Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana
Published: 13th, November 2025 GMT
Aƙalla mutum 12 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani turmutsutsu da ya faru yayin jarabawar ɗaukar aikin soja a Filin Wasa na El-Wak da ke Accra, babban birnin ƙasar Ghana.
Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da ɗaruruwan matasa masu neman aikin suka kutsa cikin filin wasan ba tare da bin tsarin shiga da aka tanada ba.
Rundunar Tsaron Ghana (GAF) ta ce mutum shida ne suka mutu a farko, amma rahotanni daga asibitin sojoji sun tabbatar da cewar adadin mamatan ya ƙaru zuwa mutum 12.
Wasu mutum 22 sun jikkata, ciki har da biyar da ke cikin mawuyacin hali, kamar yadda jami’ar asibitin sojojin ƙasar ta tabbatar.
Ministan Tsaro, Dokta Cassiel Ato Forson, ya ce an dakatar da ɗaukar na wani ɗan lokaci tare da kafa kwamiti domin binciken musabbabin lamarin, wanda ta bayyana a matsayin abin takaici.
Shugaban ƙasar, John Mahama, ya kai ziyarar jaje ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma marasa lafiya, inda ya bayyana cewa gwamnati za ta ɗauki matakan tabbatar da cewa irin wannan lamari ba zai sake faruwa ba.
Rundunar Tsaron Ghana ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da kula da waɗanda suka jikkata a asibitin sojoji.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum 14 da ake zargi da ta’amali da miyagun ƙwayoyi da kuma aikata wasu laifuka daban.
Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar.
MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotuA cewar SP Shiisu, jami’an rundunar sun kama mutanen ne a wurare daban-daban da suka haɗa da Dutse, Guri, Babura, Kanya Babba, Bulangu da kuma ‘Yankwashe.
Ya ce rundunar ta ƙwato miyagun ƙwayoyi iri-iri da suka haɗa da Exol guda 8,271, D5, Tramadol, Diazepam, Sholisho, Sukudayin, tabar wiwi, da kuma kuɗi Naira 235,225.
SP Shiisu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da farautar duk wanda yake da hannu a harkar.
Ya ƙara da cewa za su gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu da zarar sun kammala bincike, domin su fuskanci hukuncin da ya dace da laifukansu.