Aminiya:
2025-11-14@10:22:17 GMT

An kama ’yan Najeriya 3 a Kenya kan zargin aikata damfara

Published: 14th, November 2025 GMT

An kama ’yan Najeriya uku a rukunin gidaje na Mwaliko da ke garin Mwea a ƙasar Kenya, bisa zargin su da damfara ta intanet.

Rahoton da wata kafar labarai a Kenya mai suna Tuko News ta fitar ya ce Hukumar Binciken Laifuka ta ƙasar (DCI) ce ta kama waɗanda ake zargin a ranar Laraba.

Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan

Waɗanda aka kama sun haɗa da Peter Chukwujekwu, Alazor Chukulute Sunday, da Nnalue Chiagozie Samwe.

A cewar rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, an kama su a gidansu bayan jama’a sun kai ƙorafi kan take-takensu musamman da daddare a cikin ginin.

DCI ta tabbatar da kama su, tana mai cewa an gudanar da “farmakin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da dama domin kama wata ƙungiyar masu damfara ta intanet” a yankin.

Rahoton ya ambato DCI tana cewa: “An kama ’yan Najeriya uku a wani farmakin haɗin gwiwa a Kirinyaga. Wannan farmaki da aka tsara sosai a rukunin gidaje na Mwaliko cikin garin Mwea ya tona asirin wata ƙungiyar masu damfara ta intanet da ’yan Najeriya uku ke gudanarwa.”

Waɗanda ake zargin sun ce suna gudanar da kasuwanci ta yanar gizo, amma rahoton ya nuna cewa suna zaune a Kenya ba tare da izini ba, kuma ba su da takardun aiki na doka.

Kamun nasu dai na cikin jerin kame-kamen da ake yi wa ’yan Najeriya a ƙasashen waje kan laifuka daban-daban, ciki har da damfara ta intanet, safarar miyagun ƙwayoyi, da safarar mutane.

Ko a watan Yunin 2023, sai da ’yan sandan a kasar ta Kenya suka kama ’yan Najeriya 19 a Nairobi, babban birnin kasar, bisa zargin damfara ta intanet da ke kai hari ga ’yan ƙasar.

A cewar DCI, mutanen da shekarunsu ke tsakanin 19 da 33, sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen fara damfarar, suna yaudarar ’yan Kenya da sunan za su tura musu kaya daga ƙasashen waje.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Damfara Kenya damfara ta intanet yan Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya

A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su.

A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar.

 

Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba, to akwai alamun sake rage yawan kujerun zuwa dubu hamsin.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma

Ko yaya kara raguwar kujerun maniyyatan Najeriya ke kara tasiri ga Najeriya?

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya
  • Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Dillalin Makamai A Taraba
  • Kenya: An gano tarin zinari da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 a yammacin kasar
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi
  • ’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa
  • DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu
  • Hukumar Tsara Birane ta Kano Ta Fara Horar da Ma’aikata Kan Dokokin Aiki
  • DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma