PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu
Published: 12th, November 2025 GMT
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana kudurinta na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na kasa da aka tsara a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba.
Hakan na zauwa ne duk da sabon umarnin kotun tarayya da ke hana ta ci gaba da shirya taron.
Yadda muka daƙile yunƙurin tsige Akpabio daga shugabancin Majalisa – Orji Kalu DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’ummaMataimakin Sakataren Yada Labarai na kasa na jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa hukuncin kotun da ke dakatar da taron “bata lokaci ne kawai,” yana mai jaddada cewa jam’iyyar na bin hukuncin da kotun koli ta yanke a baya wanda ke tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa suna da ikon gudanar da harkokinsu na cikin gida ba tare da tsoma bakin kotu ba.
Wannan bayani na Abdullahi ya biyo bayan hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu na Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar Talata, inda ya hana PDP gudanar da taronta.
Wannan umarni ya saba da hukuncin da Kotun jihar Oyo ta yanke, wanda ya ba jam’iyyar damar ci gaba da shirin taron, lamarin da wasu masana shari’a suka bayyana a matsayin tufka da warwara.
A martaninsa ranar Talata, Abdullahi ya ce PDP ba za ta sake yarda da “hukuncin da aka samo da gangan” ba, yana mai cewa jam’iyyar PDP ‘yan Najeriya ne suka kafa, ba kotu ba.
“Hukuncin bata lokaci ne. Mun yi nisa sosai da ba za a iya dakatar da mu ba,” in ji shi.
“Ba kotu ce ta kafa mu ba, ‘yan Najeriya ne suka kafa mu, kuma su ne ya kamata mu saurara, ba hukuncin da aka samo da gangan ba.
“Ba za su iya dakatar da mu ba. Muna da hukuncin kotun koli da ke cewa harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa suna karkashin ikon su ne kawai, kuma muna bin wannan doka. Ko da wani ya yi watsi da hukuncin Kotun Jihar Oyo da ta ba mu damar ci gaba, ba zai iya watsi da hukuncin kotun koli ba. Ba za mu ci gaba da bin sabanin hukuncin kotuna ba. Mun yi nisa sosai; ba za a dakatar da mu ba.
“Su jira sai bayan mun kammala, sai su gwada kin amincewa da shi, idan za su iya. Duk da haka, suna da damar daukaka kara, amma mu mun yi gaba,” in ji shi.
A gefe guda kuma, tuni mambobin Kwamitin Shirya Babban Taron Kasa na PDP (NCOC) sun kai ziyara Ibadan a ranar Talata domin duba wurin da za a gudanar da taron.
Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo, Barista Bayo Lawal, wanda ke shugabantar kwamitin wurin taron na Babban Taron PDP na 2025, ne ya jagoranci duba wurin a Filin Wasa na Lekan Salami.
Kwamitin ya kuma gudanar da taro da masu kula da filin wasan da ‘yan kwangila domin kammala shirye-shiryen kayan aiki kafin taron da ake sa ran yi a ranar Asabar mai zuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban taro
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Yi Barazanar Maka BBC A Kotu Tare Da Neman Diyyar $1bn
Tawagar lauyoyin Trump ta ce an ɓata masa suna da mutunci, inda ta bayyana cewa BBC ta yi hakan ne don siyasa.
Trump ya taɓa shigar da ƙorafe-ƙorafe makamantan wannan a kan wasu manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka, ciki har da ABC, CBS, da The New York Times, bisa zargin yaɗa labaran ƙarya a kansa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA