Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-13@10:10:17 GMT

Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Dillalin Makamai A Taraba

Published: 13th, November 2025 GMT

Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Dillalin Makamai A Taraba

A ci gaba da aikace-aikacen yaki da ta’addanci da laifuffuka a fadin Jihar Taraba karkashin Operation Lafiya Nakowa, sojojin Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya / Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu nasarar kama wani wanda ake zargin dillalin makamai, tare da kwato makamai da harsasai daga hannunsa.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Lieutenant Muhammad, Mai Rikon Mukamin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar 6, ya sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, bisa sahihan bayanan leƙen asiri da aka samu, a ranar 12 ga Nuwamba, 2025, sojojin suka kai samame a kauyen Shagada, karkashin gundumar Namnai a Karamar Hukumar Gassol, Jihar Taraba. Samamen ya haifar da kama wani mutum mai suna Abdulmudallabi Audu, mai shekaru 25, wanda aka same shi da makamai da harsasai.

Kayan da aka gano daga hannun wanda ake zargin sun haɗa da Bindiga samfurin AK-47 guda ɗaya da kurtun harsasai AK-47 guda biyu da kuma Harsasai guda 53 masu tsawo mita kusan 8.

A yanzu haka, wanda ake zargin tare da kayan da aka kwato suna tsare a hedkwatar Runduna ta 6 domin bincike da shirin gurfanarwa a kotu.

Kwamandan Rundunar 6, Brigadier Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa sojojin bisa ƙwarewa, jajircewa, da saurin mayar da martani ga bayanan sirri da ake samu.

Janar Uwa ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aikace-aikace masu ƙarfi a duk fadin Taraba domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a Arewa maso Gabas da yankunan makwabta.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanai sahihai akan lokaci ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen kassara masu aikata laifuka da farfaɗo da cikakken zaman lafiya a jihar.

Sani Sulaiman/Jalingo

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.

 

Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.

 

Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.

 

Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da suka hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, bindiga kirar gida guda daya, harsasai 183, motoci uku, babura uku, babur mai kafa uku (Keke-napep) daya, da kuma dabbobi sama da 200 da aka sace.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa November 11, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya November 11, 2025 Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi
  • An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano
  • Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza
  • ’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina
  • Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina
  • Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe
  • ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Ta’adda Sun Fi Sojojin Nijeriya Yawan Makamai – Babachir
  • Sarkin Musulmi ya ba wa makarantu tallafin N1.3bn a Kebbi