Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026
Published: 15th, November 2025 GMT
Da yake ƙarin haske kan muhimman sassan da aka fi bai wa fifiko, Gwamnan ya bayyana cewa, ɓangaren tattalin arziƙi da ci gaban al’umma ne suka samu kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin, inda aka ware sama da Naira biliyan 269 don sanya hannun jari a muhimman fannoni.
Fannin ayyuka, gidaje da sufuri ne ke kan gaba da Naira Biliyan 135.
A fannin harkokin zamantakewa, an ware Naira biliyan 80 don samar da ayyukan ci gaba da gina jama’a, inda ilimi ya samu Naira biliyan 31.9, yayinda ilimi mai zurfi ya samu Naira biliyan 17.5.
Ɓangaren kiwon lafiya ya samu Naira biliyan 25.9, wanda hakan ke nuna yadda gwamnati ke ci gaba da zuba jari wajen samar da lafiya mai inganci.
Fannin gudanarwa ya samu Naira biliyan 19.63, sannan ɓangaren doka da shari’a aka ware masa Naira biliyan 2.17, fannin filaye ya samu Naira biliyan 6.46; shi kuwa fannin Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido ya samu Naira biliyan 4.02.
Yayin da sashen matasa da ci gaban wasanni ya samu Naira biliyan 3.33; harkokin mata da ci gaban a’umma Naira biliyan 1.28; fannin yaɗa Labarai da raya al’adu kuwa Naira biliyan 10.38.
Gwamna Yahaya ya bayyana ƙididdigar kasafin kuɗin na 2026 a matsayin na ɗorawa kan ci gaban da gwamnatinsa ta faro na gudanar da shugabanci nagari, Gwamna Inuwa Yahaya ya yi ƙira ga majalisar akan ta yi nazari tare da ƙalailaice ƙudurin tare da sanya gudunmawa da tabarrukinta.
“Aikin dake gabanmu shi ne mu samarwa al’ummarmu kasafin kuɗin da zai wanzar da fatansu ya zuwa zahiri da kuma kyautata makomarsu,” in ji shi.
Kasafin kuɗin na 2026 ya dace da tsarin ci gaban Jihar Gombe (DEVAGOM) da kuma tsarin tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya. Da yake tsokaci kan harkokin tattalin arziƙi a dunƙule, Gwamnan ya ce sauye-sauyen da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɓullo da su, da suka haɗa da cire tallafin man fetur da sakin mara ga canjin kuɗaɗen waje, sun fara haifar da sakamako na ƙwarai.
A nasa jawabin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe Rt. Hon. Muhammad Abubakar Luggerewo, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da bin doka da oda, da gaskiya da kuma tsantseni wajen tafiyar da harkokin kuɗaɗen gwamnati.
Ya bada tabbacin duba kasafin akan lokaci da kuma gaggauta amincewa da ƙudurin kasafin na 2026.
Rt. Hon. Luggerewo ya kuma nuna jin daɗinsa da yadda jihar ke tafiyar da harkokin kasafin kuɗi, inda ya ce aiwatar da kasafin kuɗin 2025 ya samu nasarar fiye da kaso 60 cikin 100 ya zuwa ƙarshen watan Satumba, sannan ya yaba da yadda gwamnati ta samu ci gaba a fannin samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, masana’antu, da sabunta birane.
“Za mu ci gaba da tallafawa manufofi da tsare-tsaren dake tabbatar da zaman lafiya, inganta ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar jama’armu,” in ji kakakin.
A shekarar da ake ciki ta 2025, Gwamnatin Inuwa ta yi kasafi ne na fiye da Naira biliyan 369.9, inda daga baya aka yi bitarsa ya koma na fiye da Naira biliyan 451.6 biyo bayan samun ƙarin kuɗaɗen shiga fiye da yadda aka yi tsammani.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: ya samu Naira biliyan da Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu
Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya.
Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotuAn shigar da ƙarar ne mai lamba FHC/ABJ/CR/610/2025, dangane da wasu rubuce-rubuce da matashin ya wallafa a shafinsa na X a watan Oktoban 2025.
A cewar DSS, waɗannan rubuce-rubuce sun nemi a kifar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki tare da nuna goyon baya ga sojoji su karɓi mulki a ƙasar.
Lauyan DSS, A.M. Danalami, ya shigar da ƙarar a ranar Talata, inda aka bayyana cewa ayyukan wanda ake zargin sun saɓa da sashe na 46A(1) da 59(1) na Dokar Manyan Laifuka ta Ƙasa, da kuma Sashe na 24(1)(b) na Dokar Laifukan Intanet ta 2024 (wacce aka yi wa gyara).
Daga cikin kalaman da ake zargin ya wallafa akwai: “Ana buƙatar juyin mulki a Najeriya. A kawar da APC, a dakatar da gwamnatin Najeriya, a shiga kungiyar AES. Wannan ne kawai muke buƙata yanzu.”
Haka kuma, ana zargin ya rubuta cewa: “A karshe zai faru, yak u ’yan Najeriya. Sojoji na buƙatar goyon bayanku yanzu! Su kaɗai ne za su iya ceton ƙasar nan. Wanda ke Aso Rock ya sayar da ƙasar nan ga Turawa, su ke sarrafa sirrikanmu. Sojoji kaɗai za su iya sake daidaita ƙasar nan.”
A wani rubutu daban kuma ya ce: “Dole ne Tinubu ya tafi, kuma dole APC ta mutu kafin Najeriya ta samu daidaito.”
Ana sa ran za a gurfanar da Onukwume, wanda mazaunin Umusayo Layout ne a Karamar Hukumar Oyigbo ta Jihar Ribas a kotu cikin makon nan.
A watan Oktoba, an samu rahotanni da ke nuna cewa wasu jami’an sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.