Aminiya:
2025-11-13@09:03:43 GMT

Yadda na yi asarar N120m a gobarar Singa — Ɗan Kasuwar Kano

Published: 13th, November 2025 GMT

Wani babban ɗan Kasuwar Singa da ke Jihar Kano, Alhaji Salisu Abdullahi, ya ce ya yi asarar kaya da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 120 a gobarar da ta auku da safiyar ranar Alhamis, wadda ƙone shaguna da yawa.

“An kira ni da misalin ƙarfe 6 na safe, na garzaya zuwa kasuwa, sai kawai na tarar komai ya ƙone.

“Na karɓi kaya bashi a makon da ya gabata domin ci gaba da sayarwa. Yanzu ban san ta yadda zan tunkari masu kayan ba,” in ji shi.

Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 5 na Asuba, ta ƙone shaguna 44 da dukiya mai tarin yawa.

Hukumar Kashe Gobara Jihar Kano, ta ce gobarar ta samo asali ne daga matsalar wutar lantarki a wani gini, wadda daga bisani ta yaɗu zuwa sauran shaguna.

Wani ɗan kasuwa, Musa Abdulhadi, ya ce gobarar ta yaɗu cikin ƙanƙanin lokaci ta yadda ba a samu damar ceto komai ba.

“Gobarar ta yaɗu cikin sauri ƙwarai; ba mu iya fitar da kaya ko ɗaya ba. Na yi asarar kaya na kimanin Naira miliyan takwas.

“Wannan abu ne mai raɗaɗi musamman a wannan mawuyacin hali na tattalin arziƙi da ake ciki,” in ji shi.

Hukumar kashe Gobara ta jihar ta bayyana cewa jinkirin da aka samu wajen kai agaji ya samo asali ne daga manyan motoci da suka toshe hanyoyin shiga kasuwar.

Duk da haka, jami’an hukumar sun samu damar dakatar da gobarar kafin ta bazu zuwa wasu gine-gine.

Wasu ’yan kasuwa sun ɗora laifin tashin gobarar kan amfani da tsohuwar wayar wutar lantarki da rashin kulawa.

Sun ce sun ta yi ƙorafi a baya amma ba a ɗauki mataki ba.

Sun roƙi gwamnati ta tabbatar da ana yin bincike akai-akai a kasuwanni domin kare rayuka da duniyoyin al’umma.

’Yan kasuwar da abin ya shafa sun roƙi Gwamnatin Jihar Kano da masu hannu da shuni da su taimaka musu.

Abdullahi, ya ce: “Muna kira ga gwamnati ta taimaka mana mu sake gina shagunanmu. Da

“Da dama daga cikinmu bashi muka ɗauki kaya domin mu sayar. Idan ba a taimaka mana ba, ba mu san yadda za mu yi ba.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: dukiya Ɗan Kasuwa Gobara Kasuwar Singa Kayayyaki

এছাড়াও পড়ুন:

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

 

Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kyautata harkokin masana’antu. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta ba da taimako wajen shigar da mambobin WTO su 130 cikin yarjejeniyar samar da sauki a ayyukan zuba jari domin neman ci gaba, ta yadda kowa zai cimma moriyar sakamakon dunkulewar duniya cikin adalci. (Mai Fassara: Maryam Yang)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya November 11, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15 November 11, 2025 Daga Birnin Sin Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa? November 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
  • Kano Ta Kaddamar da Kwamitin Jagoranci Don Shirin Tarayyar Turai na Ilimi da Ƙarfafa Matasa
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Filin Jirgin Sama Na Kano
  • Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna
  • Yadda muka daƙile yunƙurin tsige Akpabio daga shugabancin Majalisa – Orji Kalu
  • Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
  • Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal
  • CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 
  • HOTUNA: Yadda Gobara Ta Ƙone Shaguna 25 A Kasuwar Singa A Kano