Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP
Published: 12th, November 2025 GMT
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kano da Kewaye, Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi, ya bayyana ficewarsa a hukumance daga jam’iyyar NNPP.
Ƙoƙ8 inda ya danganta hakan da rikicin shugabanci da ke kara tsananta a cikin jam’iyyar.
PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shiA cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2025, wacce aka aika wa Shugaban jam’iyyar a Unguwar Zaitawa a Karamar Hukumar ta Birni, Koki ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa hakkin sa na kundin tsarin mulki na ’yancin shiga ko ficewa daga kowace jam’iyya.
“Bisa ga hakkin da kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara) ya bani a sashe na 40, da kuma sashe na 7.1 na kundin tsarin mulkin NNPP da sauran dokoki, ina sanar da ficewata daga jam’iyyar NNPP daga ranar Talata, 11 ga Nuwamba, 2025,” in ji shi a cikin wasikar.
Ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ya dabaibaye shugabancin jam’iyyar a matakin kasa ya sa shi a tsaka mai wuya, har ma ya zama kusan ba zai iya ci gaba da gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba, da kuma samar da ingantaccen wakilci ga al’ummar mazaɓarsa a majalisar.
“Ficewa daga NNPP ya zama dole saboda rikicin shugabanci a matakin ƙasa ya sanya ba zan iya ci gaba da gudanar da aikina ba tare da kawo wakilci nagari ga mutanen Birnin Kano da Kewaye,” in ji shi.
Koki, wanda aka zabe shi a karkashin jam’iyyar NNPP a zaben 2023, ya nuna godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi ya yi aiki, inda ya ce goyon baya da amincewar da ya samu daga ’ya’yan jam’iyyar sun kasance abin alfahari.
“Ina godiya matuka ga jam’iyyar bisa damar da ta bani na yi aiki a karkashinta. Goyon baya, amincewa da kwarewar da na samu a lokacin zama na dan jam’iyya sun kasance masu matukar muhimmanci, kuma ina godiya ga shugabanni da ’ya’yan jam’iyyar a dukkan matakai,” ya kara da cewa.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ɗan majalisar bai bayyana matakin siyasa na gaba ba ko jam’iyyar da zai shiga ba.
Dama dai tun a watannin baya an sha jin ’yan jam’iyyar ta NNPP na ɗaga masa yatsa saboda yadda suka ce ya cika yin mu’amala da ’yan jam’iyyar APC.
Matakin nasa kuma ma zuwa ne kwana biyu bayan takwaransa naazabar Kiru/Bebeji daga jihar, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sanar da komawa APC watanni biyu bayan an kore daga NNPP.
Kazalika, kafin nan ma, jam’iyyar ta yi asarar Sanata da wasu ’yan majalisar tarayyar guda uku da su ma suka koma APC.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan jam iyyar ga jam iyyar jam iyyar a a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Jarigbe ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Sanata Jarigbe Agom Jarigbe, mai wakiltar Arewacin Jihar Kuros Riba, ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
Sanatan ya bayyana sauyin shekarsa ne a wasiƙar da Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya karanta a zauren Majalisar ranar Talata.
Sauyin shekar ta kara yawan mambobin APC a Majalisar Dattawa zuwa 77