Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA
Published: 15th, November 2025 GMT
An haife ni a garin Kano, karamar hukumar Nasarawa, Giginyu, Mahaifana ‘yan Sakkwato ne. Na yi aure a Kano ina da yara na guda uku, namiji daya mata guda biyu. Na yi firamare da Sakandare, a garin Kano.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim?
A baya ban taba jin zan yi fim ba dan bana ra’ayi, ban taba jin abun yana burgeni ba, ban kuma taba sa shi a raina ba har in ce zan yi ba.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
‘Yan’uwana da ‘yan’uwan babanmu da suka fara gani yadda ki ka san na cike fom na ‘yan ‘kidnapping’ abun haka ya kasance min, aka rika kira na ba su yarda da hakan ba, to ni kuma na riga na san yayata uwa daya uba daya ita ce babbar yayarmu ita ce komai nawa jigona, duk duniya na riga na san ta amince min. Ita ce wacce ta san ci na, sha na, sutura ta, har ma ta kula da ‘ya’yana tunda ta amince min, kuma ita ce ta san damuwata sai na ga babu wanda ya isa ya ce zai hana ni. Da dai suka gama abinsu kuma har suka zo na fahimtar da su na ce ni fa wannan abun sana’a na dauke shi, sai kuma suka fahimta su da kansu ma suna yi min addu’a. Dan har so suke ma su gafim din da nake ciki ma su yi farinciki su yi murna.
Ya farkon fara fim dinki ya kasance?
Farkon farawar da ya kasance, yadda ki ka san tsowurar jaruma zan ce miki, farko dai abun gabana yana faduwa ko da aka saka min kyamara jikina yana rawa dai sai na daure, sai na yi musu abin da suke so ba a samu matsala ba. Dan su ma suka rika mamaki suka ce min na taba yi ne? na ce masu a’a.
Da su wa ki ka fara haduwa farkon shigarki masana’antar kannywood?
Bayan na yi aikin kwana casa’in, sai aka kira ni aikin Izzar So, na fara haduwa da su Lawan Ahmad da sauran jarumai da suke cikin Izzar So.
Daga lokacin da ki ka fara fim zuwa yanzu, kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
Gaskiya na yi su da dama ba zan iya fado adadinsu ba, amma kadan daga cikinsu akwai; Izzar So, Sirrin Boye, Dadin Kowa, Manyan Mata, da dai sauransu.
Wane fim ne ya zamo bakandamiyarki cikin finafinan da ki ka fito ciki?
Akwai Izzar So, akwai Laure. Shi Laure ba wani yi nayi da yawa ba, amma yadda ki ka san da shi na fara, saboda duk inda na shiga ma ce min ake yi Lauren.
Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?
Nasara a harkar fim sai dai na yi wa Allah godiya, na ci arzikin fim, dan wataran ina tafiya a hanya sabida darajar fim da daukakarsa abubuwa da yawa an yi min saboda Allah, saboda fim. Saboda idan wasu sun gane ni a wani abun sai su yi min alkhairi. Na sha shiga Adaidaita Sahu mutane su kaunacen su biya min kudin.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta cikin masana’antar?
Ba wani walubale dana taba fuskanta a ciki, shi fim idan ka ce za ka yi shi akwai wani abu wanda dole za ka yi hakuri, wanda yanayin fim din ne dole sai ka yi hakuri.
*Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwa?
Faranciki da bakin ciki yana nan a ranka, ba abun da ya kai rabuwa da iyaye, Astagafrillah Allah ne dai ya baka su ya karbi abinsa. Wannan abun shi ya fi taba ni, dan idan na tuna ba ni da uwa ba ni da uba duk abin da nake yi komai yana canjawa. Ko cikin farinciki nake, idan na tuna wannan ina jin komai yana canjawa. Sai na ji kamar na fi kowa maraici. Sai abun farinciki idan nayi tunanin Allah ya azurta ni da ‘ya’ya ina jin dadi ina jin sanyi a cikin zuciyata, ina kara godewa Allah.
Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?
Duk Kannywood ban da ubangidan da ya wuce Lawan Ahmad.
Kafin shigarki masana’antar Kannywood wadanne jarumai ne suke burge ki, kuma me ya sa?
Sani Danja, Lawan Ahmad, Uncle Sade S. Fulani kenan. A lokacin duna burge ni sosai har yanzu kuma. A mata kuma ina son Adaman Kamaye ina kaunarta, ina son Nafisa Abdullahi, ina son Rahama Sadau. Har yanzu ina kaunarsu, amma yanzu kowa ma yana burge ni.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Babban burina ina son Allah ya daukaka ni, na ga ni ma ina da abin da zan taimaki na kasa da ni.
Bayan fim kina wata sana’ar ne?
Ina siyar da shinkafa, ina yin ‘business’ wanda ya samu.
Misali wani daga cikin abokan aikinki ya ce yana sonki zai aure ki, shin za ki amince ki aure shi ko ba ki da ra’ayin auren d’an fim?
Tunda na yarda da aikin nawa babu batanci, kuma sana’ar mu daya da gudu zan yarda na aure shi, indai yana sona ina son shi.
Wasu na kokawa game da masana’antar kannywood, a takaice ya za ki yi wa masu karatu bayani game da masana’antar, shin wace ce Kannywood ya cikinta yake?
Kannywood masana’anta ce kamar yadda na yi miki bayani, duk yadda ka dauke ta haka za ta tafi da kai. Idan niyyarka daya sana’a ka dauke ta, Allah zai dafa maka. Idan kuma da wani manufa ka zo duk za ta tafi da kai. Ni dai gaskiya a sana’a na dauke ta, kuma Allah yana ba ni, ina samu daidai yadda sana’ar tawa ta ba ni.
Wane kira za ki yi ga masu kokarin shiga kannywood?
Kira na, dole ne su bi iyayensu in sun so su shiga, in kuma suna so su rarrashi iyayen nasu har su bar su tom, su shigo da kyakkyawan yakini sun fito sana’a.
Ko akwai wata shawara ko wani sako da ki ke da shi ga sauran abokan aikinki?
Shawara daya ce da Allah ubangiji ya hada kahunanmu, in an zo fadace-fadace in an zo a rika hakuri da juna, duk sana’ar da Allah ya hada ka da mutane sai ka yi hakuri da juna. Wataran za a yi maka ba dadi ka yi hakuri, wataran za a yi maka dadi dole ka karba ka yi farinciki. Kawai babban burina Allah ya hada kahunanmu, mu zama tsintsiya daya madaurinki daya. Gashi muna sana’a daya harkokinmu daya amman wani ya zagi wani ko wani abu bana fatan hakan, Allah ya kara hada kanmu. Allah kuma ya ba mu zaman lafiya, da daukaka mai amfani.
Me za ki ce da masoyanki masu kallon finafinanki?
Ba abin da zan ce da masoyana sai dai fatan alkhairi , ina gdoiya sosai Allah ya bar mu da masoyanmu da masu waunarmu. Ina yi wa kowa da kowa fatan alkhairi da masoyan da wanda ba masoyanma ina yi mana fatan alkhairi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: aikin kwana casa in masana antar
এছাড়াও পড়ুন:
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano
Ya kara da cewa yayin gudanar da aikin, jami’an hukumar sun gano babura hudu daga hannun wanda ake zargi babura uku na Jincheng da daya na Lifan Kumata, inda ya ce ana ci gaba da neman sauran abokan aikinsa biyu da suka tsere.
Haka kuma, ya bayyana cewa an kama mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Salisu Abdullahi, dan shekara 28, mazaunin Semegu a Karamar Hukumar Kumbotso, a yankin Sabon Titin Dorayi, tare da tarin miyagun kwayoyi da ake zargin yana sayarwa don amfani na haram.
Kwayoyin da aka samo daga hannunsa sun hada da kwayoyi 100 na Padol 5mg, kwayoyi 30 na Pregabalin 300mg, kwayoyi 170 na Diazepam 10mg, da kuma kwaya guda daya ta karin karfin maza.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan kamun na cikin dabarun hukumar wajen rushe kungiyoyin masu aikata laifuka da ke da hannu a satar kayayyaki, lalata dukiyoyin jama’a da sauran miyagun ayyuka da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.”
Abdullahi ya ce ana ci gaba da bincike a kan wadanda ake zargi, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala binciken.
A ranar 6 ga Nuwamba, jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa hukumar NSCDC ta Jihar Kwara ta kama mutane biyar bisa zargin satar igiyoyin wutar lantarki na transifoma da na fitilun titi a yankin Tanke da ke Ilorin.
Wadanda aka kama sun hada da Samson Akintola, Muhammed Zakariya, Mohammed Monsur, Ibrahim Hamida, da Kabir Abubakar.
An kama su ne da misalin karfe 1 na safe a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, yayin hadin gwiwar aikin jami’an NSCDC daga sashen Tanke Dibision da kuma Kungiyar Tsaro ta Bijilante ta al’ummar Tanke.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA