UNICEF ta ce Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza
Published: 12th, November 2025 GMT
UNICEF ta yi gargadin cewa Isra’ila na hana shigar da muhimman kayan aikin da ake buƙata don allurar rigakafi a Gaza, wanda hakan ke kawo cikas ga ƙoƙarin isa ga yara a yankin da yaƙi ya daidaita.
Hukumar ta ce kayayyakin, ciki har da sirinji da ake amfani da su don allurar rigakafi na yau da kullun da kwalaben madarar jarirai, har yanzu suna nan a wuraren bincike, duk da ci gaba da tsagaita wuta da kuma ƙaruwar buƙatun jin kai.
UNICEF ta bayyana cewa a halin yanzu tana gudanar da Shirin allurar rigakafi ga yara ‘yan ƙasa da shekara uku, waɗanda da yawa daga cikinsu sun rasa allurar rigakafi na yau da kullun a cikin shekaru biyu da suka gabata na rikici.
Duk da haka, tana fuskantar matsala mai tsanani wajen samun damar yin amfani da sirinji miliyan 1.6 da firiji masu amfani da hasken rana da ake buƙata don adana allurar rigakafi da sauran kayyayaki na kiwon lafiya, inda har yanzu Isra’ila ta hana shiga da sub isa hujjar gudanar da bincike tun daga watan Agusta.
An fara zagayen farko na shirin allurar riga-kafi na UNICEF a ranar Lahadi, da nufin isa ga yara sama da 40,000 wadanda suka rasa kariya daga cututtuka kamar su shan inna, kyanda, da kuma ciwon huhu. A ranar farko da aka fara wannan shirin, an yi wa kimanin yara 2,400 da allurar riga-kafi yayin da dama kuma suke cikin layin jira.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministocin harkokin wajen kasashen yamma sun yi Allah wadai da ta’asar RSF a El Fasher Darfur November 11, 2025 Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya November 11, 2025 Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka November 11, 2025 Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita November 11, 2025 Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar November 11, 2025 Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar November 11, 2025 Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci November 11, 2025 Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Guda Uku Zuwa Sararin Samaniya November 11, 2025 Lebanon: An Saki Hannibal Kaddafi Bayan Zaman Kaso Na Shekaru 10 November 11, 2025 An Sake Bude Gidajen Mai Da Makarantu Da Aka Rufe A Kasar Mali November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: allurar rigakafi
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Qassem: Kawar Da Hizbullah Ne Babban Burin Isra’ila A Lebanon
Babban Sakataren Hezbollah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa “Amurka, ta hanyar wakilanta na Isra’ila, tana neman kawar da karfin gwagwarmayar Lebanon da kuma ba sojojin kasar makamai don fuskantar Hezbollah,” yana mai jaddada cewa manufar wannan matakin shine “kawar da karfin soja da duk wani karfi fadin Lebanon domin Isra’ila ta ci gaba da cin karenta babu babbaa duk inda ta ga dama a cikin kasar.”
Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa “An kafa Hezbollah ne bisa ka’idojin jihadi, kare mutunci mutunci, da alfaharin Lebanon, da goyon bayan Falasdinu,” yana mai cewa “daga 2000 zuwa 2023, mun kasance cikin yanayi na tsoro.”
Ya bayyana cewa yakin baya-bayan yana a matsayin shinge ga mamayar Isra’ila, wanda ya tsayar da hankoron mamayar Isra’ila kan Lebanon a wasu iyakoki a kudancin Lebanon,” yana mai nuna cewa “Yarjejeniyar Nuwamba tana da muhimmanci domin ya haɗa da tura sojojin Lebanon a kudancin Kogin Litani.”
Ya ƙara da cewa, “Mu masu nasara ne saboda sojojin Lebanon suna nan a kudancin Kogin Litani, domin su ‘ya’yanmu ne. Kuma mu masu nasara ne a cikin wannan yarjejeniyar saboda ƙasar ta yi alƙawarin cika alkawalin da ta dauka.”
Sheikh Qassem ya zargi Amurka da “kasa aiwatar da alkawullanta ta hanyar tursasa Isra’ila yin aiki da yarjejeniyar, domin Lebanon za ta dawo da ‘yancinta da mutuncinta ne kawai idan Isra’ila ta janye.” Ya jaddada cewa “Amurka da Isra’ila suna tsoma baki a cikin makomar Lebanon, suna tantance ayyukan sojojinta, tattalin arzikinta, siyasa, da matsayinta na yankin.”
Ya bayyana cewa “matsin lamba da ake yi wa gwamnati domin ta yi sassauci ba tare da wani lamuni ba, zai kara karfafa gwiwar Isra’ila ne wajen yin gaban kanta a kasar Lebanon.”
Sheikh Qassem ya ci gaba da cewa, “Isra’ila tana son ta mallaki Lebanon ta mayar da ita wurin da za ta kara faɗaɗa matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna, a matsayin wani ɓangare na Shirin kafa Isra’ila Babba.” Ya nuna cewa “kowace rana suna fito da sabbin hujjoji, tun daga batun kwance damarar makamai zuwa gindaya wa gwamnatin Lebanon sharudda masu tsauri kan Hizbullah, wanda hakan ke nuni da cwa Hizbullah da karfinta su ne Babbar matsala a gare su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar Da Sudan Sun Jaddada Wajabcin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin November 12, 2025 Venezuela: Maduro Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tsaron Kasa Mai Cikakkiyar Kariya November 12, 2025 UNICEF: Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza November 12, 2025 Ministocin harkokin wajen kasashen yamma sun yi Allah wadai da ta’asar RSF a El Fasher Darfur November 11, 2025 Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya November 11, 2025 Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka November 11, 2025 Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita November 11, 2025 Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar November 11, 2025 Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar November 11, 2025 Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci