Babi na 25 na sabuwar doka ya shafi batun aure ga jami’ai da sojojin rundunar tsaro.

Musamman, Sashe na 5 na wannan takarda ya bayyana cewa “ba a yarda wani jami’i ya auri bakuwa ko kuma dan Nijeriya da aka ba takardar zama ba.”

 

Za A Sake Duba Daftarin HTACOS Bayan Shekara Biyar

Sabon Daftarin HTACOS na shekarar 2024, wanda Majalisar Rundunar Sojoji ta amince da shi, ya fara aiki ne a ranar 6 ga Disamba, 2024, lokacin da Shugaban Kasa ya sanya wa takardar hannu.

A cewar Babi na 25, Sashe na 1, dan karamin jami’i mai mukamin Second Lieutenant, Midshipman ko Pilot Officer (2Lt/Mid/Plt Offr) yana cikin lokacin gwaji ne, kuma ana tsammanin zai zauna a gidan jami’ai (Officers’ Mess) ba tare da matar aure ba.

Haka kuma, ba a yarda ya yi aure ba, kuma idan ya riga ya yi aure kafin ya shiga makarantar horo, duk da cewa hakan yana cikin bayanansa, ba za a dauke shi a matsayin jami’in da ya yi aure ba dangane da batun masauki, albashi, da sauran alawus-alawus da ake bai wa jami’an da suka yi aure.

Sai dai, Sashe na 2 na wannan babi ya bayyana cewa, “idan wani soja, jami’in ruwa ko jami’in sama ya samu matsayi na jami’i a cikin kowace runduna ko reshe a matsayin Second Lieutenant, Midshipman ko Pilot Officer (2Lt/Mid/Plt Officer), kuma yana da aure kafin a daga darajarsa, zai zauna a gidan jami’ai (Officers’ Mess) na tsawon akalla watanni uku. Bayan haka, ana iya ba shi gida na jami’an da suka yi aure idan akwai, ko kuma a ba shi kudin haya a madadin haka.”

A cewar doka, kafin aure, jami’ai dole ne su nemi amincewar manyan hukumomi tare da gabatar da abokan aurensu domin binciken cancanta.

Babi na 25, Sashe na 3–4 ya bayyana cewa: “Duk wani jami’i da bai yi aure ba dole ne ya fara neman izinin hukumar da ta dace kafin ya yi niyyar aure. Jami’in RCC ba zai cancanci neman aure ba sai bayan shekaru biyar da samun mukamin jami’i.”

Amincewar za ta kasance ne kawai bayan an kammala bincike da tantancewar matar da jami’in yake son aura ta hannun hukumarta ta sama da ta dace.

“Idan wani jami’i ya auri soja, jami’in ruwa, ko jami’in sama (namiji ko mace) a karkashin kowace dokar da ke akwai, za a ba jami’in ko wannan soja/jami’in damar yin ritaya daga Rundunar daga ranar wannan aure. Idan ma’aikatan da suka yi aure ga juna aka daga darajarsu, matar aure ko mijin jami’in da aka daga darajarsa za a sallame shi daga Rundunar.”

Laifi ne ga wani jami’i ya boye aurensa da soja, jami’in ruwa, ko jami’in sama (namiji ko mace) domin hana jami’in ko wannan soja/jami’in yin ritaya daga Rundunar.

 

Dalilin Da Ya Sa Aka Bayyana Haka – Tsohon Janar

A halin yanzu, wani tsohon janar mai ritaya, da aya nemi a sakaya sunansa, ya ce dokar an kafa ta ne don hana sojoji bayyana bayanai ga kasashen waje ta hannun matansu ko mazansu.

Ya ce babu yadda wani jami’i zai guji tattaunawa da matarsa ko mijinta kan al’amuran aiki lokaci-lokaci, inda ya kara da cewa yin hakan tare da abokin aure bako na kasashen waje na iya kawo barazana ga dan kasar jami’in.

Ya ce, “Tabbas, dokar an kafa ta ne don kare bayanai da sauran al’amuran tsaro. Ka yi tunanin soja dan Nijeriya da ya auri bako dan wata kasa kamar daga Kamaru ko Laberiya, kuma Nijeriya ta shiga yaki da dayan wadannan kasashen, abin da ake tsammani shi ne cewa aminci na iya rabuwa ko wani abu makamancin haka. Idan aka yarda da hakan gaba daya, hakan ba zai amfani kasa ba daga bangaren tsaro.”

 

Tsohon Kwamandan Runduna Ya Ce A Sake Duba Dokar

Kwamandan Runduna Shehu Sadeek (mai ritaya) ya ce, duk da cewa wannan Daftari ya samo asali ne daga tsaron kasa, ya kamata a sake duba irin wannan doka bisa ga kyawawan hanyoyi da kasashe masu ci gaba ke bi, inda ake yin bincike kan abokin aure da aka nufa. Ya ce yawancin rundunonin soja a duniya suna da irin wadannan dokoki amma ba sa hana aure gaba daya.

Ya bayyana cewa HTCOS (Ka’idoji da Sharudan Aiki na Rundunar Sojoji) Daftari ne da rundunar kanta ta tsara don tsara yadda al’amuran cikin rundunar za su gudana, kuma ta bambanta da Dokar Rundunar Sojoji (Armed Forces Act).

A cewar sa, haramcin aure da baki gaba daya an kafa shi ne don hana yiwuwar barazanar tsaro saboda jami’ai na da damar samun bayanai masu muhimmanci. Ya kara da cewa wannan tanadi ya samo asali ne daga la’akari da tsaron kasa, ba daga son ra’ayi ko al’adu ba.

Ya ce aure da bako na iya samar da hanyar bayyana sirrin kasa ba da gangan ba.

Na biyu, ya ce haramcin yana da alaka da dan kasa da biyayya, inda ya kara da cewa “dan kasar bakon abokin aure na iya haifar da tambayoyi game da biyayya biyu, kamar hakkin gado da hakkin zama, a hanyoyi da ka iya saba wa dokokin tsaron Nijeriya.”

Na uku, a cewarsa, shi ne hadarin tura jami’ai aiki da kuma matsalolin da ke tattare da wuraren aiki. Ya ce jami’ai da suka yi aure da baki na iya fuskantar takurawa lokacin da aka tura su kasashen waje, musamman idan suna rike da mukamai masu mahimmanci, watakila a fannin leken asiri, wanda ke kawo cikas ga gudanar da ma’aikata. Dalili na karshe da ya bayar shi ne alaka ta mayar da martani da dalilan diflomasiyya.

A cewar Shehu, yawancin rundunonin soja a duniya suna da irin wadannan dokoki. Sai dai ya bayyana cewa ba doka ce ta duniya ba, amma kuma ba ta musamman ga Nijeriya ba.

“Alal misali, a Amurka, babu wani haramci gaba daya, amma jami’ai a wasu hukumomi suna bukatar samun izinin tsaro kafin su auri bako. Duk da cewa ba a haramta gaba daya ba, ana bukatar bincike kan abokin aure da aka nufa.”

“A Birtaniya, ba sa haramta aure da bakon wata kasa, amma damar jami’in samun bayanai masu muhimmanci ana takaita ta har sai an kammala bincike kan abokin aure. Sin, Rasha, da wasu kasashe a Gabas ta Tsakiya da Afirka suna haramta shi a fili. Indiya da Pakistan kuma suna bukatar amincewa kafin aure,” in ji shi.

“Watakila, idan aka duba abin da ke faruwa a sauran sassan duniya, ina ganin za mu iya sake duba wannan doka don gabatar da hanyoyin bincike kafin a yi irin wannan aure maimakon haramtawa gaba daya.

An kafa wannan doka ne a lokacin mulkin soja; sabbin jami’ai na iya ganin irin wadannan sharuda a matsayin tauye hakkokinsu. Ina ganin wannan wani fanni ne da rundunar za ta iya dubawa, ganin abin da ke faruwa a sauran kasashe,” in ji shi.

Binciken da aka gudanar ta Inatanet ya nuna cewa a rundunar sojin Amurka, jami’ai suna da ikon yin aure da ‘yan kasashen waje, amma dole ne su sami takardar izinin tsaro.

Ana bukatar su sanar da hukumarsu game da dangantakar auren, kuma ana la’akari da wannan aure a yayin yanke shawara kan batun izinin tsaro.

Da yake mayar da martani kan dokar da ke hana sojojin Nijeriya yin aure da ‘yan kasashen waje, Daraktan Cibiyar Albarkatun Dan’Adam da Ilimin Jama’a (CHRICED), Dokta Zikirullahi Ibrahim, ya soki wannan doka.

Ya ce irin wannan ka’ida ya kamata ta shafi mutanen da ke da manyan mukamai kawai, kamar Shugabannin Rundunoni wadanda ke da damar shiga bayanai masu mahimmanci, ba duk wanda ke cikin rundunar soja ba.

A cewarsa, “Idan aka ce ‘yan rundunar soja ba za su yi aure da ‘yan kasashen waje ba, me ya sa za a ware su daga sauran jami’an gwamnati? Ina tambaya, yaya game da ‘yan Nijeriya a cikin rundunar soja da suka mayar da iyalansu kasashen waje?

“Iyalansu da yawa daga bisani suna samun zama ‘yan kasa a wadannan kasashe. Mun ga misalai da dama. Mafi yawan manyan hafsoshin mu na soja, iyalansu suna da fasfot biyu, na Nijeriya da na wata kasa. To me muke yi game da wannan lamari?”

Ya kara tambayar dalilin da ya sa irin wannan doka ba ta shafi ‘yan siyasa ba.

Ya ce, “Yaya game da ‘yan siyasa? Da dama daga cikinsu suna da fasfot biyu (dual citizenship). To me ya sa sai sojoji ne kawai ake warewa? Ashe ba ‘yan kasa ba ne su ma?

“Idan har muna son tsaftace tsarin gwamnati, babu wani reshe na gwamnati da ya kamata a ware shi. Ba za ka yi doka ga rukuni daya, sannan ka yi wata doka daban ga wani rukuni ba.

“Ya kamata a samu daidaito wajen kirkirar manufofi, domin a karshe ba za ka kirkiri doka da ba za a iya aiwatar da ita ba, wacce kuma ba za ta yi tasiri ba.”

Ya jaddada cewa irin wannan takurawa ya kamata ta shafi mutanen da ke neman mukamai na jagoranci kawai.

A cewarsa, wadanda ake tunanin za a nada su a matsayin shugabannin runduna ne kadai ya dace a hana su yin aure da ‘yan kasashen waje.

Ya kara da cewa, “Soyayya da kauna ba su kamata su kasance karkashin dokokin dan’Adam ba.”

Ya ce, “Dangantakar soyayya aiki ne na Allah. Za mu iya samun doka gaba daya wadda za ta ce wasu mukamai ba za a bari su rika mutane masu fasfot biyu, ko ‘ya’ya, ko mata ko miji masu fasfot biyu ba. Wannan zai sa mutane su zama masu hankali, su kuma fahimci al’amuran kasa, domin za su san cewa ‘idan na kasance da wannan, akwai iyaka a ci gaban aikina.’”

Sai dai Daraktan CISLAC (Cibil Society Legislatibe Adbocacy Centre), Auwal Rafsanjani, ya nuna goyon bayansa ga takaita aure ga jami’an soja masu aiki.

A cewarsa, mutanen da ke irin wadannan mukamai suna da bayanai masu mahimmanci na kasa, don haka ya kamata su yi la’akari da muradun kasa wajen zabar abokan aure.

Ya ce, “A ganina, idan kana rike da mukamin tsaro mai matukar muhimmanci, lallai zai zama hadari ka yi aure ko ka rike dangantaka da mutum daga wata kasa daban, wanda watakila zai iya fallasa irin wadannan bayanai.”

Ya ce, “Don haka idan ka yanke shawarar zama jami’in tsaro, to ka riga ka san sakamakon hakan. Ban yi imani cewa irin wadannan mutane ya kamata su rike dangantaka wadda za ta iya fallasa bayananmu masu mahimmanci ba.

“Idan ka yanke shawarar zama jami’in tsaro, tun kafin ka shiga aikin, ka riga ka san irin sadaukarwa da gata da ke tattare da ita.

Saboda haka, a ganina, tun daga farko, ya kamata mutane su san wadannan abubuwa. Sun riga sun san akwai wasu bayanai da dole su kasance a boye saboda tsaron kasa.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna November 8, 2025 Rahotonni Jerin Gwarazan Taurarinmu! November 7, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yan kasashen waje Ya kara da cewa Ya bayyana cewa ya kara da cewa ya bayyana cewa irin wadannan bayanai masu irin wannan wannan doka wani jami i

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Nsukka ta ce Gwamnatin Tarayya na lalata makomar ƙasar nan saboda rashin cika yarjejeniyar 2009.

A taron manema labarai da ta gudanar a Jami’ar Jihar Benuwe da ke Makurdi, Kodinatan yankin, Kwamared Christian Opata, ya ce gwamnati ba ta jajirce wajen magance matsalolin da suka shafi ɓangaren ilimi.

Ya yi magana ne a madadin jami’o’i takwas da ke yankin.

Opata, ya ce an tattauna tare da ƙumla yarjejeniyoyi da dama tsakanin ASUU da gwamnati tsawon shekaru, amma babu wani ci gaba da aka samu.

Ya zargi jami’an gwamnati da yin lƙawarin ƙarya da gangan.

Ya ce ASUU ta dakatar da yajin gargaɗin da ta yi kwanan nan saboda ɗalibai, iyaye, da ƙungiyoyin ƙwadago, amma har yanzu gwamnati ba ta ɗauki aniyar warware matsalar ba.

Opata, ya gargaɗi gwamnati cewa idan ba ta kammala tattaunawar cikin wata ɗaya ba, jami’o’i na iya sake tsunduma yajin aiki.

ASUU, ta kuma zargi wasu jami’an gwamnati da yaɗa bayanan ƙarya game da tattaunawar, musamman batun biyan bashin albashi da wasu kuɗaɗen da aka riƙe musu.

Kungiyar ta ce Najeriya na da isasshen kuɗi, amma gwamnati ce ba ta yi niyyar saka hannun jari a ilimi.

Sun roƙi sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin ƙwadago, ɗalibai, da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su matsa wa gwamnati lamba don ganin an daidaita abubuwa.

ASUU ta ce malamai na cikin tsaka mai wuya saboda ƙarancin albashi, kuma ba ya isarsu wajen al’amuransu na yau da kullum.

Ƙungiyar ta sake jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta cika alƙawarun da ta ɗauka a baya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU
  • Mutum ɗaya ya rasu yayin da ’yan sanda da ’yan bindiga suka yi artabu a Kwara
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani
  • An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya
  • An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe
  • MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC
  • Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
  • Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro
  • AIG Zubairu Ya Umurci ‘Yan Sanda a Kwara Su Ninka Kokarinsu Don Karfafa Tsaro