Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce barazanar Amurka na amfani da karfi kan zababiyar gwamnatin Venezuela ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Ya kuma bayyana cewa irin wadannan ayyuka tamkar keta ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman haramta amfani da karfi.

A daya bangaren kuma, M. Baghai ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kai wa jiragen kamun kifi na Venezuela a matsayin misalai na kisan gilla ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma yi kira ga Washington da ta daina keta ikon kasar Venezuela a karkashin hujjar yaki da miyagun kwayoyi, sannan ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da Sakatare Janar António Guterres da su sauke nauyin da ke kansu na hana duk wani karin tashin hankali.

Amurka ta kai hare-hare akalla sau 20 kan kananen jiragen ruwa da take zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyi a yankin Caribbean da Pacific, Wadannan sukayi sanadiyyar mutuwar mutane 80.

Tun daga watan Agusta, Amurka ta tura jiragen ruwa a yankin ciki har da katafaren jirin nan na sojojin ruwan ta mafi girma a duniya USS Gerald R. Ford da jiragen yaki samfarin F35 da dubban sojoji zuwa yankin Caribbean, bisa fakewa da yaki da kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi na Latin Amurka.

Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya yi watsi da zargin hannu a safarar miyagun kwayoyi, yana mai jaddada cewa Washington tana amfani da batun don ci gaba da shirinta na “canjin gwamnati” da kuma kwace arzikin mai na Venezuela.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025  Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin  Da Kotu  Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025  An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a yankin Caribbean miyagun kwayoyi

এছাড়াও পড়ুন:

Rasha Ta yi Gargadin Cewa Za ta Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Amurka

Rahotanni sun bayanna cewa kakakin fadar kremlin Dimitry peskov yayi gargadi game da barazanar baya yana nan da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubios yayi da cewa akwai yiyuwa Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya.

Ci gaba da gwajin nukiliya ga Amurka zai kara fadada zaman dardar a duniya, kuma zai kawo cikasa ga kokarin shawo kan yaduwar makamai na tsawon shekaru da ake yi, sannan ya sake farfado da fargabar sake shiga sabuwa gasar makamai a dangantakar Amurka da rasha da ta riga ta tabarbare

Idan ana iya tunawa a ranar 29 ga watan oktoba ne shugaban Amurka Donald trump ya umarci maaikatar tsaron  Amuka da ta ci gaba da gwajin nukiliya  wanda yake nuna yiyuwar samun sauyi a manufofin Amurka.

A ranar 5 ga watan nuwamba shugaban kasar rasha viladimir putin ya umarci ministocinsa da su fara shirin uiyuwar dawo da gwajin nukiliya dominmayar da martani ga shirin Amurka

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Iran Da Qatar Sun Tattauna Ta Wayar Tarho Kan Dangantakar Dake Tsakaninsu November 13, 2025 Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Sun Kona Masallaci A Yammacin Kogin Jodan November 13, 2025 November 13, 2025 Iran da china Za su Yi Bikcin Cika Shekaru 55 Da Huldar Diplomasiya Tsakaninsu November 13, 2025 Faransa: An Fara Shari’ar Shugaban ‘Yan Tawayen DRC Bisa Laifuna Akan Bil’adama November 13, 2025 Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya  ( IEA)  Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji November 13, 2025   Janar Ali Fadwi: Muna Aiki Tukuru Domin Sabunta Nisan Makamanmu Masu Linzami November 13, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Iran da Rasha sun Tattauna Gabanin Taron Gwamnonin IAEA November 13, 2025 Iraki: An Fara Sanar Da Sakamakon Farko Na Babban Zaben Da Aka Gudanar November 13, 2025 Kenya: An gano tarin zinari a karkashin kasa da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 November 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba
  • Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana
  • Gaza: Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro don amincewa da shirin zaman lafiya na Trump
  • AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro
  •  Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin
  • Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin
  • Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka
  • Rasha Ta yi Gargadin Cewa Za ta Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Amurka
  • Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya  ( IEA)  Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji