Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan
Published: 15th, November 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin November 15, 2025
Daga Birnin Sin Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya November 14, 2025
Daga Birnin Sin Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba November 14, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan
Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis.
WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin yankin, da safiyar ranar.
HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman RaniWasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ce rubuce-rubucen da aka fesa da fenti sun haɗa da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da harshen Ibrananci.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan zargin.
Babu rahoton rauni ko mutuwa a lamarin kawo yanzu, amma bidiyon da ke yawo a kafafen yada labaran Falasɗinu da Isra’ila sun nuna lalacewar masallacin.
Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana harin a matsayin “mai matuƙar daure kai.”
Herzog ya ce wannan laifin da “ƙalilan daga cikin masu laifi” suka aikata ya “saba ka’ida,” inda ya ƙara da cewa “dukkan hukumomin gwamnati dole su ɗauki mataki mai ƙarfi don kawar da wannan dabi’a.”
Babban hafsan sojin Isra’ila, Laftanar Janar Eyal Zamir, ya goyi bayan suka da Herzog ya yi, yana mai cewa rundunar soji “ba za ta lamunci ayyukan wasu ’yan ƙalilan masu laifi da ke bata sunan jama’ar da ke bin doka ba.”
Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya (UN), Antonio Guterres, a ranar Alhamis, ya la’anci harin da Yahudawan masu haramtattun gidajen suka kai kan masallaci a yankin wanda Isra’ila ta mamaye.
Tashin hankali daga Yahudawa masu ra’ayin rikau kan Falasɗinawa a yankin ya ƙaru tun bayan fara yaƙin Gaza a watan Oktoban 2023, wanda aka fara bayan hare-haren da Hamas ta jagoranta kan Isra’ila.
Tun daga lokacin, an samu ƙaruwar hare-haren da ke haddasa mutuwa tsakanin Falasɗinawa da sojojin Isra’ila a yankin na Yammacin Kogin na Jodan.
Rundunar sojin Isra’ila na yawan fuskantar zargi kan gazawarta wajen ɗaukar mataki mai ƙarfi kan tashin hankalin da Yahudawa ke haddasawa.