Faransa: An Fara Shari’ar Shugaban ‘Yan Tawayen DRC Bisa Laifuna Akan Bil’adama
Published: 13th, November 2025 GMT
A jiya Laraba ne aka bude shari’ar tsohon madugun ‘yan tawayen kasar DRC Roger Lombala a kasar Faransa bisa tuhumar da ake yi masa da aikata laifuka akan bil’adama a yayin yakin DRC na biyu. Ana kuma tsammanin cewa wannan shari’ar za ta dauki wata daya ana yinta.
A yayin zaman shari’ar za a gabatar da shaidu daga wadanda su ka cutu sanadiyyar ayyukan kungiyar ‘yan tawayen wacce Lombala ya jagoranta.
Wannan shi ne karon farko da za a yi wa dan kasar DRC shari’a a kasar Faransa bisa ka’idar hurumin shari’a na duniya.
Ofishin Fada Da Laifuka Aka Bil’adama ( OCLCH) ya kama Lombala ne a ranar 29 ga watan Disamba 2020 a birnin Paris. An kuma gabatar da shi a gaban kotu a ranar 2 ga watan Janairu 2021 inda aka tuhume shi da; “Kitsa makirci da zummar aikata manyan laifuka akan bil’adama” da kuma ” Makarkashiyar aikata laifuka akan bil’adama.”
A cikin watan Nuwamba na 2023 aka tuhumi madugun ‘yan tawayen a karkashin wani tsari da doka da yake bai wa wata kasa yin shari’a akan laifuka masu hatsari da aka tafka, ba tare da la’akari da inda inda aka yi laifukan ba.
Ana zargin Lombala da kungiyarsa da cewa ya aikata laufukan a tsakanin watan Oktoba na 2002 zuwa watan janairu na 2003 a karkashin kungiyarsa ta “Gamayyar ‘yan Demokradiyya da Masu Kishin Congo” wacce kasar Uganda take taimakawa. A wancan tsakanin kungiyar ta yi kokarin shimfida ikonta a yankin Bini wanda yake cike da ma’adanai a gundumar Itori ta gabas. Daga cikin laifukan nasu da akwai kisa da kuma fyade da wawason dukiyar al’umma.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya ( IEA) Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji November 13, 2025 Janar Ali Fadwi: Muna Aiki Tukuru Domin Sabunta Nisan Makamanmu Masu Linzami November 13, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Iran da Rasha sun Tattauna Gabanin Taron Gwamnonin IAEA November 13, 2025 Iraki: An Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar November 13, 2025 Kenya: An gano tarin zinari a karkashin kasa da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 November 13, 2025 Gaza: Hamas Ta Nemi Kawo Karshen Kisan Kiyashi Da Lamunce Shigar Da Taimako November 13, 2025 MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya November 13, 2025 Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Shugaban Iran Ya Aike Da Wasika Ta Musamman Zuwa Ga Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya November 12, 2025 Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa suna adawa da yunkurin kai hari kan Venezuela
Galibin Amurkawa na adawa da yunkurin gwamnatin kasar na neman kai harin soji kan Venezuela da sunan murkushe safarar miyagun kwayoyi.
Ayyukan sojin Amurka a yankin ya zuwa yanzu sun sanadiyar mutuwar mutane 87, sanann kuma ana gudanar da su ne ba tare da izini daga alkali ko kotuko kuma majalisar dokoki ba.
Binciken ya nuna cewa kashi 48 cikin 100 na wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun nuna adawa da da harin, yayin da kashi 34% ke nuna goyon bayansu, kuma kashi 18% ba su da ra’ayi.
Masu adawa da Shirin sun fi yawa a tsakanin ‘yan jam’iyyar Democrat, inda kashi 80% na ‘yan jami’iyar na adawa da wadanna ayyukan kashi 9% cikinsu ne kawai ke nuna goyon baya. A cikin ‘yan Republican, 67% sun goyi bayan harin, kuma 19% na adawa dashi.
Jin ra’ayin jama’ar na kwanaki shida, na zuwa ne a daidai lokacin da takun-saka ke kara ta’azzara tsakanin Washington da Caracas, kuma a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke la’akari da karin wasu hanyoyin soji da suka hada da kai hare-hare kan kasar, a daidai lokacin da Amurka ke zargin shugaban Venezuela Nicolas Maduro na da hannu a safarar miyagun kwayoyi. Maduro ya yi watsi da zargin baki daya, tare da bayyana shi a matsayin batu na siyasa zalla.
Hare-haren na baya-bayan nan da sojojin Amurka suka kai a kusa da Venezuela, wanda aka kaddamar a ranar 2 ga Satumba, 2025, karkashin Operation Southern Spear, ya haifar da cece-kuce bayan da aka kashe mutane 87 ba bisa ka’ida ba. Inda masana kan harkokin shari’a na kasa da kasa da kuma kungioyin kare hakkin bil adama suka bukaci da a gudanar da bincike kan lamarin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Najeriya: Majalisar Dattawa Ta Bawa Tunubu Damar Kai Sojoji Zuwa Kasar Benin December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci