Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU
Published: 15th, November 2025 GMT
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Nsukka ta ce Gwamnatin Tarayya na lalata makomar ƙasar nan saboda rashin cika yarjejeniyar 2009.
A taron manema labarai da ta gudanar a Jami’ar Jihar Benuwe da ke Makurdi, Kodinatan yankin, Kwamared Christian Opata, ya ce gwamnati ba ta jajirce wajen magance matsalolin da suka shafi ɓangaren ilimi.
Ya yi magana ne a madadin jami’o’i takwas da ke yankin.
Opata, ya ce an tattauna tare da ƙumla yarjejeniyoyi da dama tsakanin ASUU da gwamnati tsawon shekaru, amma babu wani ci gaba da aka samu.
Ya zargi jami’an gwamnati da yin lƙawarin ƙarya da gangan.
Ya ce ASUU ta dakatar da yajin gargaɗin da ta yi kwanan nan saboda ɗalibai, iyaye, da ƙungiyoyin ƙwadago, amma har yanzu gwamnati ba ta ɗauki aniyar warware matsalar ba.
Opata, ya gargaɗi gwamnati cewa idan ba ta kammala tattaunawar cikin wata ɗaya ba, jami’o’i na iya sake tsunduma yajin aiki.
ASUU, ta kuma zargi wasu jami’an gwamnati da yaɗa bayanan ƙarya game da tattaunawar, musamman batun biyan bashin albashi da wasu kuɗaɗen da aka riƙe musu.
Kungiyar ta ce Najeriya na da isasshen kuɗi, amma gwamnati ce ba ta yi niyyar saka hannun jari a ilimi.
Sun roƙi sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin ƙwadago, ɗalibai, da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su matsa wa gwamnati lamba don ganin an daidaita abubuwa.
ASUU ta ce malamai na cikin tsaka mai wuya saboda ƙarancin albashi, kuma ba ya isarsu wajen al’amuransu na yau da kullum.
Ƙungiyar ta sake jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta cika alƙawarun da ta ɗauka a baya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alƙawari Ɗalibai tattaunawa Yajin aiki yarjejeniya
এছাড়াও পড়ুন:
An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.”
“Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira da kwarewa,” in ji sanarwar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA