An kama diraben da ke jan motar Shafiu Sharp-Sharp, domin yi masa tambayoyi.

“An riga an fara bincike. Ana yi wa direban tambayoyi, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke duba bidiyon CCTV,” in ji wata majiya.

“An miƙa bayanan motar ga jami’an tsaro domin su gano motar da kuma kama ɓarawon.”

Kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bai amsa kiran waya da saƙonnin da aka tura masa ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025 Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina November 11, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Ministan Yada Labarai Alhaji Mohammed Idris, ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa jagoranci na gaskiya da tsari, yana mai cewa Jihar Jigawa ta zama abin koyi wajen gudanar da mulki da kuma ingantaccen aiki a ma’aikatu.

Ministan ya yi wannan yabo ne lokacin wata ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan a Gidan Gwamnati da ke Dutse.

Muhammad Idris ya tuna da wata ziyarar da ya taba kaiwa Jigawa a baya, lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin duba harkokin noma. Ya ce yadda ya ga ana yin noman rani ya sa shi shauki game da irin ci gaban da ake samu a jihar.

Ya kuma bayyana godiyarsa kan kyakkyawan tarba da tawagarsa ta samu, yana mai cewa Jigawa jiha ce mai mutunci, zumunci da karimci.

Ministan ya kara tabbatar da aniyar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki, musamman ta hanyar gyaran da ake yi a rundunar tsaro domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yi maraba da ministan da tawagarsa, yana mai bayyana cewa taron matasan APC na Arewa maso Yamma wata dama ce ta musayar ra’ayi game da mulki, ci gaba da kuma bunkasar matasa.

Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen bunkasa karkokin matasa da mata a cikin tsarin shirye shiryenta na cigaban jihar.

“Muna goyon bayan mulikin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Mutanen Jigawa suna tare da shi, muna goyon bayan shirin sa na ‘Renewed Hope’ domin gina Najeriya mai da hadin kai,” in ji gwamnan.

Daga nan sai gwamnan tare da ministoci suka halarci taron matasan APC na Arewa maso Yamma a Dutse, inda aka tattauna batutuwan shugabanci, gudunmawar da matasa ke badawa, da ci gaba mai dorewa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Filin Jirgin Sama Na Kano
  • Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal
  • Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar
  • HOTUNA: Yadda Gobara Ta Ƙone Shaguna 25 A Kasuwar Singa A Kano
  • Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano
  • Gwamnatin Kaduna Za Ta Ɗauki Ma’aikatan Lafiya 9,000 Cikin Shekaru 5 – Maiyaki 
  • Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL