An fara koyar da aikin jarida a Nijeriya tun farkon bayan samun ‘yancin kai, kuma BUK ta kasance cikin jami’o’in farko da suka kafa sashen Koyar da Aikin Jarida (Mass Communication). A tsawon shekaru, jami’ar ta samar da fitattun ‘yan jarida, malamai, da ƙwararrun ma’aikatan kafofin watsa labarai da ke taka rawa a fadin ƙasar.

An gina ra’ayin kafa wannan cibiyar ne a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Umaru A. Pate, shahararren masani a fannin jarida kuma jajirtaccen mai fafutukar gyaran tsarin kafafen yaɗa labarai a ƙasa. Hangen nesa da shawarwarinsa sun taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa madogarar bincike da ci gaban ilimin jarida a BUK.

Da zarar an kammala cikakken kafuwar cibiyar, ana sa ran za ta ƙara ɗaukaka sunan Jami’ar Bayero Kano, tare da ƙarfafa matsayinta a matsayin cibiyar ƙwarewa, kirkira, da bin ka’idojin aikin jarida na gaskiya da rikon amana.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025 Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Labarai Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki November 14, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

A bisa wannan dalilin, ya kuma zama waji, manyan hafsohin tsaron su mayar da hankali, wajen ingnata jin dadi da walwalar dakarun sojin, musamman duba da cewa, manyan hafsoshin tsaron, su ba baki ne, kan wadannan kalubalen ba, domin kuwa kafin nada su, a baya an nada su kan makamai da ban da ban.

Kwarewar da kuma ilimin da suke da shi, a aikin soji, abu ne da zai taimaka masu wajen sauke nauyin da aka dora masu.

Abu na biyu shi ne, akwai bukatar a tsakaninsu, su hada karfi da karfe, domin su samu nasarar tunkarar aikin da ke a gabasu na tabbatar da tsaro a kasar, ba wai su rinka yi aiki, a daidaikunsu ba.

Kazalika, dole na rundunar sojin sama ta taimaka wa rundunar soji na kasa da kuma na ruwa, a yayin duka wani farmaki, tare da kuma yin musayar bayanai, a tsakansu.

Na ukun shi ne, dole ne su mayar da hankali kan samar dabaru, yayin gudanar da ayyukansu, musamman duba da irin sarkakiyar da ke tattare da yanayin kalubalen rashin tsaron kasar, misali duba da irin salon ayyukan ‘yan bindiga daji da masu garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan ta’adda, na kai hare –hare, wanda a yanayi irin wannan akwai matukar a dauki dabarun magance wannan barazanar ta su.

Yakar ta ‘yan bindiga daji da masu garkuwa da mutane da kuma masu aikata manyan laifuka, ya zarce ace manyan hafsoshin tsaro ne kadai za su yi hakan, domin kuwa, akwai kuma bukatar su tabbatar da sun samu goyon bayan alummar gari, musamman ta hanyar samun bayanan sirri.

Bugu da kari, na hudun shi ne, su tabbatar da dakarunsu na kai farmaki ta kasa duba da cewa, akasarin kalubalen rashin rashin tsaron ya ta’allaka ne na kasa, musamman duba da cewa maboyar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga daji, a kan doron kasa suke.

Dole ne manyan hafsoshin tsaron su sanya a zuciyarsu na cewa, su masu yin biyayya ne, ga kundun tsarin mulkin kasar kuma dole ne su kare su tabbatar da sun kare dorewar mulkin dimokaradiyyar kasar.

Kazalika, ya zama wajbi, a tantace a tsakanin ayyukan soji na kuma na siyasa.

A saboda haka ne, ba ma goyon bayan soji yin kutse a cikin batun abinda ya shafi fanin siyasa, musamman duba da cewa, kasashen da soji suka shiga cikin lamarin siyasa, sun kasance, ba su ji dadi ba, kuma bai kamata Nijeriya ta kasance a cikin jerin irin wadannan kasashen ba.

Wannan Jaridar na shawartar ‘yan siyasar kasar nan, kar su kutsa kansu kan batun da ya shafi lamuran ayyukan sojin kasar, musamman gwamnonin jihohin kasar, musamman duba da cewa, mun lura da irin wannan shishigin na wasu ‘yan siyasar kasar inda suke bayyana gazawar da sojin kasar ke yi, na tabbatar da tsaro a kasar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 November 13, 2025 Manyan Labarai Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2 November 13, 2025 Manyan Labarai Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su November 13, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki
  • Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya
  • Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 
  • An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea
  • NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane
  • Gwamna Nasarawa Ya Ce Za Su Samar da Masana’antu Don Ayyukan Yi
  • Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Ka’idoji Ga Samar da Injinan Noma a Najeriya
  • CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15