CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15
Published: 12th, November 2025 GMT
An gudanar da taron karawa juna sani game da aikin watsa shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15 ta hanyar talabijin ta zamani, wato taron karawa juna sani na hada fasahohin yada labarai, a jiya Litinin a birnin Guangzhou dake lardin Guangdong na kasar Sin. A yayin taron, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da sabbin manhajoji guda 10 da ya kirkiro ta hanyoyin kimiyya da fasaha don watsa gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15.
A yayin taron, mamban kwamitin tsara shirye-shirye na CMG Jiang Wenbo ya bayyana cewa, CMG ya ci gaba da zurfafa aikin gina tsarin tsara shirye-shiryen rediyo da bidiyo masu inganci ta dukkanin kafofin watsa labarai. Haka kuma, zai mai da hankali wajen nuna sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ta hanyar nuna shirye-shiryen rediyo da bidiyo masu inganci, da yin amfani da damar watsa manyan bukukuwa da gasanni wajen karfafa aikin yin kirkire-kirkire, ta yadda za a karfafa amfani da fasahar tsara shirye shiryen rediyo da bidiyo masu inganci da fasahar AI cikin aikin watsa gasannin motsa jiki daga wasu kafofi, da kuma inganta fasahohin watsa shirye-shiryen talabijin masu inganci, da aikin tsara shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki. (Mai Fassara: Maryam Yang)
ADVERTISEMENT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA
কীওয়ার্ড: tsara shirye shirye shirye shiryen
এছাড়াও পড়ুন:
Tarayyar Afirka (AU) Ta Yi Gargadi Akan Tabarbarewar Harkokin Rayuwa A Kasar Mali
Kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana matukar damuwarta akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a cikin kasar Mali, tana mai yin Ishara da yadda ‘yan ta’adda su ka killace iyakokin kasar da hana shigar da muhimman kayan bukatun rayuwa na yau da kullum.
Tarayyar Afirka ta kuma yi tir da yadda ake kashe farafen hula a kasar ta Mali da hakan yake haddasa rashin zaman lafiya da tsaro.
Bugu da kari, tarayyar Afirkan ta nuna cikakken goyon bayanta ga al’umma da kuma gwamnatin kasar Mali da iyalan wadanda aka kashe.
Kungiyar ta Afirka ta kuma nuna cewa a shirye ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukatuwa da shi a kasar ta Mali domin samun zaman lafiya.
Kungiyar “Jama’atu Nusratul-Islam Wal Muslimin” mai alaka da alka’ida ce ta killace iyakokin kasar da ake shigar da kayan bukatuwar yau da kullum. A cikin watannin bayan nan an rika nuna fayafayen bidiyo na yadda ‘yan al’ka’idar suke kona jerin motocin jigilar makamashin da ake amfani da shi. A wasu yankunan kasar ma,kungiyar ta kone gidajen man fetur.
Kamfar makamashin da ake fama da ita a cikin kasar ya sam shugaban kasar Assimi Goita, ya yi kira ga al’ummar kasar da su rage yawan tafiye-tafiye akan Ababan hawa saboda a rage yawan bukatuwa da makamashin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Fara Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Sheikha Hind Bint Maktoum November 10, 2025 Zaben Iraki: Gwaji don ‘yancin siyasa da kawo karshen tsoma bakin Amurka November 10, 2025 Iran da Rasha sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa November 10, 2025 Iran ta nuna damuwa kan zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan November 10, 2025 Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa November 10, 2025 Maduro ya kirayi taron CELAC da ya yi tir da ayyukan tsokana na Amurka a yankin Caribbean November 10, 2025 Lebanon: Mutane 28 ne suka yi shahada a hare-haren Isra’ila tun daga watan da ya gabata November 10, 2025 Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla November 10, 2025 Araghchi : Iran na yunkurin warware rikicin Pakistan da Afghanistan November 9, 2025 Kasashen (AES) za su hanzarta kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci