siriya. Ya ƙara da cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya tan zama ita ce babbar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: A bayyane yake cewa Amurka tana da hannu dumu-dumu wajen wuce gona da iri kan kasar Iran Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya mayar da martani ga amincewar da shugaban Amurka ya yi na daukar alhakin harin da sojojin Sahayoniyya suka kai wa Iran, yana mai cewa: “Tun daga farko a bayyane yake cewa Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran.” Baqa’i ya rubuta a shafinsa na X-Platform: “Shin kuna tuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 cewa: Amurka ba ta da hannu a harin da ‘yan Sahayoniyya suka...
Kasashen Mexico da Iran sun yi watsi da zarge-zargen da ake yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ofishin jakadancin Iran da ke Mexico ya yi watsi da “iƙirarin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi game da wargaza wani makircin da Iran ta shirya na kashe jakadan Isra’ila a Mexico.” A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin Iran ya bayyana zarge-zargen a matsayin “ƙirƙirar kafofin watsa labarai da kuma ƙarya bayyananna da nufin lalata dangantakar abokantaka da tarihi tsakanin ƙasashen biyu (Mexico da Iran),” yana mai jaddada kin amincewa da ikirarin tare da bayyana shi a matsayin makircin makiya a fili. A nata ɓangaren, hukumomin Mexico sun fitar da wata sanarwa suna cewa: “Ba su da wani rahoto game da...
A cewar ‘yansanda, “A ranar 10/10/25, an gayyato wani Mista Oke Emmanuel, dan NYSC kuma abokin dakin wanda ya bace, domin yi masa tambayoyi. Ya tabbatar cewa wanda ake nema ya kasance tare da iyalan George har zuwa 06/10/25. “An samu karin bayani daga George cewa dan NYSC din ya koka da rashin lafiya, aka kai su Asibitin Kaiama Referral Hospital a ranar 04/10/25, kuma aka sallame shi ranar 05/10/25. Sai dai a ranar 06/10/25, dan NYSC din ya bace zuwa wani wurin da ba a sani ba.” ‘Yansanda kuma suna binciken zargin karbar kudin rashawa na Naira 100,000 daga iyayen wanda ya bace, da wasu fursunoni biyu da ke gidan gyaran hali na Igbara, Abeokuta, Jihar Ogun, wadanda suka...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi tsokaci kan yadda bangaren shari’a na Turkiyya ya bayar da sammacin kama Netanyahu fira ministan Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yaba da fitar da sammacin neman kama jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila 37, ciki har da shugaban gwamnatin mamayar, Netanyahu mai aikata laifukan yaki, da ministocin tsaro Gallant da Katz. A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Juma’a, kungiyar ta ce wannan matakin “ya tabbatar da matsayin al’ummar Turkiyya da shugabancinsu, wadanda suka jajirce kan kyawawan dabi’un adalci da dan Adam, da kuma ‘yan uwantaka da ke tsakaninsu da al’ummar Falasdinawa da ake zalunta.” Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: “Al’ummar Falasdinawa na ci gaba da fuskantar mummunan yakin kawar da...
Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta
Tarayyar Afirka ta yi kira da a girmama ‘yancin kai na tarayyar Najeriya kuma ta yi watsi da barazanar Trump Kwamitin Tarayyar Afirka ya bayyana damuwarsa game da kalaman da Amurka ta yi kwanan nan game da zargin gwamnatin Najeriya da hannu a kisan Kiristoci da kuma nuna alamun yiwuwar shiga tsakani na soja a karkashin hujjar “kare ‘yancin addini.” A cikin wata sanarwa a hukumance, wacce Al Jazeera ta samu kwafinta, Kwamitin ya jaddada jajircewarsa ga ka’idojin ‘yancin kai, rashin tsoma baki, ‘yancin addini, da kuma bin doka, kamar yadda aka tsara a cikin Dokar Tsarin Mulki ta Tarayyar Afirka da sauran kayan aikin da suka shafi hakan. Sanarwar ta tabbatar da cewa: Tarayyar Najeriya kasa ce mai muhimmanci...
Daga Usman Muhammad Zaria Gidauniyar Tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello (ABMF) ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa sauƙin kai, tawali’u da jajircewarsa wajen ci gaban Jihar Jigawa. Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan yabon yayin da ya jagoranci tawaga zuwa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse. Ya ce salon jagoranci na Gwamna Namadi na ɗauke da ƙima da marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya shahara da su, musamman tsari, girmama jama’a da shugabanci na gaskiya da rikon amana. Dr. Aliyu ya yi kira ga shugabannin Arewa su rungumi jagoranci da ke maida hankali kan al’umma, tare da fifita ilimi a...
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
A nata tsokacin kuwa, kwamishiniya mai lura da ababen more rayuwa da makamashi a hukumar zartarwar kungiyar AU Lerato Dorothy Mataboge, kara tabbatar da alaka ta yi tsakanin hadin gwiwar Sin da Afirka, da burin da ake da shi na bunkasa masana’antu a sassan nahiyar. Mataboge ta kara da cewa, yunkurin bunkasa samar da masana’antu a Afirka na bukatar karfafawa ta hanyar gina kwarewa, da horar da sana’o’i, da samar da cibiyoyi da albarkatun al’umma, don haka ta yi kira da a hada karfi-da-karfe wajen tsara shirye-shiryen bunkasa sanin makamar aiki a cikin gida, da samar da cibiyoyin horo masu nagarta, don horar da jama’a fasahohin amfani da makamashi marar gurbata yanayi. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birni Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassa Abu Turabi Fard, ya bayyana cewa; Tsayin dakar da kungiyar Hizbullah ta Lebabon da Ansurllah na kasar Yemn da kuma al’ummar Iran su ka yi wajen fada da masu girman kai na duniya, sakamako ne na koyarwar alkur’ani maigirma, Ahlul Bayt ( a.s) da kuma Ashura da jagorar matan duniya Fatima az-Zahra ( a.s). Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya ambato limamin na birnin Tehran yana kuma cewa; Makarantar gwgawarmaya tana yi wa zuriya bayan zuriya tarbiyya akan riko da gaskiya da kuma kalubalantar masu danniya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
Jami’i a Asusun yara na MDD y ace; Daga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu Yahudawa ‘yan share wuri zauna da sojojin HKI sun kashe kananan yaran Falasinawa 47,tare da yin gargadi akan hatsari dake tattare da hakan. Manaja mai kula da yanayi na musamman a karkashin Asusun kananan yaran da MDD Recardo Peres ya ce; “Yan share wuri zauna da sojojin HKI sun kashe Kananan yaran Falasdinawa 47 a yammacin kogin Jordan da birnin Kudus tun daga watan Oktoba na 2023. Haka nan kuma ya ce; Bayan abinda ya faru na barnar yakin tsawon shekaru biyu a Gaza, da tsagaita wutar da ake ketawa da kuma kashe yara a cikin sa’o’i kadan da su ka gabata, bai kamata a...
Tarayyar turai ta bayyana cewa ma’aikatan Agaji ba za su iya isha cikin garin Al-fahar ba,kuma birnin ya zama tamkar makabarta. Tarayyar turai din ta bakin mai Magana da yawunta Eva Herneserova ta kuma ce; Sudan ta zama daya daga cikin kasashen da gudanar da ayyukan agaji ya tsananta a duniya,kuma har yanzu da akwai fararen hula da aka killace su adaidai lokacin da ake ci gaba da kai wa asibitoci hare-hare. Eva Herneserova ta kuma ce; Babu sauki ko kadan a kokarin shiga cikin birnin domin isar da kayan agaji. Ma Magana da yawun kungiyar tarayyar turai din ta kuma yi gagradi akan cewa bai kamata a rika amfani da yunwa da kuma kisan kiyashi a matsayin makamin yaki...
Bugu da kari, a gefen taron na COP30, Ding ya gana da sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio Guterres. (Bello Wang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo November 7, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta November 7, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru November 7, 2025
Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale. Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar. “A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar...
Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 a cikin masai. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a. Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai. “Hukumar kashe gobara ta...
“A yayin da ake tarwatsa masu kai harin, DPO na Sassan A da B sun tura ma’aikatansu suka harba hayaki mai sa hawaye, amma wasu motoci cikin motar gwamnan sun lalace,” in ji Abiodun. Ya bayyana cewa mutane uku na farko da ake zargi sune Ali Mohammed da Adamu Hussain, dukkansu daga yankin Nasarafu, Bida, da Isah Umaru na yankin Darachita, Bida. Ya kara da cewa an kama Nagenu, mai shekaru 39, daga yankin Bello Masaba, daga baya dangane da wannan lamari, sannan ya ambaci wasu biyu, Salihu Mohammed da Abdulrahman Baba, yayin tambayoyi. “Dukkan wadanda ake zargi suna karkashin bincike kuma suna taimaka wa ‘yansanda wajen gano wasu. Ana ci gaba da kokarin kama karin mutane da ake zargi,”...
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawat 1 a garin Talasse, karamar hukumar Balanga. Aikin, wanda aka kulla ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), Bankin Duniya, da kamfanin MIDS Dynamics, na da aniyar samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba ga sama da gidaje 8,000 a Talasse da kauyuka makwabta, idan aka kammala shi cikin watanni huɗu. Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 A wajen bikin kaddamar da aikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana shi a matsayin muhimmin ci gaba a...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah wadai da cin zarafin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi wa Lebanon Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da babban harin soji da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon, tana dora alhakin kai harin kan Majalisar Dinkin Duniya, al’ummun duniya, da kuma kasashen yankin kan abin da ta bayyana a matsayin halin gwamnatin mamayar Isra’ila na kokarin tayar da masifar yaƙe-yaƙe. Ma’aikatar ta tabbatar da cikakken hadin kan Iran ga gwamnatin Lebanon da al’ummarta a kan wadannan hare-haren ta’addanci, tana mai jaddada goyon bayanta ga halaltacciyar gwagwarmaya wajen kare ikon mallakar Lebanon. Ta kara da cewa; Hare-haren soji da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya take kai wa kan Lebanon, wadanda suka...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a kafa kwamitin kasa da kasa domin tantance makomar wadanda suka bata a Gaza Shugaban Kwamitin Binciken Mutane da Suka Bace a tawagar Babban Hafsan Rundunar Sojin Iran, Birgediya Janar Seyyed Mohammad Baqirzadeh, ya gabatar da shawarar kafa kwamitin kasa da kasa don neman fiye shahidai 10,000 da suka bace a yankin Gaza. Birgediya Janar Baqirzadeh ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na bangarori uku wanda ya hada da Iran, Iraki, da Kwamitin Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), da nufin tantance makomar shahidai da suka bace da kuma mayar da gawarwakinsu ga iyalansu. Ya jaddada muhimmancin rawar da Kungiyar Red Cross take takawa wajen bin wannan batu na jin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an November 6, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST November 6, 2025 Daga Birnin Sin Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya November 6, 2025
Shugaban ya kuma yaba bisa gudunmawar da kwararrun matasa ke samar wa, musamman masu yiwa kasa hidima da ke yin aikin yiwa kasa hidama, a Hukumar ta NPA. Ya danganta su a matsayin matasan gobe da za su samar da sauyi wajen ci gaba da bunkasa fannin tattalin azrki na Teku da kuma ga daukacin tattalin arzikin kasar nan. An kirkiro da wannan ranar ta NMD ce, a shekarar 2014 wadda kuma aka kaddamar da ita a kasar Ingila a shekarar 2016, wadda kuma ake gudnar da bikin zagoywar ranar, a duk ranar 27 na watan Okutobar kowacce shekara. Kazalika, gudanar da bkin wannan ranar, ta yi daidai da cimma muradun karni, na Majalisar Dinkin Duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Rahotanni su bayyan cewa zanga-zanga ta barke a wajen filin wasan kwallon kafa a Birmingham kafin fara gasar kwallon kafa tsakanin isra’ils maccabe tel aviv da kuma England Ason villa inda suke yi ta rera taken nuna damuwa da halin da yankin Gaza ke ciki da kuma yin kira ga hukumar fifa da ta kori Isra’ila daga cikintta, Wannan yana nuna irin yadda kin jinin Isra’la ya yadu a duniya saboda irin kisan gillan da take yi wa alummar gaza, inda lamarin ya shafi hatta a harkokin wasanni da sauran rayuwar alumma a kasashen turai . Rahotano da jaridar the independent ta nakalto ya nuna cewa magoya bayan falasdinawa sun lika hotuna a fadin birnin dake yin kira ga hukumar...
Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar. Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.” Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League Ajax ta kori kocinta John Heitinga De Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma. Roma...
Ɗan wasan gaba na Nijeriya, Victor Osimhen, ya sha gaban fitattun ‘yan wasa irin su Erling Haaland, Harry Kane, da Kylian Mbappé a yawan zura ƙwallaye a gasar Champions League ta bana. Osimhen ya cimma wannan nasarar ce bayan ya zura ƙwallaye uku rigis a ragar Ajax a wasan zagaye na huɗu na gasar. Ajax ta kori kocinta John Heitinga Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe Wannan ya kai adadin ƙwallayensa zuwa shida, yayin da Haaland, Kane da Mbappé ke da ƙwallaye biyar-biyar kowannensu. A watan da ya gabata, Osimhen ya kuma zura ƙwallaye uku a ragar Jamhuriyyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026, abin da ya ƙara masa farin jini a...