HausaTv:
2025-12-13@13:21:47 GMT

Iraki: Hukumar Zabe Ta Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar

Published: 13th, November 2025 GMT

A yammacin jiya  ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar 2025, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci ta hanyar amfani da na’urorin lantarki.

A taronta na manema labarai, Hukumar ta bayyana cewa yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 56.

11% bayan samun sakamako daga kashi 99.98% na rumfunan zabe.

Wannan sanarwar ta zo ne sa’o’i 24 bayan kammala babban zaben da aka gudanar a wannan  Talata, da kuma zabe na musamman da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, domin zaben ‘yan majalisar dokokin Iraki na shekara ta 2025.

Jimillar masu kada kuri’a sun kai 20,063,773, tare da cibiyoyin zabe 8,703 da rumfunan zabe 39,285.

Hukumar ta ci gaba da bayyana cewa adadin masu kada kuri’a ya yi daidai dari bisa dari. Adadin sojoji da jami’an tsaron da suka cancanci kada kuri’a a zabukan na musamman ya kai 1,313,859, wanda aka raba a rumfunan zabe 4,501.

Ga ‘yan gudun hijira (IDPs), masu kada kuri’a 26,538 ne aka yiwa rajista a rumfunan zabe na musamman guda 97.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (IHEC) ta tabbatar da cewa aikinta ba ya nuna son kai ko Rashin sanin makamar aiki, kuma ta ci gaba da kasancewa mai kre hakkokin dukkan ‘yan takara da kuma ‘yan siyasa. Hukumar ta IHEC ta jaddada cewa ba za a iya daukaka kara a sakamakon farko ba kafin fitar sakamakon  karshe ba.

Hukumar ta tabbatar da cewa, za a sanar da sakamakon karshe bayan an warware korafe-korafe da bin kadunsu, inda ta ce an gudanar da zaben a dukkanin jihohin  kasar bisa ka’idojin kasa da kasa, tare da sanya ido sosai na jami’ai a cikin gida da waje.

Dangane da Bagadaza babban birnin kasar kuwa, hukumar ta IHEC ta bayyana cewa, adadin wadanda suka yi rajista ya zarce miliyan hudu, inda yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 48.76%.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kenya: An gano tarin zinari a karkashin kasa da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 November 13, 2025 Gaza: Hamas Ta Nemi Kawo Karshen Kisan Kiyashi Da Lamunce  Shigar Da Taimako November 13, 2025 MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya November 13, 2025 Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Shugaban Iran Ya Aike Da Wasika Ta Musamman Zuwa Ga Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya November 12, 2025 Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki November 12, 2025 Iran Da Pakistan Sun yi Kira Da Yin Aiki Tare Don Tunkarar  Makiyansu November 12, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Rikicin Yankin November 12, 2025 Gabon: An Daure Mata Da ‘Dan  Tsohon Shugaban Kasa Bongo Shekaru 20 A Gidan Yari November 12, 2025 Tanzania: MDD Ta Yi Kira Da A Yi Bincike Akan Daruruwan Mutanen Da Aka Kashe Sanadiyyar Rikcin Zabe November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza

Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Faidan ne ya bayyana cewa; kasarsa za ta iya daukar nauyin wararen matsalar Falasdinu, kuma a shirye take ta aike da sojoji zuwa yankin na Gaza idan bukatar hakan ta taso.

Fidan ya fada wa kamfafen watsa labaru cewa; Tukriya a shirye take ta yi duk abinda za ta iya yi, ta kuma dauki nauyin da ya dace akan batun Falasdinu.

A can Amurka kuwa, manzon musamman na Amurka akan harkokin yammacin Asiya, Barrack ya  fada wa jaridar  “Jerrusalem Post” cewa: Kasar Turkiya tana da sojoji masu karfi, kuma tana hulda da Hamas, a dalilin hakan shigarta cikin rundunar da za a aike Gaza, zai yi amfani.”

A ranar 18 ga watan Nuwamba ne dai kwamitin tsaro na MDd ya amince da rinjaye akan wani kuduri da Amurka ta gabatar domin kawo karshen yakin Gaza. A karkashin wannan kudurin zai a kuma aike da sojojin kasa da kasa daga nan zuwa karshen 2027.

Kudurin ya kuma tanadi cewa za a kafa gwamnati a yankin na Gaza ta kwararru wacce kwamijin tsaro ne zai rika kula da tafiyar da ita.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro  Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Yi Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi AkanDoron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu   December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na  Venuzuela
  • Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699
  • Birtaniya Ta yi  Barazanar Yanke Gudunmawar Da Take Bawa Kotun Duniya
  •  Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza
  • Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannun kan yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu
  • Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Hamsa: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjeniyar Tsagaita Bude Wuta A Yankin
  • Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan
  • Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila
  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky