John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi
Published: 11th, November 2025 GMT
Shahararren ɗan wasan wrestling, John Cena, ya samu nasarar lashe kambun Intercontinental a karon farko a tarihinsa.
Cena ya lashe kambun ne da yammacin jiya Litinin, bayan ya doke Dominic Mysterio a birnin Boston, ƙasar Amurka.
Sanata Jarigbe ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Kotu ta sake dakatar da babban taron PDPDa wannan nasarar, yanzu John Cena ya cika burinsa na lashe dukkan manyan kambuna da ake bugawa a gasar wrestling.
Ɗan wasan mai shekaru 48, wanda ake sa ran zai yi ritaya a watan Disamba mai kamawa, ya zuwa yanzu ya lashe kambuna 17 a gasannin daban-daban da ya shiga.
Tuni dai Cena ya bayyana cewa bayan ritayarsa zai mayar da hankali wajen fitowa a fina-finan Hollywood, kuma ana tsammanin zai gwabza wasansa na ƙarshe a ranar 13 ga watan Disamba, 2025.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa.
Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia.
An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP ’Yan bindiga sun sace mata 5 a KanoA cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan dawo in sake taka leda a nan gaban masoyana kafin in yi ritaya.”
A shekarar 2021 Messi ya bar Barcelona bayan matsalolin kuɗi da suka dabaibaye kulob ɗin, inda ya koma Paris Saint-Germain (PSG) ta Faransa, kafin daga bisani ya sauya sheƙa zuwa Inter Miami ta Amurka bayan shekaru biyu.
Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau takwas, ya ƙara da cewa ziyarar da ya kai Camp Nou ta sake jaddada masa irin farin cikin da yake ji a duk lokacin da yake wannan fili.
“Camp Nou wuri ne da yake sa ni farin ciki matuƙa. Ina fatan zan dawo ba wai kawai don yin bankwana ba, har ma don sake taka leda a matsayin ɗan wasa.”