2025-09-24@13:12:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 930

«Birnin Gwari»:

    A ranar Talata, 1 ga Rabi’ul Thani 1447H, daidai da 23 ga Satumba 2025, Allah Ya yi wa Babban Mai Bayar da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh, rasuwa. An yi jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh a ranar Talata bayan sallar La’asar, wanda Yarima Mai Jiran Gado, Muhammad bin Salman ya jagoranci manyan malamai da jami’an gwamnati da dubban mutane. Haka kuma, an yi masa Salatul Gaib a Masallacin Ka’aba da ke Makkah da kuma Masallacin Annabi Muhammad (SAW), da kuma sauran daukacin masallatan da ke kasar bisa umarnin masarautar UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
    A ranar Alhamis 25 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban taro a birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar yankin. An shirya fara bikin da shugaba Xi zai halarta da karfe 10:30 na safiyar Alhamis, kuma babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da dandalin shafin intanet na kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhuanet) za su watsa shi kai-tsaye. (Abdulrazaq Yahuza Jere)     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Sojojin HKI sun amabci cewa sojoji biyu sun halaka a wani kwanton bauna da mayaka a Gaza su ka yi, daga ciki har da kwamandan rundunar “Folcan”. Kakakin sojan HKI ya bayyana cewa wanda aka kashe din shi ne Manjo Shahir Natna’il, sai kuma Midgal Haimik a wani fada da aka yi a arewacin Gaza.  Wasu kafafen watsa labarun HKI sun ambata cewa mayakan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas sun yi wa sojoji kwanton bauna a wasu wurare biyu mabanbanta.  A bisa kididdigar sojojin HKI adadin wadanda aka kashe zuwa yanzu a yakin Gaza, sun kai 911. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website...
    Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita. Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a...
    Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin noma, da kauyuka da kuma manoma a fadin kasar. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a bana, mun shawo kan illar bala’o’i kamar fari, da ambaliyar ruwa, da samun daidaiton noman hatsin rani, da karuwar noman shinkafa mai nuna da wuri, ana kuma sa ran samun karin girbin hatsi. Xi Jinping, ya jaddada cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin ba za a iya...
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa a yayin da take guje wa harin ’yan bindiga a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja. Sarkin yankin Bassa, Bagudu Amos, ne ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da mata kan zaman lafiya da kare su daga cin zarafi, mai taken: “Ƙarfafa kariya daga cin zarafin jima’i da na jinsi a Jihar Neja.” Kungiyar Tunani Initiative, tare da goyon bayan Dorothy Njemanze Foundation da Ford Foundation, ce ta shirya taron domin ƙarfafa mata wajen yaki da cin zarafi da ke ƙara ta’azzara a sakamakon rashin tsaro. Bagudu Amos ya bayyana cewa mahaifiyar ta yi tafiya mai nisa a kafa da jaririn a bayanta domin tserewa daga harin ’yan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata cuta mai cin naman jikin dan’Adam ta yi sandin mutuwar mutum takwas yayin da wasu fiye da 60 suke kwance a asibiti a garin Malabu dake Karamar Hukumar Fufure ta Jihar Adamawa.   Wannan lamari dai ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankin. NAJERIYA A YAU: Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike a kan yadda wannan cuta take yaduwa da matakan da ya kamata a dauka don kauce wa kamuwa da ita. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ministan harkokin wajen Falasdinawa Varsen Aghabekian Shahin, ta godewa kasashen  duniya da suka amince da samuwar kasar Falasdinu ya zuwa yanzu kuma kuma wadanda suke shirin yinhaka, sannan tana kodaitar da sauran kasashen duniya da su yi hakan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shahin tana fadar haka a taron yan jarida da ta kira a yau Lahadi a birnin Ramallah, sannan ta kara da cewa ya zuwa yanzu kasashe da dama  sun bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu, Kuma sakone mai kyau ga Falasdinwa, kuma banda haka wannan sakonnin fata ne na samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Ta kara da cewa, amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta yana nufin HKI bata da iko a kanta....
    Firay ministan kasar Burtaniya da tokwarorinsa na kasashen Canada da Australia duk sun bayyana amincewar gwamnatocinsu da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Wanda ya nuna sauyi babba a al-amuran diblomasiyya wadanda suka sha fi HKI da kuma Falasdinawa. Kafin haka dai, idan an masu maganar samar da kasar Falasdinu sai suce sun barwa HKI ta tattunawa da Falasdinawa don warware matsalar tsakaninsu. Sauya matsayinda wadan nan manya-manyan kasashen duniya suka yi ya sake bude batun samar da kasashe biyu, wanda kuma zai kara tura HKI zuwa bongo don amincewa da samar kasar Falasdinu da kuma bukatar ta dai kissan kiyashin da takewa al-ummar Falasdinu a Gaz da kuma yankin yamma da kogin Jordan. Kafin haka Falasdinawa sun bukaci kasashen...
    Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Wang Yong ya bayyana cewa, kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwa da dukkan bangarori a muhimman fannoni kamar na masana’antu. Wang, wanda shi ne mataimakin shugaban babban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wacce take babbar hukumar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen bikin bude taron masana’antun duniya na shekarar 2025 da aka gudanar a lardin Anhui da ke gabashin kasar Sin. Wang ya kara da cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa, sun bi ka’idar samun moriyar juna...
    Kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa ta gayyata domin halartar taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah wanda za yi a ranar 27 ga watan nan na Satumba. Tunawa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah da sauran wadanda su ka yi shahada a lokacin, kamar su Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin, zai kasance a wani gagarumin taro a birnin Beirut da kuma sauran garuruwan Lebanon  a ranar 27 ga watan Satumba da misalin karfe: 4;30. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Hamas...
    A ranar Alhamis 18 ga watan nan, aka kaddamar da fara nuna fim din nan mai taken “Evil Unbound” a dukkanin sassan duniya, fim din da ya ba da labarin yadda a yayin yakin kin mamayar dakarun Japan, wata rundunar dakarun sojin kasar Japan ta aiwatar da wani shirin sirri, na gwaje-gwajen kimiyya ta makamai dake iya illata lafiyar bil’adama, a wani boyayyen wuri dake lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin. Duk da cewa akwai shaidu na hakika, da suka tabbatar da aukuwar muggan laifukan da rundunar ta 731 ta tafka, bukatar kasar Sin ta shigar da wannan lamari cikin kundin killace abubuwan tarihi na UNESCO ya gamu da tsaiko, har na tsawon sama da shekaru shida. Kazalika,...
    Al’ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da jama’a ke tserewa daga wani sabon harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane fiye da kima ya kife. Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Abubakar Rufa’i, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin Rediyon Najeriya a jihar. ASP Abubakar ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka shiga kwale-kwalen ba, yana mai jaddada cewa ana ci bincike da aikin ceto. Wani shaidan gani da ido, wanda bai...
      Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu.   “Na ji wani babban ƙara har sai da ya girgiza gine-ginen da ke kewayen DICON. Mutane na ta gudu daga wurin, amma muna tunanin fashewar bam ne, amma daga baya mun gano cewa daga masana’anta ne,” inji wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa.   Shaidun gani da ido sun ce fashewar na da nasaba da samar da hoda mai matukar muhimmanci wajen ƙera hodar harsashi ga sojojin Nijeriya. Daga...
    Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya  juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da bunkasa ta fuskokin ttatalin arzki, siyasa da al’adu da ci gaba. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya kira yi kasar Saudiyya da ta bude sabon shafin alakarta da kungiyoyin gwagwarmaya. Har ila yau Sheikh Na’im Kassim ya ce, HKI wani makami ne na kasashen turai da aikinsa shi ne yin kisan kare dangi akan duk wanda ya ki yin biyayya a gare su....
    An tsinci gawar Igbonna Uzoma, kwamandan hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a otel da ke birnin Kalaba, Jihar Kuros Riba, a ranar Juma’a. Rahotanni sun ce Uzoma, wanda aka dawo da shi aiki daga wata jiha zuwa Kuros Riba a kwanan nan, bai daɗe da kama aiki a sabon ofishin ba kafin wannan lamarin da ya jefa hukumar cikin ɗimuwa. Kakakin NDLEA na ƙasa, Femi Babafemi, ya tabbatar da mutuwar babban jami’in, inda ya bayyana cewa an tsinci gawarsa a ɗakin otel ɗinsa a ranar Alhamis da ta gabata. A cewarsa, “Kwamandan Ogbonna mutum ne mai tsananin jajircewa a aiki. An shirya fita aikin haɗin gwiwa tare da shi da misalin ƙarfe 10 na safiyar Alhamis,...
    An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa.   Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Ilorin.   Sanarwar ta ce shirin rufe kasuwannin Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi ba tare da sanin sarakunan gargajiya da shugabanni da masu gudanar da aiki ba, bai dace ba.   Ya bayyana cewa kafin daukar irin wadannan shawarwarin da shugaban karamar hukumar ya yi ya kamata a yi shawarwari da yawa don tafiyar da...
    Dubban ’yan Nijeriya ne ke zaune a ƙasar Saudiyya ba tare da takardun izinin zama ba, musamman a biranen Makkah da Madina. Rayuwarsu cike take da fargaba da rashin tabbas, a yayin da suke yin ayyukan hannu ko ƙananan sana’o’i ba tare da wata kariya ta doka ba. A yayin aiki Hajjin shekarar nan ta 2025, wakilimmu ya samu yin hira da wasu ’yan Nijeriya da ke zaune a can — waɗanda aka fi sani da Takari — inda suka bayyana masa yanayin rayuwarsu sa iliminsu da tsarin matsuguninsu da yanayin aikinsu da rayuwar ’ya’yansu da wasu ƙalubale na fargabar kame da rushe gidajenau, da ma ra’ayinsu kan komawa Nijeriya da sauransu. Ameera, wata ’yar Najeriya da ke zaune...
    Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu. Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna, da tabarmi, da gidajen sauro, da magungunan zazzabin cizon sauro. A cewar ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai, kimanin mutane 273,000 ne ambaliyar ta shafa a gundumomi 12 na jihohin Jonglei da Unity da Upper Nile da Central Equatoria, inda jihohin Jonglei da Unity suka dauki sama da kaso 91 na jimilar mutanen da ambaliyar ta shafa. Martha Remijo Rial, daraktan kula da...
    Wata matar aure ta shiga hannu kan zargin ƙone fuskar ’yar mijinta, Fatima Talba mai shekara 17 da tafasasshen man girki, a unguwar Jiddari Polo da ke Jihar Borno. Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata, bayan wata taƙaddama da kaure tsakanin Fatima da matar ubanta. Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe “Matar ce ta kwara wa Fatima man girki mai zafi a fuska, wanda ya janyo mata mummunan ƙuna,” in ji majiyar. An bayyana cewa Fatima na tare da mahaifinta a lokacin da suke shirye-shiryen aurenta da ake sa ran yi a nan...
    Majalissar gudanarwar kasar Sin ta fitar da takardar bayani, game da bunkasa ci gaban mata mai taken “Nasarorin Sin a fannin bunkasa ci gaban mata a dukkanin fannoni a sabon zamani”. Takardar bayanin da aka fitar a Juma’ar nan, na zuwa ne gabanin bude babban taron shugabanni na kasa da kasa na 2025, game da daidaiton jinsi, da karfafar rayuwar mata da zai gudana a nan birnin Beijing. Takardar ta kunshi cikakkun bayanai na gabatar da falsafar kasar Sin, da ka’idoji da ayyukan kirkire-kirkire masu nasaba da ingiza daidaiton jinsi, da bunkasa rayuwar mata a dukkanin fannoni a sabon zamani. Kazalika, ta fayyace muhimman nasarorin da matan kasar suka cimma, da tarin gudummawar da suka bayar, da jaddada himmar Sin...
    Albarkacin bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar Jam’iyyar Zhigong ta Sin, shugaban kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya aika wasikar taya murna, kuma a madadin kwamitin tsakiyar JKS, ya taya dukkan ’yan Jam’iyyar Zhigong murna tare da nuna musu gaisuwa. Xi Jinping ya jaddada cewa, a kan sabon tafarki, ana fatan Jam’iyyar Zhigong ta ci gaba da zaune bisa jagorancin JKS, ta kuma kara zurfafa fahimta da aiwatar da tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, ta hada kai da ’yan uwa Sinawa dake ketare, da wadanda suka dawo gida, da kuma daliban dake karatu a kasashen waje, don ba da gudunmawa ga babban aikin dunkulewar kasar, da kuma taka rawar...
    Idan aka yi ɗan nazari kan tafiyar siyasar Seyi Makinde a Jihar Oyo da kuma yammacin Nijeriya gaba ɗaya, za a fahimci sosai wane ne Makinde da kuma dalilin da ya sa ya dace kowanne ɗan siyasa mai hangen nesa ya yi hattara da shi kafin 2027. Ko da yake Gwamnan Jihar Oyo, wanda ake kira da “Star Boy”, ya kafa kansa a matsayin jagoran PDP a yankin yamma, tafiyarsa zuwa kujerar gwamna ba ta zo masa da sauƙi ba. Kafin shekarar 2019, Makinde ya tsaya takarar kujerar Sanatan Oyo ta Kudu a shekarar 2007, amma ya sha kaye a hannun Kamoru Adedibu. Duk da wannan rashin nasara ta farko, bai karaya ba. A 2010, ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya sake...
    Aƙalla mutane 58 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon barkewar cutar Kwalara a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 da ke jihar Bauchi. Haka kuma, an samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar a faɗin jihar. Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar rataya Mataimakin Gwamnan jihar, Auwal Mohammed Jatau, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wasu kwamitoci biyu kan yaki da cutar a jihar. Mataimakin Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda barkewar cutar ke ci gaba da kashe mutane, lalata rayuwar jama’a, da kuma jefa tsarin kiwon lafiya na jihar cikin matsala. Jatau ya bayyana cewa: “Ana iya kaucewa wannan barkewar cutar idan...
    Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita. An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta zuwa ƙetare. ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa Munduwar mai ɗauke da ado na musamman, na da matuƙar daraja tun zamanin Fir’aunan, yayin da ake danganta ta da tsofaffin gumakan da aka yi bautar su a can baya, sannan an ce tana da ƙarfin warkarwa. Munduwar na cikin jerin kayayyakin...
    A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma’aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami’an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala taro na musamman da shugabannin sassa na hukumar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar. Yayi bayanin cewar, hukumar zata bada bitar ne ga jami’an da kuma shugabannin shiyya-shiyya kan hanyoyin kara kula da walwala da jin dadin maniyyata da kuma dabarun magance kalubale yayin gabatar da aikin hajji. Yana mai cewar bada horo na da matukar mahimmaci duba da yadda...
    Rundunar ‘yan Sandan Jihar Jigawa ta bada sanarwar nasarar cafke wani sojan bogi da ƙarin wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota a ƙauyen Sabon Sara. Kamar yadda Kakakin rundunar ’yan sanda na Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ya sanarwa manema labarai a garin Dutse cewa, an kama matashin sojan bogin da abokansa da ake zargin su da satar mota a ƙauyen Sabon Sara, cikin ƙaramar hukumar Kafin Hausa. Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya A cewar majiyar an kama sojan bogin mai suna Kabiru Musa da abokan aikinsa Umar Ali da Sabi’u Bashir, dukkansu ‘yan asalin Jihar Kano. A cewar kakakin rundunar waɗannan...
    Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira da a kara fahimtar juna a tsakanin kasashe tare da yin addu’ar samun zaman lafiya a duniya a yayin da ake fama da rikice-rikice a duniya.   Ta yi wannan kiran ne a lokacin da ta karbi bakuncin jakadan Qatar a Najeriya Ali bin Ghanem Al-Hajri a ofishinta da ke Abuja. Uwargidan shugaban kasar, yayin da take mayar da jawabi game da harin da aka kai a birnin Doha na baya-bayan nan, ta jaddada cewa, zaman lafiya, kamar yadda manyan addinai ke wa’azi, muhimmin abu ne ga bil’adama, kuma ya kamata ya kasance muhimmin fifiko ga dukkan kasashe.   Tattaunawar da aka yi a yayin ziyarar, wadda ta kasance a...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, ya yi jawabi ga wadanda suka tsira daga kisan Pager a bikin cika shekara guda da aiwatar da wannan harin ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi a ranar 17 ga Satumba, 2024. “Ku ne masu gani na gaskiya, tushen begenmu, kuma sadaukarwar ku ga Allah ita ce ke ba wa rayuwa ma’anarta ta har abada, ku ne hasken da ke shiryar da mu domin bin hanya, kuma juriyarku ita ce zuciyar juriyarmu,” in ji Sheikh Qassem a cikin sakonsa ga mutanen da suka jikkata a harin. “Me zan iya ce muku? Don yanzu ku ne malamai, masu ba da shawara, ku ne jagorori, saboda kun yi sadaukarwa kuma kuna a kan yi,...
    Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma.   A nasa bangaren, mahaifin budurwar, Malam Aliyu dake Garin Dakasoye, ya tabbatar da cewa za su gudanar da bikin domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya ba su.   Ya kara da cewa: “Mun gode wa Allah bisa wannan arziki, kuma muna sa ran gudanar da bikin tare da sanya musu suna domin nuna godiya ga Allah mai daukaka.” Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Jami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta. Ya ce, “Binciken farko ya...
    A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.   Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Al’ummar garin Dukku a Ƙaramar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe sun koka kan mummunan halin hanyar da ta haɗa su da babban birnin jihar, tare da kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran ta. A cewar direbobi, tafiyar Dukku zuwa Gombe wadda a da take ɗaukar mintuna 50 kacal, yanzu ta koma fiye da awa biyu saboda lalacewar hanyar, abin da ke jawo gajiya da takaici ga fasinjoji da masu tuƙi. An fara gina hanyar Gombe-Dukku-Darazo ne tun a shekarun 1980, aka gyara ta a farkon shekarun 2000. Sai dai daga baya aka yi sakaci da ita duk da kasancewarta hanyar da matafiya daga jihohin Adamawa, Taraba, Jigawa, Kano, Bauchi da wasu ke bi. “Gyaran motoci na cinye mana kuɗi”...
    An garzaya da ita asibiti, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarta. ’Yansanda sun kama Bosede kuma suna bincike a kan lamarin. Kakakin rundunar, DSP Olusola Ayanlade, ya ce za su tabbatar da adalci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur. Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki. Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya. “Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama....
      Har ila yau, Lin ya ce matsayin kasar Sin dangane da rikicin kasar Ukraine bai sauya ba, cewa tattaunawa, da gudanar da shawarwari ne kadai hanyoyi mafiya dacewa na warware rikicin. Har kullum Sin na kan turbar adalci game da rikicin, tana kuma ci gaba da ingiza bukatar komawa teburin shawara tun barkewar rikicin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi. Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka. NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar. A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a...
    Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.   Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka.   “Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin ne dai kungiyoyin kasashen musulmi da na larabawa su ka yi taron gaggawa a birin Doha na kasar Qatar da aka tattauna harin wuce gona da iri da HKI ta kai wa kasar. Bayanin bayan taron ya kunshi bangarori mabanbanta da su ka hada da daukar matakai kwarara domin taka wa HKI birki akan ta’addancin da take yi, da kuma hanyoyin kare kai anan gaba.  Kungiyar kasashen larabawan yankin tekun fasha ta sake jaddada muhimmancin aiki da dokar kafa rundunar hadin gwiwa ta kare kai daga duk wani wuce gona da iri daga waje. Bugu da kari, mahalarta taron sun amince da dukar dukkanin matakan dokoki a fagen duniya domin hukunta jami’an HKI da su ka tafka...
    Ya ƙara da cewa ‘yan’uwa da abokan arziƙi da suka shirya wannan biki na karrama Farfesa Armaya’u Bichi tare da bashi lambar yabo tare da wasu muhimman mutane waɗanda suka taimaimake shi wajen gudanar da shugabanci sun kyauta sannan sun ajiye ƙwarya a gurbinta.   Shima da yake gabatar da jawabinsa, shugaban riƙo na jami’ar gwamnatin Tarayya dake Katsina (FUDMA), Farfesa Aminu Ado ya ce Bichi mutum ne mai jin tausayin al’umma musamman mutanen dake ƙarƙashinsa.   Farfesa Ado ya ce har ƙasa ta naɗe ba zai mance da irin gagarumin ci gaban da Farfesa Arma’yau ya kawo ma jami’ar FUDMA ba.   Haka kuma a yayin bikin an ƙaddamar da littafin waƙoƙin da wasu mawaƙa suka yi wa tsohon...
    Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya ƙaryata zargin da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya yi masa, dangane da mutuwar wasu marasa lafiya sakamakon katse wutar lantarki da aka ce kamfanin ya yi. Asibitin na AKTH ya bayyana damuwarsa a ranar Lahadi kan abin da ya kira abin takaici yana mai cewa mutanen da suka mutu za su iya tsira da ransu da ba a ɗauke wutar ba. Amma a martanin da ya bayar, Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na KEDCO, Sani Bala Sani, ya ce asibitin na ƙoƙarin ɓata sunan kamfanin ne kawai, domin an dawo da wutar tun kafin asibitin ya fitar da wannan sanarwar. Sani ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne...
    Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwarorinsa na Qatar, Turkiyya, Pakistan da Lebanon a Doha fadar mulkin kasar Qatar Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na Qatar a gefen taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Doha. Doha ta sanar da cewa, fira ministan kasar Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar ya yi nazari kan al’amuran yankin na baya-bayan nan yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi. A yayin wannan taro, harin da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a birnin Doha shi ne babban abin da ake tattaunawa akai. Araqchi yayi Allah wadai da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai, yana mai tabbatar da goyon bayan Jamhuriyar...
    Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura. Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda za a iya kauce wa ne idan akwai tsayayyiyar wutar lantarki. Ta bayyana cewa Asibitin yana AKTH yakan biya kuɗin wuta akai-akai daga kuɗaɗen shigansa, kuma yana kashe kuɗaɗe wajen sanya mai a janareto domin amfani idan aka ɗauke wuta daga KEDCO. Don haka, “Hukumar gudanarwar Asibitin AKTH na roƙon Kamfanin KEDCO da ya taimaka wa ayyukan asibitin ta hanyar dawo da wutar a yayin...
    Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa jihohi 11 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa ambaliya daga ranar Lahadi zuwa Alhamis. A cikin sanarwar da Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli, ta fitar, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Benuwe, Nasarawa, Taraba da Delta. An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan a Akwa Ibom Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango Sauran sun haɗa da Neja, Kebbi, Kano, Katsina, Sakkwato da Zamfara. Sanarwar ta bayyana cewa cikar kogunan Gongola, Benuwe da Neja na ƙara barazana ga al’ummar da ke zaune a gefen kogunan. Gwamnati ta shawarci al’ummar da ke yankunan da abin ya shafa, musamman waɗanda ke kusa...
    Wani mutum mai shekara 67 aka kai asibiti da raunuka masu barazana ga rayuwa, abin takaici kuma ya rasu a asibiti a ranar Juma’a, 5 ga Satumba. An bayyana sunansa da James Gbadamosi.” Bayan faruwar lamarin, ƴan sanda sun bayyana cewa sun kama Wright-Walter mai shekaru 37, suka gurfanar da shi bisa laifin kai hari a watan Agusta, amma aka ba da belinsa. Sai dai an sake kama shi a ranar Asabar bayan rasuwar Gbadamosi, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare a ranar Litinin. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Andre Wright-Walters, mai shekaru 37 (05.02.1988) na Aɓery Hill, Greenwich, an gurfanar da shi a ranar Lahadi, 7 ga Satumba. Ya bayyana a gaban kotun majistare ta...
    Haka kuma, kamfanonin gwamnatin tarayya da suka durƙushe a jihar sun haɗa da: Nigeria Paper Mill, Jebba; Nigeria Sugar Company, Bacita; da Nigeria Yeast and Alcohol Manufacturing Company, Bacita. Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi Jaridar LEADERSHIP Sunday ta gano cewa wasu kamfanonin gwamnati na jihohi sun riga sun durƙushe tun kafin zuwan tsarin mulkin dimokuraɗiyya na yanzu a Nijeriya a shekarar 1999. Haka kuma, an gano cewa wasu kamfanonin masu zaman kansu sun durƙushe ne sakamakon manufofin gwamnati marasa kyau, mawuyacin yanayin tattalin arziƙi, wutar lantarki mai yawan ɗauke wuta, shigowar kayayyaki marasa inganci, hauhawar farashin kayayyaki, tashin farashin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Juma’a, Araqchi ya ce, “Akwai yiwuwar sake yin wani taro da jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, kuma hakan ya dogara ne da shawarar Turai. Dangane da tattaunawar da aka yi a birnin Alkahira, ya ce, wadannan shawarwarin masu muhimmanci ne sosai, da kuma shawarwarin da ake yi a bayan yaki, inda hotunan shahidai ke wucewa a kan idonun mutane daya bayan daya, ba tattaunawa...
    “Haka zalika, shi ma matuƙin babur ɗin; ruwan ya yi awon gaba da shi,” a cewar tasa. Ganau ɗin ya ci gaba da cewa, wani ƙwararre a fannin iya ruwa; nan da nan ya garzayo tare da yin sufa a cikin ruwa, domin ƙoƙarin ceto su, amma tuni ruwan ya riga ya yi awon gaba da su. Limamin da ya jagoranci sallar jana’izar gawar da aka samu a kwarin Dangoma, Mallam Musa Umar Al mishawi ya bayyana cewa; marigayin ya samu rauni a goshinsa. “Marigayin, mazaunin Unguwar Gidan Dangoma ne da ke tudun jukun ta garin Zaria, sannan kuma an yi jana’izarsa kamar yadda a safiyar yau kamar yadda addinin musulunci ya tanada,” in ji shi.   Kazalika, har zuwa lokacin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kamata a kafa hukumar musamman da za ta kula da gano mutane da suka ɓace tare da bata ƙarfi don gudanar da bincike. Kaso 68 cikin 100 na masu neman ƴaƴan da suka ɓace iyaye mata ne, amma da dama suna dawowa hannu rabbana saboda rashin tsari daga mahukunta. A jihar Yobe kaɗai, yara 2,500 ne aka ce sun ɓace, mafi yawan su a Gujba, abin da ya nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka a Arewa maso Gabas. Yakuma zama wajibi a samar da tsare-tsaren gwamnati da za su kare haƙƙin ƴanuwa waɗanda suka rasa nasu, musamman a jihohin da ake fama da tashe-tashen hankula. Waɗannan tsare-tsaren za su yi aiki kaf shoulder da al’ummomin yankuna, sarakunan gargajiya, malaman...
    Mataimakiyar shugaban kasar Venezuela Delcy Rodriguez ta  yi gargadi game da shirin Washington na kara ruruta wutar rikicin soji a yankin Latin Amurka, tana mai zargin Amurka da neman sauyi gwamnati a Venezuela da kuma sarrafa albarkatun kasar. Rodriguez ta bayyana cewa “kasancewar sojojin Amurka a yankin Caribbean na nufin aiwatar da sauyin gwamnati a Venezuela da kuma mamaye  dukiyarta.” Ta kara da cewa, biyo bayan gazawar takunkumi da tsare-tsare na tattalin arziki, Washington ta “yanke shawarar haddasa  yaki a wannan bangare na  duniya,” tana mai jaddada cewa duk wani harin soji a kan Venezuela “zai haifar da rashin kwanciyar hankali a yankin Latin Amurka.” Mataimakiyar shugaban kasar ta Venezuela ta yi watsi da zargin da Amurka ta yi a...
    Har ila yau, karkashin wadannan shawarwari, kasashe membobin BRICS za su ci babbar gajiya daga fifikonsu, da ma alfanun dake tattare da hadakarsu wuri guda.   Zage damtse da kasashe membobin BRICS ke yi wajen karfafa cudanya, da hadin gwiwa na zuwa ne a wani muhimmin lokaci da duniya ke fuskantar karin rashin tabbas, ake kuma kara fuskantar koma baya ta fuskar jituwa tsakanin wasu sassan kasashen duniya. Don haka, dandalin BRICS karin dama ce ga duniya ta rungumar juna, don kare cudanyar mabanbantan sassa, da tsarin cinikayya mai game dukkanin bangarori, har a kai ga cimma nasarar kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya ga kowa da kowa.   Tarihi ya sha nuna yadda cudanyar sassa daban daban ke...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta yadda ma’amala tsakanin bangarorin biyu zata kasance. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia. A lokacinda yake jawabin hadin guiwa ta tokwaransa na kasar ta Tunisia. Kafin haka dai Aragchi ya yada zango a birnin Alkahira na kasar Masar inda ya gana da Rafael Grossi shugaban hukumar IAEA, suka kuma rattaba hannu kan sabuwar yarjeniya da hukumar, ta yadda hulda tsakaninsu zata kasance bayan hare-haren da HKI da Amurka suka kai wa cibiyoyin sarrafa makamashin nukliya na kasar ta...
    A cewarsa, kudaden fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan wadanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa.   Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka.   Masanin tsaron ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta fi ƙarfin dabarun soja kaɗai, inda ya danganta ta da cin hanci da rashawa wanda ya kira “babban mai ba da damar ayyukan ta’addanci.”   Ya yi gargadin cewa ya zama dole a guji yin zarge-zargen da ba su da tushe kan shugabannin da ke kan karagar mulki, yana mai tunatar da cewa irin wadannan maganganu...
    Wata budurwa mai shekaru 24 mai suna Kelechi Ebubechukwu, ta rasu a cikin wani yanayi da mai daure kai a gidan saurayinta da ke Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya Abuja. Wani ƙwararren masani kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba. A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Talata. Mota ɗauke da tabar wiwi ta yi hatsari a Kano, ta faɗa hannun jami’an NDLEA Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki  Majiyoyin ’yan sanda sun ce binciken farko ya nuna cewa marigayiyar na fama da zazzabin cizon sauro kafin rasuwarta. A cewar mjiyoyin, an samu takardar da ke dauke da rubutun magungunan da...
    A yayin taron rattaba hannun, Farfesa Gwarzo ya bayyana manufar wannan yarjejeniya, inda ya ce hadin gwiwar za ta bai wa dalibai da ma’aikata damar cin moriyar albarkatu da kwarewa daga kasashen waje.   “Wannan hadin gwiwar alama ce ta jajircewarmu wajen hada jami’o’inmu da manyan cibiyoyi na duniya domin bunkasa kirkire-kirkire da bincike a rukunin jami’o’inmu na MAAUN,” in ji shi.   A karkashin wannan yarjejeniyar, cibiyoyin biyu za su rika raba kwarewar su tare da tallafa wa juna don cimma manufofi na bai daya. Muhimman bangarorin hadin gwiwar sun hada da samar da koyarwar harshen Turanci ta yanar gizo ga daliban MAAUN, samar da hanyoyi don ci gaba da karatu a Seneca, da bayar da shawarwari kan harkokin...
    Dukkanin kamfanonin sun roƙi abokan hulɗarsu da su yi haƙuri, inda suka ce injiniyoyi na aiki don gyara wutar. Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ƙoƙarin gyara wutar lantarkin yanzu haka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar Kaduna (KSSQAA), ta gargadi masu makarantu masu zaman kansu kan kara kudin makaranta ba tare da samun amincewar gwamnatin jihar a hukumance ba. A wata takarda mai kwanan ranar 7 ga Satumba, 2023, wacce Mercy Bainta Kude, Daraktar Sashen Makarantu masu zaman kansu ta sanya wa hannu a madadin Darakta-Janar, Hukumar ta jaddada cewa “babu wani ko wata mai makaranta da zai ko za ta kara kudin makaranta ko inganta makarantar ​​ba tare da amincewar KSSQAA ba.” Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Yaya Da Ƙannuwa Da Wasu A Zaria Majalisa Ta Bai Wa Minista Sa’o’i 48 Ya Bayyana A Gabanta Kan Hatsarin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna Umurnin ya zo ne a daidai...
    Cikin shekarar 2024, an kafa sabbin kamfanonin 59,000 masu jarin waje a kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 9.9 bisa dari kan na 2023. Wani rahoto da ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta fitar a wajen bikin baje kolin cinikayya da zuba jari karo na 25 dake gudana a birnin Xiamen ya ce, ainihin jarin waje da aka yi amfani da shi a kasar a bara ya kai dala biliyan 116.24, lamarin da ya sa kasar ta ci gaba da rike matsayinta na mafi samun jarin waje a tsakanin kasashe masu tasowa. Haka kuma, ana ci gaba da samun ingantuwar bangarorin da ake zubawa jarin waje a kasar, inda masana’antar fasahohin zamani ta dauki kaso 34.6 na...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba. Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da ita shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, tana mai kafa hujja da cikar wa’adin watanni shida da aka dakatar da ita. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya Ana zargin jami’in sibil difens da harbe abokin aikinsa a Abuja Sanatar ta bayyana cewa kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yulin da ya gabata...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu mazauna unguwar Oworonshoki da ke ƙaramar hukumar Kosofe a Jihar Legas, sun datse wani sashe na gadar Third Mainland a ranar Litinin, a wata zanga-zanga da suka gudanar don nuna adawa da rushe musu gidaje. Datse hanyar da suka yi ya haddasa cunkoson masu ababen hawa da fasinjoji, lamarin da ya tilasta wa ’yan sanda tarar hanzarin lamarin, inda suka riƙa harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zangar-zangar. MDD ta buƙaci hukumomin Najeriya su kamo waɗanda suka kai hari a Bama Yarima Harry ya ziyarci kabarin Sarauniya Elizabeth II Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Yulin 2023 aka soma rusau ɗin, lamarin da ya raba wasu mazauna unguwanni kamar Oke-Eri, Odunfa Lane, Ogo-Oluwa, Precious Seed, Coker da kuma...
    Najeriya na iya shiga cikin matsalar ƙarancin man fetur daga yau Litinin, muddin Gwamnatin Tarayya ba ta warware rikicin da ya kunno kai tsakanin Ƙungiyar Direbobin Tankar Mai (PTD) ta ƙarƙashin NUPENG da kamfanin Matatar Mai ta Dangote ba. Direbobin sun sanar da shiga yajin aiki saboda shirin kamfanin Ɗangote na fitar da motoci 4,000 da ke amfani da gas ɗin CNG domin kai mai kai tsaye ga kasuwa ba tare da direbobin da ke ƙarƙashin NUPENG ba. Ƙungiyar ta yi zargin cewa wannan tsari zai rusa ayyukan dubban direbobi, ya hana ’yancin kafa ƙungiya kuma ya haifar da “mulkin danniya” a harkar rarraba man fetur. Gwamnati ta shiga tsakani Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Muhammad Maigari Ɗingyadi, ya tabbatar a...
    Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba. Kukan Iyaye A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida. Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros...
    Bictor Boniface Wani dan wasan da ya tafi zaman aro shi ne Bictor Boniface wanda ya bar Bayer Leberkusen ya koma Werder Bremen a matsayin aro na tsawon kaka guda a ranar da za a rufe cinikin yan wasa, dan wasan na Nijeriya ya saka hannu akan kwantiragin da zai sa ya zauna a Werder har zuwa watan Yuni na shekarar 2026, kungiyoyin biyu ne za su biya albashin Boniface.   Tolu Arokodare Wolbes ta sanar da daukar Arokodare daga kungiyar KRC Genk ta kasar Belgium dake buga gasar Belgian Pro League a ranar karshe ta musayar yan wasa, dan wasan mai shekaru 24 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu da kungiyar ta Firimiya tare da zabin karin shekara,...
    Kwamandan Sojojin Iran ya jaddada cewa: Dole ne a ko da yaushe Iran ta kasance a shirye don yin yaki Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada wajibcin kasancewa cikin shiri a ko da yaushe domin yaki, yana mai cewa: A yau sun fahimci yaki da gaba da kuma makircin makiya daidai da yadda suke a baya. Babban kwamandan sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Manjo Janar Amir Hatami, ya ziyarci rundunonin sojoji a yankunan Isfahan, Tabriz, da Hamadan. A yayin da yake yin nazari kan shirye-shiryen wadannan runduna tare da rakiyar kwamandoji, mayaka, da matukan jirgin sama, ya lura da tsayin daka da al’ummar Iran suka yi wajen tunkarar wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar na tsawon...
    A jiya Jumma’a 5 ga wannan wata, babban taron MDD karo na 79 ya jefa kuri’a tare da zartas da kudurin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da kasar Sin da dukkan kasashe membobin kungiyar SCO kimanin 40 suka gabatar tare. Kudurin ya amince da muhimmiyar rawar da kungiyar SCO ta taka wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasa da yin imani da juna da kuma hadin gwiwa a yankin, kana ya yaba wa kungiyar SCO bisa kokarin nuna goyon baya ga ayyukan MDD, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da tsarin MDD. Mukaddashin shugaban tawagar dindindin ta Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana yayin da yake bayani game...
    Ministan harkokin wajen Iran, Seyyed Abbas Araghchi, ya tattauna ta wayar tarho da takwaroribnsa na kasashen Girka, Slovenia da Saliyo a wannan Juma’a kan batutuwan da suka shafi kasashen. Mista Abbas ya gana ne Georgios Gerapetritis, ministan harkokin wajen Girka, Tanja Fajon, ministan harkokin wajen Slovenia, da Alhaji Musa Timothy Kabba, ministan harkokin wajen Saliyo. Dukkan kasashen uku a halin yanzu mambobi ne a kwamitin sulhu na MDD. Tattaunawar ta ta’allaka ne kan dangantakar da ke tsakanin Iran da kasashen, da kuma ci gaban yanki da na kasa da kasa, musamman dangane da matakin da kasashen Turai uku (Birtaniya, Faransa, da Jamus) suka yi a kwamitin sulhu. Ministan harkokin wajen na Iran ya yi kakkausar suka kan matakin da kasashen...
    Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa da dama sun bayyana bacin ransu kan barazanar da ministan yakin Isra’ila ya yi na bude “kofofin jahannama” a zirin Gaza. Wannan martanin ya zo ne a ranar Juma’a bayan da Isra’ila Katz ya ayyana cewa gwamnatin sahyoniyawan na gab da maida yankin jahannama a gabar tekun. Katz, ya bayyana cewa sojojin Isra’ila za su zafafa kai hare-hare har sai kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta sako mutanen da aka kama. A nata bangaren, Hamas ta ayyana barazanar Katz a matsayin “kalubale da ba a taba ganin irinsa ba ga dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai.” Kalaman na Katz na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta riga ta ba da damammaki don ba...
    Don haka, ana so a dan dakatar da yi masa ban-ruwa har zuwa wasu ‘yan makwanni, wato kafin a yi masa girbi. Sinadaran da ya kamata a yi amfani da su: Sai dai, mangwaro na jurewa yin girma a cikin kowane irin yanayi, sannan kuma bai cika samun wasu kalubale wajen samun harbin kwayoyin cututtuka ba. Sinadaran da ake yi wa mangwaro feshi da su, ya danganta ne da irin cututtukan da suka harbe shi. Wasu daga cikin sinadaran feshin sun hada da kamar irin su ‘Potassium’. Zuba takin zamani: Takin zamanin da ake zuba wa mangwaro, ya danganta da irin matakin da ya kai na yin girma. Wadannan su ne tsarin da aka bayar da shawa kan sinadaran da...
    Ya kara da cewa, saboda haka; akwai bukatar a kara yawan hektar noman kwakwar manjar zuwa hekta akalla 500,000, domin cike gibin bukatar da ake da ita a kasar nan tare kuma da kara bunkasa nomanta a Nijeriya baki-daya. Shugaban ya ci gaba da cewa, har yanzu a Nijeriya ana ci gaba da fuskantar samun gibi wajen samar da kwakwar, sai dai ya bayyana cewa; sama da shekara 10 zuwa shekara 15 kungiyar ta POFON ta yi namijin kokari, wajen kara yawan noman kwakwar a daukacin fadin kasar. A cewarsa, manyan gonaki a kasar da ke nomanta kamar irin su, Presco da kuma Okomu sun kara dage damtse wajen zuba hannun jari da kuma kara fadada gonakin noman kwakwar manjan...
    Ya yaba da jajircewar Gidauniyar Abdullahi Maikudi, yana mai kira ga sauran masu kudi da kungiyoyi su yi koyi da wannan aiki na alheri. Ya kara da cewa a matsayinsa na dan arewa, ba zai daina fafutukar ganin matasa sun samu damar da za ta inganta rayuwarsu ba. A yayin taron, daliban da aka dauki nauyin karatunsu sun bayyana farin ciki da godiya ga gidauniyar, inda suka yi alkawarin jajircewa a wurin karatunsu don su dawo su yi wa al’umma hidima. Taron ya kasance cike da nishadi, addu’o’i da kuma kira ga hadin kai wajen gina al’umma ta hanyar ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Kwamitocin kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya sun bayyana barazanar Katz da cewa; Kira ne ga aiwatar da kisan kare dangi da kuma shafe wata al’umma Kwamitin kungiyoyin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa ya tabbatar da cewa: Kalaman ministan tsaron Isra’ila Katz game da “bude kofofin jahannama” kan birnin Gaza ya zama kira ga jama’a na Aiwatar da kisan kiyashi, kawar da wata al’umma daga kan doron kasa da kuma kai hare-haren wuce gona da iri kan ababen more rayuwa da farare hula. Kwamitocin sun bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa: Laifukan da sojojin mamaya Isra’ila suka aikata a birnin Gaza, da suka hada da barna, ta’addanci, da kuma kashe jama’a, sun bayyana hakikanin fuskar “hukumar da ke karkashin jagorancin...
      “Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW).   “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW).   “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da mu zuwa ga kyawawan ɗabi’u, halaye da ayyuka.   “Ya kamata mu yi amfani da irin waɗannan muhimman lokuta na addini domin mu dage da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ƙasa baki ɗaya.   “Allah (T) ya kawo mana ƙarshen ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifuka a cikin al’ummarmu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    “Muna miƙa ta’aziyyar mu ta musamman ga iyalan waɗanda abin ya shafa, gwamnatin jihar da kuma al’ummar Neja. Jimamin mu da addu’o’in mu suna tare da duk wanda wannan ibtila’i ya shafa.”   Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta samar da dukkan tallafi da ake buƙata ga iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka tsira, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Neja domin tabbatar da gaggawar tallafi da taimako.   Haka kuma, gwamnatin ta umurci Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da ta gudanar da babban kamfen na wayar da kai a faɗin ƙasar nan domin ƙara faɗakar da jama’a kan matakan tsaro...
    Watanni biyu da rabi da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran tare da fadin Donal Trump kan cewa sojojinsa sun lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, amma har yanzun ba’a san halinda cibiyoyin nukliyar kasar suke ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar IAEA tana iya kokarinta don sanin halin da cibiyoyin nukliyar kasar Iran suke don bawa Amurka da HKI damar sanin yadda zasu kaiwa Iran hare-hare a yakin da za’a fafata da su nan gaba. Gwamnatin JMI tana zargin hukumar IAEA da kasancewa yar leken asiri Amurka da HKI a cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, don basu damar `lalatasu a yaki na gaba. Bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan...
    Watanni biyu da rabi da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran tare da fadin Donal Trump kan cewa sojojinsa sun lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, amma har yanzun ba’a san halinda cibiyoyin nukliyar kasar suke ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar IAEA tana iya kokarinta don sanin halin da cibiyoyin nukliyar kasar Iran suke don bawa Amurka da HKI damar sanin yadda zasu kaiwa Iran hare-hare a yakin da za’a fafata da su nan gaba. Gwamnatin JMI tana zargin hukumar IAEA da kasancewa yar leken asiri Amurka da HKI a cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, don basu damar `lalatasu a yaki na gaba. Bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan...
    A yanzu haka yankuna da dama wadanda a baya ba su fuskanci kalubalen matsalar tsaro ba, a yanzu haka sun fara dandana ukubar ta’addanci da bakuntar sansanin ‘yan gudun hijira. Kalubalen tabarbarewar tsaro da kiran da shugaban rundunar tsaro ta Kasa, Janar Christopher Musa ya yi kan ‘yan Nijeriya su dauki matakan kare kai ya haifar da cece- kuce musamman ga galibin jama’a da ke ganin gwamnati ta kasa. Da yawan jama’a na ganin duk da makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro da kwarewar jami’an sojoji amma ‘yan ta’adda sun rinjaye su har suna ikirarin jama’a su dauki matakan kare kai. Janar Musa wanda daga baya ya janye kalamansa, tun da farko ya bukaci ‘yan Nijeriya da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da ake gudanar da bukukuwan Mauludi a sassa daban-daban a garuruwan Najeriya, wasu yankunan na gudanar da nasu bukukuwar na daban. Ko yaya ake gudanar da bikin Sallar Gani? NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda ake gudanar da bikin sallar a wasu garuruwan kasar Hausa. Domin sauke shirin, latsa nan
    Mahukuntan lafiya sun tabbatar da sabuwar ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuryar Dimokraɗiyyar Congo wadda zuwa ƙarshen watan Agustan da ya gabata ta yi ajalin mutum 15 a lardin Kasai da ke tsakiyar ƙasar. Ministan Lafiya, Samuel Roger Kamba, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Kinshasa, babban birnin ƙasar. Saudiyya ta ƙaƙaba wa masu laifukan rashin ɗa’a sabuwar tara Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13 a Borno Rahotanni sun nuna cewa an samu mutum 28 da ake zargin sun kamu da cutar a lardin Kasai, inda a karon farko a ranar 20 ga watan Agusta aka gano ta a jikin wata mata mai juna biyu mai shekara 34 bayan kwantar da ita a asibiti. “Wannan...
    Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sanya tarar kuɗi kan masu aikata ayyukan da suka shafi rashin ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan salla, domin kare mutunci, tsaro da kuma zaman lafiya. Sabbin matakan, wanda za a fara aiwatarwa nan take, sun shafi masu sanya kaya marasa mutunci a bainar jama’a, da masu kunna kiɗa lokacin salla, da masu bahaya ko zubar da shara a wuraren da doka ta haramta. Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13 a Borno Hisbah ta kama mai safarar mutane da mata 12 A cewar sabuwar doka, duk wanda aka kama da kunna kiɗa a lokacin salla zai biya tara ta Riyal 1,000 (kimanin Naira 390,000) a karon farko, kuma idan aka sake kama shi, tarar...
    Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da ɓullar cutar cholera a garin Tureta, ƙaramar hukumar Tureta, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin. Kwamishinan lafiya na jihar ya ce an tura samfurin majinyatan zuwa ɗakin gwaje-gwaje na ƙasa da ke Jihar Oyo domin tabbatar da cutar. Ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da magunguna ƙyauta tare da taimakon likitoci, inda ya bayyana cewa da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa suna amsawa da magani. Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Kashe Wani Mutum Da Jikkata Wasu Da Dama A Sokoto Sai dai, mazauna yankin sun yi iƙirarin cewa aƙalla mutane goma ne ke mutuwa...
    Sama da mutane dubu ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a yankin Darfur na kasar Sudan Sama da mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta hallaka daukacin wani kauye a yankin Darfur na yammacin Sudan, a wani lamari da aka bayyana a matsayin daya daga cikin bala’o’i mafi muni da aka taba fuskanta a tarihin Sudan a wannan zamani, a cewar kungiyar fafatukar ‘yantar da al’ummar Sudan (SLM) da ke iko da yankin. Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, zabtarewar kasa gaba daya ta lalata kauyen Tarsin da ke gabashin Jebel Marra, kusa da yankin Soni, tare da kashe daukacin al’ummarta, wadanda aka kiyasta sama da maza da mata da yara sama da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin. Wannan ajanda, ta nuna hanyar da za a bi, tare da ba da jagoranci ga aiwatar da ayyukan gina tsarin mulkin duniya mai adalci da dacewa, a karkashin yanayin duniya mai fuskantar manyan sauye-sauye, da kuma jagorancin cike gibin kudi na samar da ci gaba da bunkasa. Sabuwar ajandar mulkin duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta yi magana kai tsaye kan wasu muhimman abubuwa guda uku a tsarin jagorancin duniya, wato rashin daidaiton iko, da rarrabuwar ra’ayoyi, da kuma rashin daukar matakai. Ajandar, wadda ta fitar da wasu ka’idoji guda biyar, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kasa, da...
    Gwamnatin kasar Belgium ta bada sanarwan cewa zata bayyana amincewarta da samuwar kasar Palasdinu mai cikekken yenci, a babban taron MDD a cikin wannan watan a birnin NewsYork. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Belgium Maxime Prevot yana fadar haka a shafinsa na X a yau Talata. Ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu dai sun rika sun dauki matakan kakabawa HKI wasu takunkuman tattalin arziki saboda kissan kare dangin da takewa al-ummar Falasdinu a gaza.. A cikin watan Yulin da ya gabata shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa kasarta zata amince da kasar Falasdinu mai zaman kanta, kafada da kafada da HKI. Bayan haka ne wasu kasashen turai da...
    Mukaddashin daraktan ofishin bunkasa tattalin arziki, hada kai da raya cinikayya a hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, mista Patrick Ndzana Olomo, ya ce nahiyar Afirka da Sin na da makoma mai haske a fannin raya hadin gwiwa, don bunkasa harkokin noma da shawo kan matsalar kamfar abinci a Afirka. Olomo, wanda ya yi tsokacin a ranar Juma’a yayin da ya ziyarci cibiyar gwajin fasahohin noma, inda kwararrun kasar Sin ke baje kolin fasahohin zamani na inganta noma dake birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha, ya ce kasashen Afirka da Sin na aiki tare wajen samar da gamammen tsarin bunkasa noma, wanda zai ingiza matsayin nahiyar Afirka zuwa ga cimma nasarar samar da isasshen hatsi da wadatuwar abinci....
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta dauki matakai wajen samar da duniya mai zaman lafiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a matsayin muhimmin ginshiki na tsarin kasa da kasa, dole ne ta dauki matakai na zahiri, na musamman, da kuma a bayyane kan hanyoyi guda biyu masu kamanceceniya da juna, don samar da duniya mai zaman lafiya, da duniya mai shirin fadada hadin gwiwar tattalin arziki. A yayin taron kolin shugabannin kungiyar hadin gwiwar Shaghai “SCO” karo na 25 a birnin Tianjin na kasar China, shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, a cikin tsarin karfafa hadin...
    Ƙungiyar Arewa ta ’Yan Jarida (ABMPF) ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da rushe Kasuwar Alaba Rago da Gwamnatin Jihar Legas ta fara, tana mai cewa matakin ya jawo asarar biliyoyin naira tare da barin dubban ’yan kasuwa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Yelwa, ya ce rusau ɗin ya haddasa wa ’yan kasuwar asarar kimanin Naira biliyan 20, tare da ruguza shaguna da wuraren ibada fiye da 40, abin da ya ce “bai dace ba kuma yana iya jawo rikicin ƙabilanci.” Kungiyar ta roƙi gwamnonin Arewa, ’yan majalisa da sarakuna na gargajiya su shiga wajen tabbatar da kare haƙƙin ’yan Arewa da suke zaune a Legas. Haka kuma ta yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya...
      Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori.   Kafin liyafar maraba, Shugaba Xi da madam Peng Liyuan sun yi maraba da shugabannin kasashen waje da matansu cikin fara’a, inda suka mika musu hannu tare da gaisawa, kuma suka dauki hotuna tare da su.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar Mohammed Sinwar, wanda aka daɗe ana ɗauka a matsayin jagoranta a Gaza. Wannan tabbaci ta Hamas ta bayar na zuwa ne fiye da watanni uku bayan Isra’ila ta ce ta kashe shi a wani harin sama. Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  Xi na karɓar baƙuncin taron SCO a China Hotunan da Hamas ta fitar ranar Asabar sun nuna Sinwar tare da wasu manyan shugabannin siyasa da na soji, waɗanda aka bayyana a matsayin “shahidan kwamitin soji.” Mohammed Sinwar, shi ne ƙanen Yahya Sinwar wanda Isra’ila ke zargi da jagorantar harin ranar 7 ga Oktoban 2023 a Isra’ila, rikicin da har yanzu wutarsa ke ƙara ruruwa. Kamfanin Dillancin Labaran...
    Gaskiya dai inda matsalar take shi ne, rashin wayewa da wasu mazan suke da shi, mafi yawa kuma mazan da suke da rashin ilimi su ke da wannan dabi’ar da take ba, dauwamammiya ba. Hakan gaskiya kwata-kwata bai dace ba, saboda an fi so namiji ya auri mai ilimi, wacce za ta tarbiyyantar da ‘ya’ya kan hanya ta gaskiya, da tarbiyya gurin rayuwa ta yau da kullum. Amma idan aka ce mace ba tada wani wayewa to, ba ita kadai za ta zauna cikin wannan rashin wayewar ba, har sai ya kai ga yaran da aka haifa suma su zama cikin duhun kai, su kasa mu’amala da al’umma. Saboda duk mutum wanda yake da rashin wayewa yana tare da tsatstsauran/baudadden...
    Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar. Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a yayin wani biki a birnin Nyala na kasar Sudan, ko da yake kamfanin dillancin labaran  Reuters ya kasa tabbatar da inda yake. Nyala, daya daga cikin manyan biranen kasar Sudan dake yankin Darfur, wanda kuma shi ne babbar tungar mayakan kungiyar RSF, kungiyar da ta nada nata firaminista da majalisar shugabancin karkashin jagorancin Dagalo. A ranar 16 ga watan Afrilu, Dagalo, kwamandan rundunar RSF  ya...
    Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma a samu wannan harshen ya ci gaba da yaduwa kamar wake dan arba’in. An taba yin wani shugaban kasa da ya ayyana nazartar wasu darussa a matsayin bata lokaci domin bai ma san a ina za su yi aiki ba. Duk kuwa da kasancewar duk kasar da ya ratsa a Arewacin kasar domin yakin neman zabe, da harshen Hausa yake magana. Abin da nake nufi...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  A cewarta, wannan mataki ya biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku a ranar 15 ga qatan Agusta, 2025. Ambaliyar ta shafi dubban jama’a kuma ta lalata gidaje da dama. Binciken da NEMA tare da wasu ƙungiyoyin agaji suka gudanar ya nuna cewa gidaje 2,557 ne abin ya...