Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal
Published: 13th, November 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aiwatar da harajin shigo da man fetur da dizal na kashi 15, wanda a baya aka amince da shi domin daidaita farashin shigo da kayayyaki da yanayin kasuwa.
Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NMDPRA) ce, ta sanar da hakan a wata sanarwa da Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a, George Ene-Ita, ya sanya wa hannu.
Harajin ya janyo cece-kuce, inda wasu ke ganin zai kare matatun gida, yayin da wasu ke cewa hakan zai ƙara tsadar kayayyaki sannan ya tsauwala wa talakawa.
“Hukumar na shawartar ’yan kasuwa da su guji ɓoyewa ko sayar da mai da tsada ba bisa ƙa’ida ba.
“Harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal ba zai ci gaba da aiki ba,” in ji sanarwar.
NMDPRA ta tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da dizal a faɗin ƙasar nan, kuma babu ƙarancin mai da zai sanya dogayen layuka a gidajen mai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dakatarwa Gwamnatin tarayya Haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da sabon umarnin dakatar da Babban Taron Jam’iyyar PDP da ake shirin gudanarwa ranar 15 da 16 an watan nan a Ibadan, fadar Jihar Oyo.
Umarni na uku masu karo da juna ke nan da kotu ta bayar kan taron babbar jam’iyyar adawar mai cike da ruɗani.