Aminiya:
2025-08-02@20:58:03 GMT

Mutum ɗaya ya rasu, an jikkata wasu yayin arangama da ’yan sanda a Abuja

Published: 2nd, August 2025 GMT

Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake zargin masu ƙwacen fili ne suka zo ƙauyen tare da ‘yan sanda daga ofishin Byazhin, suna ƙoƙarin ƙwace wani fili a ƙauyen.

Zulum zai mayar da ’yan gudun hijira 5,000 Bama Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa

Dangana, ya ce lokacin da mazauna ƙauyen suka gan su, sai suka taru suka toshe hanya don hana su zuwa wajen filin.

Ya ce mutanen ƙauyen suna riƙe sanduna da duwatsu, inda suka fuskanci jami’an tsaro.

Daga nan ’yan sandan suka fara harba barkonon tsohuwa da harsasai.

“Ɗaya daga cikinmu an harbe shi ya mutu, biyu kuma sun jikkata,” in ji Dangana.

Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke garin Bwari domin kula da su.

Ƙwamishinan da ke wakiltar mazaɓar Byazhin/Kuchibiyi, Hon. Dogara J. Ahmed, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an shaida masa cewa mutum ɗaya ya rasu, yayin da wasu biyu kuma sun samu rauni.

“Yanzu haka na iso ƙauyen domin samun cikakken bayani,” in ji shi.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce an kama wasu mutane kan rikicin fili a ƙauyen Kuchibiyi.

Ta ce DPO na Byazhin da na Kubwa sun garzaya wajen domin kwantar da tarzoma, kuma lamarin ya lafa.

Ta tabbatar da cewa an kama mutane kuma suna ci gaba da bincike, amma ba ta ce komai ba kan wanda aka ce ya rasu ko waɗanda suka jikkata ba.

Sai dai ta bayyana cewa Kwamishinan ’yan sandan Abuja, CP Ajao Saka Adewale, ya soki yadda matasan ƙauyen suka kai wa jami’an tsaro hari.

Ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci hakan ba, kuma za ta ɗauki matakin doka kan duk wanda ya aikata hakan.

’Yan sanda sun ce za su yi ƙarin bayani a nan gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Arangama Ƙauye

এছাড়াও পড়ুন:

Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu

Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis.

Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya.

Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana

Sakataren masarautar Gudi da ke Gadaka ne ya tabbatar da rasuwar Sarkin, ya kuma ce an shirya gudanar da Sallar Jana’izar marigayi Sarkin a ranar Juma’a da ƙarfe 2:00 na rana a fadar Sarkin da ke Gadaka.

Labarin rasuwar Sarkin dai ya tayar da hankalin a ɗaukacin al’ummar masarautar da ma Jihar Yobe baki ɗaya, inda da yawa ke jinjinawa jagorancinsa da kuma abin da ya bari.

Ana ci gaba da miƙa saƙon ta’aziyyarsu daga ko’ina, a dai-dai lokacin da jama’a ke juyayin rashin Sarkin.

Marigayi Sarkin Gudi ya shahara wajen hikima da jagoranci da jajircewa wajen ci gaban al’ummarsa tare da  taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da haɗin kai a tsakanin al’umma, kuma za a riƙa tunawa da abin da ya bari har zuwa tsawan lokaci.

Sallar jana’izar wadda manyan malamai za su jagoranta, za ta samu halartar manyan baƙi, shugabannin gargajiya da sauran al’umma.

Za a binne gawar Sarkin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin na Gadaka.

Al’ummar masarautar dai na cikin alhini, inda da dama ke nuna alhininsu dangane da rashin jagoransu.

Ana sa ran gwamnati da al’ummar Jihar Yobe za su yi wa marigayi Sarkin gaisuwar ban girma, ganin irin rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dadiyata: Buhari ya gaza nemo shi, Tinubu yana da lokaci — Amnesty
  • Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa
  • HOTUNA: Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gudi na Yobe bayan rasuwarsa a Abuja
  • An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi
  • Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata
  • Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu
  • Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
  • ‘Yan Sandan Niger Sun Hada ‘Yan’uwa Mutanen 35 Da Aka Ceto Da Iyalansu 
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina