AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya
Published: 16th, November 2025 GMT
Shugaban Kwamitin Tarayyar Afirka ya yi watsi da zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ana wa Kiristoci kisan kare dangi a arewacin Najeriya.
Da yake jawabi a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, ya ce irin wadannan kalamai kan iya gurbata matsalolin tsaro mai sarkakiya.
Da yake magana tare da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a ranar Alhamis, Mahmoud Ali Youssouf ya jaddada cewa Tarayyar Afirka ta riga ta fayyace matsayinta kuma ta yi kira da a yi taka tsantsan a cikin harshen da ake amfani da shi wajen bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a nahiyar.
“Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya,” in ji Youssouf. “Mun fitar da wata sanarwa a fili da ke nuna cewa abin da ke faruwa a arewacin Najeriya ba shi da alaka da ta’addancin da muke gani a Sudan ko a wasu sassan gabashin DRC.”
Musulmai da Kiristoci, dukkansu abin ya shafa inji shi…
Ya kara da cewa tashin hankalin da ake yi a arewacin Najeriya, wanda galibi kungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISIS a Yammacin Afirka ke haifarwa, ya shafi Musulmai da Kiristoci.
“Ina ganin lamarin arewacin Najeriya ya kamata mu yi taka tsantsan kafin mu yi irin wadannan kalamai,” in ji Youssouf.
“Musulmai ne suka fara shan wahala a hannun Boko Haram, ba Kiristoci ba, kuma ina faɗin haka ne bisa bayanai da muke dasu.”
A kwanan baya ne shugaba Trump na Amurka ya bayyana cewa zai doki matakin soji a Najeriya bisa zargin cewa gwamnatin kasar na kauda kai a game da kisan da y ace ana wa Kiristoci a kasar batun da Najeriya ta musanta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana November 15, 2025 Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu. November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a arewacin Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Mali ta Dakatar da Tashoshin Talabijin na Faransa TF1 da LCI
Hukumomin Mali sun dakatar da watsa shirye-shiryen tashoshin gidajen talabijin na kasar Faransa TF1 da LCI a fadin kasar.
Hukumar Sadarwa ta Mali ta bayar da dalilan dakatar da wadanan tashohin bisa wani shiri da tashar LCI ta yi kan halin da ake ciki sakamakon matsalolin tsaro masu nasaba da kungiyoyin dake ikirari da sunan jihadi.
Shirin mai suna “Grands Dossiers” da aka watsa a LCI a ranar Lahadi, 9 ga Nuwamba, wanda aka raba zuwa sassa biyu ya kunshi kanun labarai kamar haka ” Masu ikirarin Jihadi a Kofofin Bamako” da kuma “Mali, Karkashin kungiyar Al-Qaeda.”
A sashen guda, wanda aka dora a shafin yanar gizon tashar TF1+, rahoton yi ikirarin cewa gwamnatin mulkin soja ta haramta sayar da mai, kuma yankunan Kayes da Nioro suna killace, kuma ‘yan ta’adda suna kusa da kwace babban birnin.
A cewar hukumomin Mali, hakan ya karya ka’idar da’a ga ‘yan jarida a Mali, wanda ke bukatar su yi gaskiya da kuma buga bayanai da aka tabbatar.
Takun tsaka tsakanin Mali da Faransa ya yi kamari tun bayan da sojoji suka kwace mulki a kasar.
Kuma wannan ba shi ne karon farko da Mali ke dakatar da watsa shirye shiryen gidajen talabajin da radiyo na faransa a kasar ba.
A cen baya Mali ta dakatar da watsa shirye shiryen gidan radiyo RFI da kuma tashar talabijin ta France24 a kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro don amincewa da shirin zaman lafiya na Trump November 15, 2025 AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro November 15, 2025 Iran ta bukaci duniya ta gaggauta daukar mataki a Sudan November 15, 2025 EU ta nemi Isra’ila ta dauki mataki kan tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan November 15, 2025 Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin November 14, 2025 Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire November 14, 2025 Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza November 14, 2025 Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya November 14, 2025 Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya November 14, 2025 Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci