Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25
Published: 13th, November 2025 GMT
1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo
Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari a gaba.
Ko da yake ƙungiyar sau da yawa tana saumn rinjayan samun kwallo da kirkirar damar kai hari, amma kash suna gaza amfani da waɗannan damarmaki zuwa nasara.
2. Tallafin Gwamnati — Jin Dadi Ba Tare da Tasiri Ba
Ba kamar mafi yawan ƙungiyoyi a gasar NPFL ba, Pillars suna samun cikakken tallafi na kudi da walwala da duk goyon bayan da suke bukata daga Gwamnatin Jihar Kano. Albashi da ƙarin lada (bonus) suna samu a kai a kai, kuma wuraren horonsu yana ɗaya daga cikin mafi kyau a arewacin Nijeriya. Sai dai jin dadi ya gaza nunawa a cikin fili.
Samun jin daɗi ga kuma rashin nasara ya nuna cewa motsa sha’awa a ƙwallon ƙafa ba kawai maganar kudi ce ba, yana bukatar babban buri daga kungiya da yan wasa, da hangen nesa, da sha’awar yin nasara a aikace. Wasu ‘yan wasan ba su da yunwar kafa wani sabon tarihi, ba su da babban burin samun wata dama ko nuna kansu ko kuma fito da sunansu.
3. Tsoma Baki a Shugabanci
Wani muhimmin dalili da ya cefa ƙungiyar cikin wannan mummunan hali shi ne tsoma baki a shugabanci da yadda ake tafiyar da kungiyar. Wasu bayanai sun nuna cewa ana matsa lamba ga masu horarwa kan zaɓin ‘yan wasa, ko salon dabarun shiga fili a taka leda, da yayin sayen ‘yan wasa.
Wannan tsoma bakin yana rage amincewa daga magoya baya sosai, yana haifar da rikici na zaman doya da manja tsakanin yan wasan da wasu mahukunta, kuma yana hana masu horarwa aiwatar da amfani da dabarun da zasu iya kai wa ga nasara.
Ci gaba na gaske zai zo ne kawai idan kowa ya janye hannu ya bar ƙungiyar da masu horarwa su ɗauki cikakken hukunci da alhakin duk wani sakamako da ya biyo baya na nasara ko akasaninta.
4. Matsalar Gane Dabarun Ƙungiya
Idan aka kalli Pillars a yau, yana da wahala a iya bayyana wane dabaru su suke amfani da shi. Shin ƙungiya ce mai matsawa gaba-gaba (attacking)? Ko suna jiran dama don kai hari (counter attack)? Ko ƙungiya ce mai riƙe kwallo kamar Manchester city ko Barcelona?
Gaskiyar ita ce, suna haɗa komai amma ba ko yaushe ne ake iya ƙwarewa a komai ba. A yanzu sun haɗa komai ba tare da ƙwarewa a ko ɗaya ba.
Ta hanyar dogaro da wasannin baya na salon da suke amfani da shi na amfani da gefe da kuma yawan aika dogayen ƙwallo ta sama ya sa abokan taka leda sun gane Pillars Cikin sauƙi, musamman idan ana wasa da ƙungiyoyin da suke rufe gida sosai. Don dawo da martaba, ƙungiyar ana buƙatar sabunta dabaru da koyon saurin sauya salo idan wata dabara ta gaza aiki.
5. Matsin Lamba Daga Magoya Baya Da Koyon Sarrafa Fushi
Kano Pillars suna da magoya baya mafi ƙarfi a Nijeriya. Amma ƙauna na iya sauyawa zuwa matsin lamba. Wasannin gida a filin Sani Abacha, wanda a da ya kasance tsani mai tsoro gare su, amma a yanzu sun kasance da damuwa ga ‘yan wasa da ke tsoron fushin magoya baya a kowane wasan da suka yi rashin nasara.
Sarrafa tsammanin magoya baya ta hanyar magana a fili da nuna cewa nasara da rashin duk wani fanni na rayuwa da kuma a wasanni na da mahimmanci wajen dawo da ƙwarin gwuiwar masu kallo da kuma ɗakin sauya kaya.
A rubutu na biyu nazarina ya zurfafa cikin matsalolin tsarin fasalin ƙungiyar, al’adu, da wasu abubuwan ke hana ƙungiyar ci gaba tun daga damuwa kan lafiyar ‘yan wasa fargabar zuwan Azumin da ƙarancin ‘yan wasa a wasu sassan, da rashin tabbas na shugabanci, da buƙatar gaggawa yin hangen nesa don samar da ci gaba mai ɗorewa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: magoya baya
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP
Rahotanni na cewa rayukan mayaƙa 200 sun salwanta a sanadiyyar wani rikicin cikin gida tsakanin ’yan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne a yankin Dogon Chiku, kusa da Tafkin Chadi, a ranar Lahadi.
’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shiBayanai sun ce wannan dai na daga cikin rigingimun da suka fi zafi tun bayan da ɓangarorin suka yi hannun riga saboda saɓanin ra’ayi a shekarar 2016.
Wani ɗan sa-kai da ke taimaka wa dakarun Nijeriya wajen sa ido kan lamurran tsaro, Babakura Kolo, ya ce sun ƙirga gawarwakin aƙalla mayaƙa 200.
“Mun ƙirga aƙalla gawarwaki 200, mafi yawansu na bangaren ISWAP,” in ji shi.
Shi ma wani tubabben ɗan Boko Haram mai suna Saddiku, wanda ke bin diddigin lamurran ƙungiyoyin, ya tabbatar da faruwar rikicin.
A cewarsa, “an kashe aƙalla ’yan ISWAP 200, kuma an ƙwace makamai da dama. Sai dai daga ɓangaren Boko Haram an rasa mayaƙa huɗu kacal.”
Majiyoyin tsaro ma sun tabbatar da aukuwar rikicin, inda cikin farin ciki wata majiyar sirri ta ce, “muna da bayanan da suka nuna an kashe mayaƙa fiye da 150, kuma wannan abu ne da ke rage musu ƙarfi.”
Tun bayan rabuwa tsakanin Boko Haram da ISWAP a shekara ta 2016, ɓangarorin biyu sun riƙa kai wa juna farmaki lokaci zuwa lokaci, musamman a yankin Tafkin Chadi da wasu sassan Jihar Borno.