Aminiya:
2025-11-15@21:24:38 GMT

PDP za ta sake farɗaɗowa idan shugabanninta suka cire girman kai — Anenih

Published: 15th, November 2025 GMT

Tsohuwar Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP, Iyom Josephine Anenih, ta ce jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi idan shugabanninta suka cire girman kai suka mayar da hankali kan yi wa jama’a hidima.

Ta bayyana haka ne yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan a ranar Asabar.

PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso

Ta ce har yanzu ’yan Najeriya da dama suna sa ran jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi domin yi musu jagoranci.

Anenih, ta yi gargaɗin cewa PDP na iya zama tarihi idan ba a gyara matsalolinta ba.

“Idan ba mu fuskanci matsalolinmu ba, PDP za ta zama tarihi, labarin yadda sakaci da girman kai suka lalata babbar jam’iyyar siyasa mafi girma a Afirka,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa rikicin cikin gida, rashin ladabi, da cin amanar juna ne suka raunana jam’iyyar.

“Mambobinmu su ne ƙarfin PDP na gaskiya. Sun yi tsayin daka duk da matsalolin da ake fuskanta. Wannan babban taro dole ne ya girmama jajircewarsu,” ta ce.

Anenih, ta roƙi shugabannin jam’iyyar su kawo ƙarshen rigingimu da suka dabaibaye ta hanyar haɗa kai don sake gina jam’iyyar.

Ta ce Najeriya na buƙatar jam’iyyar adawa mai ƙarfi, wacce za ta kawo ƙarshen talauci da rashin tsaro da ake fama da su.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi

Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar.

Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa Cin Zarafi (SARCs) da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) a Ilorin da kuma Asibitin Kwarari ta Sobi da ke Alagbado.

Kwamishiniyar ta bayyana cewa cibiyar an kafa ne tare da hadin gwiwar ofishin Uwargidar Gwamna, domin jinya kyauta da kuma kwantar da hankali, da tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafi a jihar.

Afolashade ta ƙara da cewa bincike da tantancewar da ake yi yanzu zai taimaka wajen tantance ingancin kulawar da ake bayarwa, da gano wuraren da ake bukatar gyara domin samar da tsarin taimako mai inganci da niyya kai tsaye ga masu bukata.

Ta kuma jaddada bukatar ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki tare da horar da ma’aikatan cibiyoyin SARC a fannin tattara bayanai da bayar da rahoto domin inganta tsarin tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafin jinsi.

Ali Muhammad Rabiu/Ilorin

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HOTUNA: Yadda Babban Taronjam’iyyar PDP ke gudana
  • Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
  • ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027
  • Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar
  • Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa
  • Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA
  • Dalilin da ya kamata PDP ta jingine taron da za ta gudanar— Saraki
  • Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi
  • Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna