Bayan hukunci, kwamitin gudanarwa karkashin shugabancin Damagum ta dakatar da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu da mashawarcin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade da sakataren shirye-shirye na kasa, Umar Bature na tsawon wata guda saboda zargin ayyukan da ke goyon bayan abin da ya saba wa jam’iyya.

Bayan awanni 24, Anyanwu da magoya bayansa sun hadu a Abuja suka sanar da dakatar da Damagum da dukkan mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.

Sun kuma bayyana sunan mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Arewa ta tsakiya, Abdulrahman Mohammed, a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam’iyya kasa.

Yayin da bangarorin biyu suke kalubalantar junansu, bangaren da Damagum ke jagoranta ya samu umurnin alkalin babban kotun Jihar Oyo, Ladiran Akintola, wanda ya umartar PDP da ta ci gaba da gudanar da taron babban taronta na kasa.

Saboda haka, yayin da Damagum wanda gwamnoni da mambobin kwamitin amintattu da shugabannin jihohi ke goyon baya ke shirin taron, Wike da Anyanwu da wasu sun dage cewa taron ba zai gudana ba.

A sa’ilin da yake magana da ‘yan jarida a ranar Lahadi, wani jami’i a ofishin PDP mai masaniya kan rikicin, ya ce za a taru da wakilai sama da 3,000 a Ibadan don zaben sabbin shugabanni na jam’iyyar.

Ya ce, “Fiye da wakilai 3,000 ne za su raba gardama, kuma ka da ka manta cewa akwai manyan mukamai da za a zaba.

“Lokacin da ka ji mutane waɗdanda abin da suke sha’awa kawai shi ne hallaka jam’iyya suna cewa ba a gudanar da tarukan jam’iyya a wasu jihohi ba, don haka wadannan jihohin ba su da ‘yancin zabe, karya ne dukkaninsu ne saboda har yanzu muna da tsoffin mambobi a wadannan jihohin.”

Wata majiyar wadda take tare da Damagum, ta ce taron zai gudana saboda umarnin Alkali Akintola wanda shi ne mafi girman hukuncin kotu guda biyu da suka bayar.

Ya kara da cewa, “Akwai umarnin kotu guda biyu daga kotunan da ke sauraron shari’ar. A doka, jam’iyya na da ‘yanci ta zabi wanne daga cikin umarnin za ta bi, yayin da wasu lauyoyi ke cewa umarnin karshe (ko na baya-bayan nan) shi ne mafi inganci tun da an bayar da shi daga babban kotun.”

Ya ce bayan an dakatar da Anyanwu daga shugabancin jam’iyya, an ganshi a matsayin mai jagorantar wata kungiya mai batanci, yana kara da cewa, “Duk wanda ke mai da hankali ga kungiyar yana yin hakan ne saboda dalilai na siyasa.

“A bisa tsarin kundin tsarin mulkin PDP, taron kwamitin gudanarwa yana gudana ne bisa umarnin shugaban jam’iyya na kasa, kuma shugaban jam’iyyar na kasa a wannan yanayin shi ne Umar Damagum.

“Dangane da abin da ke sama, daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa guda 17 da suka rage, 14 ne suka gana a ranar 1 ga Nuwamba, 2025, suka dakatar da Anyanwu, Bature, Ajibade, da mataimakin mai ba da shawara na kasa a harkokin shari’a, Okechukwu Onuoha.”

Ya yi kira ga kafofin watsa labarai da su daina kiran bangaren da Wike ke jagoranta a matsayin wata bangare na jam’iyyar. Yana bayyana cewa dole ne a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa, kuma dole ne mambobi su fita a filin taron a wuri daya da rana daya, ba abin da Wike da magoya bayansa za su iya yi.

A halin yanzu, Sanata Anyanwu ya ce taron Ibadan ba zai gudana ba. Ya kara da cewa idan wasu shugabannin jam’iyya suka ci gaba da gudanar da shi, INEC ba za ta sa ido a kai ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya November 7, 2025 Tambarin Dimokuradiyya Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta October 17, 2025 Tambarin Dimokuradiyya 2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara October 17, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kwamitin gudanarwa shugaban jam iyya a gudanar da

এছাড়াও পড়ুন:

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila da Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ziyarci zauren Majalisar Wakilai ranar Alhamis domin shaida sauya sheƙar ƴan majalisa biyu daga NNPP zuwa APC.

Ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Hon. Abdulmumin Jibrin, wanda ke wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, da Hon. Sagir Koki, wakilin Kano Municipal.

A cikin wasiƙunsu da Kakakin Majalisar Abbas Tajudeen ya karanta, sun bayyana rikici mai sarƙakiya da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar NNPP a matsayin dalilin barin jam’iyyar zuwa APC.

ADVERTISEMENT

Duk da jayayya da Hon. Kingsley Chinda daga bangaren marasa rinjaye, wanda ya dage wajen ɗaga batun sanarwar a lokacin karanta wasiƙun da karɓar sauya shekarun, Kakakin Majalisar bai amince da buƙatarsa ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su November 13, 2025 Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule November 13, 2025 Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista November 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa
  • Ramaphosa Ya Caccaki Trump Kan Kauracewa Taron G20 A Johannesburg
  • Dalilin da ya kamata PDP ta jingine taron da za ta gudanar— Saraki
  • NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna
  • Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2
  • NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane
  • Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP
  • PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu
  • An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba