Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa
Published: 14th, November 2025 GMT
An yi hadaka tsakanin asusun da ke tallafa wa bunkasa aikin noma na kasa (NADF) da kuma Gwamnatin Jihar Jigawa, inda suka kaddamar da shiri na farko na bai wa manoma bashin noma.
A cikin sanawar da asusun ya fitar, shirin zai bayar da dama ga masu zaman kansu, musamman kananan manoma wajen ba su bashin kudin noma tare kuma da kara samar musu da wadataccen abinci.
Babban Sakataren Asusun, Mohammed Ibrahim ya bayyana cewa; shirin zai magance gibin da kananan manoma ke fuskanta wajen samun rance kudaden noma.
ADVERTISEMENTShi kuwa, Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Aikin Noma na Jihar Jigawa, wato JATA Dakta Saifullahi Umar, ya bayar da tabbacin cewa; jihar ta mayar da hankali wajen bunkasa fannin aikin noma ta hanyar yin amfani da fasahar zamani tare da jawo kamfanoni masu zman kansu, ta hanyar yin hadaka.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da ya kamata PDP ta jingine taron da za ta gudanar— Saraki
Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya buƙaci jam’iyyar PDP da ta ɗage babban taronta da ta shirya gudanarwa tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
Saraki ya ce ci gaba da shirin gudanar da taron duk da irin umarnin dakatarwa da kotuna suka bayar zai ƙara ta’azzara rikicin jam’iyyar sannan ya jefa ta cikin matsaloli a nan gaba.
An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin DuniyaYa bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan karɓar baƙuncin ’yan kwamitin amintattun jam’iyyar ƙarƙashin shugabancin Ambasada Hassan Adamu, a gidansa.
Tawagar ta ziyarci Saraki ne domin neman tabarrakinsa da shawarwari kan yadda za a cimma haɗin kai a jam’iyyar da ta samu rarrabuwar kai.
Tsohon shugaban da ya jagoranci Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019, ya ce umarnin kotuna kusan huɗu masu karo da juna game da babban taron zai iya jawo matsala kan halascin duk wani mataki da ya biyo bayan taron.
Zuwa yanzu, akwai ƙararraki uku a gaban kotuna daban-daban waɗanda suka bayar da umarnin dakatar da shirin taron, yayin da PDP ta ce tana ci gaba da shirin gudanar da shi a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba.
Daga cikin waɗanda suka kai jam’iyyar kotu kan taron akwai Ministan Abuja, Nyesom Wike, da tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido.