Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe
Published: 13th, November 2025 GMT
A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce hadaddiyar sanarwar da aka fitar a gun taron ministocin harkokin waje na kungiyar G7 ba ta da tushe, inda ta zargi kasar Sin, ta kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar. Don haka Sin ba ta amince da sanarwar ba.
Rahotanni na cewa ministocin harkokin wajen kasashe membobin kungiyar G7, sun tattauna damuwar da ake nunawa game da fadada karfin soja, da makaman nukiliya na kasar Sin, inda suka ce suna bukatar bangaren Sin ya yi alkawarin kiyaye zaman lafiya.
Game da hakan, Lin Jian ya ce Sin kasa ce da ta fi mayar da hankali ga batun kiyaye zaman lafiya da tsaro, tana kuma tsayawa tsayin daka kan turbar samun ci gaba cikin lumana, da manufofin kiyaye tsaron kasa, da na kiyaye takaita yawan makaman nukiliya bisa bukatun tsaron kasar.
ADVERTISEMENTJami’in ya ce kungiyar G7 ba ta ambato alhakin dake wuyan kasar Amurka, na rage makaman nukiliya, da hadarin yaduwar makaman nukiliyar a sakamakon raya dangantakar abota, ta kiyaye tsaro a tsakanin Amurka da Birtaniya da Australia ba, amma ta zargi kasar Sin ba tare da wani tushe ba. (Zainab Zhang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Jakadun Kasashen Waje: Shirin Raya Kasa Na 15 Na Sin Na Dauke Da Kyakkyawan Sako
Manyan jami’an diplomasiyya daga kasashe sama da 160, ciki har da jakadu 90 dake kasar Sin da manyan jami’an ofisoshin jakadancin kasashen ne suka halarci taron, wanda sashen kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS ya shirya. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA