Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Published: 9th, November 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin.
Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin Olympics.
A nasu bangaren, Kirsty Coventry da Thomas Bach sun bayyana cewa, kwamitin wasannin Olympics na duniya yana godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da take bayarwa na tsawon lokaci, kuma suna fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, tare da inganta ci gaban harkokin wasannin Olympics, da kara yada ruhin wasannin na Olympics a duk fadin duniya, da karfafa hadin kai tsakanin al’ummomin dukkan kasashe, da kuma inganta zaman lafiya a duniya.
Kazalika, duk dai a wannan rana, Xi ya gana da wakilan rukunonin gwajin al’amura da na daidaikun mutane a fannin wasanni na kasa da na gasar wasannin motsa jiki, kafin bude gasar wasannin ta kasa ta karo na 15 a Guangzhou. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: wasannin Olympics gasar wasannin a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa November 8, 2025
Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi November 8, 2025
Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne November 8, 2025