Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin
Published: 14th, November 2025 GMT
Ministan yakin Amurka Pete Hegseth ya bayyana cewa kasar tasa ta fara kai farmakin da ta kira ” Mashin Kudu” akan dillalan muggan kwayoyi.
Ministan yakin na Amurka ya rubuta a Shafin X cewa; manufar wannan farmakin shi ne kare kasarmu, da kawo karshen masu dillancin muggan makamai ‘yan ta’adda, da kare kasarmu daga muggan kwayoyin da suke kashe mana ‘yan kasa.
Gwamnatin Donald Trump dai ta bude kai hare-hare akan jiragen ruwan a doron ruwan Carrebia da tekun Pacific bisa abinda take riya cewa masu fataucin muggan kwayoyi ne.
Sai dai har yanzu babu wani dalili guda daya da Amurkan ta gabatar da shi wanda yake nuni da cewa wadannan jiraegen ruwa da take kai wa harin suna dauke da muggan kwayoyi.
Amurka din ta girke jiragen ruwa na yaki da su ka hada da “Gerald Ford”.
Kafafen watsa labarun Amurka da su ka hada da ” CBS” sun ambaci cewa, makusantan Donald Trump sun ba shi shawarar kai hare-hare a cikin kasar Venezuela.
A nata gefen, gwamantin kasar ta Venezuela ta sanar da girke sojoji a fadin kasar domin fuskantar duk wani hari daga kasar Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire November 14, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 14, 2025 Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza November 14, 2025 Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya November 14, 2025 Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya November 14, 2025 Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya November 14, 2025 Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka November 14, 2025 Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu November 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka
Tehran ta yi Allah wadai da sanarwar da kasashen gungun G7 suka fitar kwanan nan, wadda ta amince da matakan da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana zarge-zargen kin jinin Iran dake kunshe a cikin sanarwar karshe ta gungun kasashen da suka hada da (Faransa, Amurka, Kanada, Japan, Burtaniya, Italiya, da Jamus), a matsayin “marar tushe, kana mai cike da karairayi.”
Baghhai ya yi ikirarin cewa yunkurin Amurka da Tarayyar Turai na mayar da takunkumin kai tsaye daidai yake da amincewa da wani laifi na kasa da kasa.
Da yake sukar kasashen kungiyar G7 kan yin kira ga Iran da ta ci gaba da hadin gwiwa da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Mr. Baghai ya jaddada gazawarsu wajen hana hare-haren Isra’ila da Amurka kan cibiyoyin nukiliya na zaman lafiya a Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu November 14, 2025 Abdoulaye Diop: ‘Yan Tawaye Ba Za Su Iya Mamaye Dukkan Kasar Mali Ba November 14, 2025 Ramaphosa Ya Caccaki Trump Kan Kauracewa Taron G20 A Johannesburg November 14, 2025 MDD ta nuna damuwa game da rahotannin kisan gilla a El Fasher November 14, 2025 Rasha Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Amurka November 13, 2025 Iran Da Qatar Sun Tattauna Kan Dangantakar Dake Tsakaninsu November 13, 2025 Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Sun Kona Masallaci A Yammacin Kogin Jodan November 13, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Fara Karbar Harajin Man Fetur November 13, 2025 Iran da china Za su Yi Bikin Cika Shekaru 55 Da Huldar Diplomasiya Tsakaninsu November 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci