Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso
Published: 15th, November 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewar Muhammadu Sanusi II ne, halastaccen Sarki a hukumance
Ya bayyana haka ne a ranar Asabar, a lokacin bikin yaye ɗalibai karo na huɗu a Jami’ar Skyline University of Nigeria (SUN) da ke Kano.
Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94“Muhammadu Sanusi II shi kaɗai ne Sarkin Kano a wajen mutane da gwamnatin jiha.
A cewarsa, duk wanda wasu suka naɗa a matsayin Sarki ba shi da ƙima a idon al’ummar Kano da gwamnatin jihar.
Kwankwaso, wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP a 2023, ya yaba wa jami’ar saboda samar da ingantaccen ilimi.
Ya shawarci matasa su dage wajen neman ilimi domin nan na gaba za su iya jagorantar ƙasar.
Yayin da yake magana kan rikicin masarauta a Kano, Kwankwaso ya jaddada cewa Muhammadu Sanusi II ne, Sarki halastacce.
Kwankwaso ya nuna damuwa kan hare-haren ’yan bindiga a KanoHaka kuma ya nuna damuwa game da ƙaruwa hare-haren ’yan bindiga daga Jihar Katsina da ke kai wa yankunan Tsanyawa, Shanono, Gwarzo da Karaye hare-hare.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki domin magance barazanar.
Ya ce idan gwamnati ba za ta iya kare rayuka da dukiyoyi ba, to lallai sai ta sake nazari kan yadda ta ke jagoranci.
Ya ƙara da cewa matsalar tsaro da ta samo asali a Zamfara ta bazu zuwa Sakkwato, Kebbi, Kaduna, sannan yanzu tana barazanar tsallakowa zuwa Kano da Jigawa.
“Idan gwamnati ba za ta iya kare rayuka da dukiyoyi ’yan ƙasa ba, to lallai dole ta zauna ta sake tunani. Matsalar tsaro da ta fara a Zamfara ta bazu zuwa Sakkwato, Kebbi, Kaduna, sannan yanzu tana barazana ga Kano da Jigawa.”
Kwankwaso, ya nuna yadda ya kashe maƙudan kuɗaɗe don samar da tsaro a lokacin da ya yi gwamna, sannan ya roƙi gwamnati mai ci ta shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta ƙara himma wajen kare ’yan Najeriya.
A nasa ɓangaren, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne jagoran Jami’ar, ya shawarci waɗanda suka kammala karatu da su zama masu gaskiya.
Ya ce ilimi ba shi da amfani idan ba a yi amfani da shi wajen kawo canji ba.
Ya nuna farin cikinsa kan samun mata da suka kammala karatu, inda ya yi fatan samun mata a harkokin shugabanci.
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Ajith Kumar V.V., ya bayyana cewa ɗalibai 24 daga cikin 180 sun samu sakamako mafi daraja.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwankwaso sarki Sarkin Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya
Cibiyar dake kula da noman dabino ta kasa a Iran, ta ce kasar ta zamo ta farko wajen fitar da dabino a duniya, inda take samar da tan miliyan 1.5 a kowace shekara.
Bayannin ya zayyana Kasashe goma mafiya samar da dabino a duniya wadanda su ne Masar, Saudiyya, Iran, Aljeriya, Pakistan, Iraki, Sudan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman, da Tunisiya, wanda ya nuna Iran na cikin kasashe na uku na farko.
Kuma a yadda Iran ke fitar da tan 430,000 na dabino a kowace shekara, hakan ya sa ta kasance ta farko wajen fitar da dabino a duniya, sai Saudiyya da tan 390,000 sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da tan 330,000.
Fitar da dabino daga Iran an kiyasta yana samar mata da kimanin dala miliyan 430, a nau’in dabino iri bakwai dake akwai a kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Kwamitin Tsaro ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya November 14, 2025 Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka November 14, 2025 Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu November 14, 2025 Abdoulaye Diop: ‘Yan Tawaye Ba Za Su Iya Mamaye Dukkan Kasar Mali Ba November 14, 2025 Ramaphosa Ya Caccaki Trump Kan Kauracewa Taron G20 A Johannesburg November 14, 2025 MDD ta nuna damuwa game da rahotannin kisan gilla a El Fasher November 14, 2025 Rasha Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Amurka November 13, 2025 Iran Da Qatar Sun Tattauna Kan Dangantakar Dake Tsakaninsu November 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci