Aminiya:
2025-11-12@13:19:26 GMT

DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu

Published: 12th, November 2025 GMT

Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya.

Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja.

Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu

An shigar da ƙarar ne mai lamba FHC/ABJ/CR/610/2025, dangane da wasu rubuce-rubuce da matashin ya wallafa a shafinsa na X a watan Oktoban 2025.

A cewar DSS, waɗannan rubuce-rubuce sun nemi a kifar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki tare da nuna goyon baya ga sojoji su karɓi mulki a ƙasar.

Lauyan DSS, A.M. Danalami, ya shigar da ƙarar a ranar Talata, inda aka bayyana cewa ayyukan wanda ake zargin sun saɓa da sashe na 46A(1) da 59(1) na Dokar Manyan Laifuka ta Ƙasa, da kuma Sashe na 24(1)(b) na Dokar Laifukan Intanet ta 2024 (wacce aka yi wa gyara).

Daga cikin kalaman da ake zargin ya wallafa akwai: “Ana buƙatar juyin mulki a Najeriya. A kawar da APC, a dakatar da gwamnatin Najeriya, a shiga kungiyar AES. Wannan ne kawai muke buƙata yanzu.”

Haka kuma, ana zargin ya rubuta cewa: “A karshe zai faru,  yak u ’yan Najeriya. Sojoji na buƙatar goyon bayanku yanzu! Su kaɗai ne za su iya ceton ƙasar nan. Wanda ke Aso Rock ya sayar da ƙasar nan ga Turawa, su ke sarrafa sirrikanmu. Sojoji kaɗai za su iya sake daidaita ƙasar nan.”

A wani rubutu daban kuma ya ce: “Dole ne Tinubu ya tafi, kuma dole APC ta mutu kafin Najeriya ta samu daidaito.”

Ana sa ran za a gurfanar da Onukwume, wanda mazaunin Umusayo Layout ne a Karamar Hukumar Oyigbo ta Jihar Ribas a kotu cikin makon nan.

A watan Oktoba, an samu rahotanni da ke nuna cewa wasu jami’an sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Gwarzo Ta Kaddamar da Sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya

A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni.

Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da wakilan al’umma.

Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda Mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa kowane yanki a cikin karamar hukumar na da damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai sauƙin samu da araha.

Ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Ahmad Shehu Sabon Birni, da sauran kansiloli bisa hadin kai da jajircewarsu wajen aiwatar da muhimman ayyukan raya al’umma, yana mai cewa irin wannan haɗin gwiwa ita ce ginshiƙin ci gaban karkara mai dorewa.

A nasa jawabin, Ahmad Shehu Sabon Birni, ya bayyana sabuwar cibiyar lafiya a matsayin wata cibiya da za ta tallafawa jama’ar Dankado da makwabtansu. Ya jinjinawa karamar hukumar bisa mayar da hankali ga bangaren lafiya, tare da yin alkawarin ci gaba da ba da goyon bayan majalisa ga duk wani shiri da zai inganta rayuwar jama’a.

Shugaban sashen kula da kiwon lafiya na Gwarzo, Alhaji Tukur Makama, ya yaba da hangen nesa da jajircewar shugaban karamar hukumar wajen saka jari a fannin lafiyar jama’a. Ya ce sabuwar cibiyar za ta taimaka wajen rage mace-macen mata da jarirai, faɗaɗa rigakafi, da kuma samar da taimakon gaggawa ga al’umma cikin lokaci.

Shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa da na mata, sun bayyana godiyarsu, suna mai cewa aikin ya zo a kan kari kuma ya dace da bukatun jama’a.

Rel/Khadijah Aliyu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Gwarzo Ta Kaddamar da Sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya
  • Araghchi: Matsalar Yammacin duniya ita ce ci gaban kimiyyar Iran ba makaman nukiliya ba
  • Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar
  • Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni 9 Da Aka Zartarwa Da Hukuncin Kisa Shekaru 30 A Baya
  • EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jallo
  • Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC
  • Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu sa barazanar Trump– Jigon APC
  • Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump bisa zargin kisan Kiristoci