Aminiya:
2025-11-09@22:10:51 GMT

Yarin Fika ya sauya sheƙa PDP zuwa APC a Yobe

Published: 9th, November 2025 GMT

Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar.

Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar.

Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci

Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar.

Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen goyon bayan jam’iyyar APC.

Ya ce, “Ina son ku gane cewa a halin yanzu, PDP da sauran jam’iyyun adawa a Yobe kamar sun ƙare.”

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka, ya bayyana zuwan Yarin Fika a matsayin babbar nasara ga jam’iyyar.

Ya ce, “Muna maraba da ku a cikin jam’iyyar, kuma za mu ba ku cikakkiyar damar da kowane mamba yake da ita. Za mu yi aiki tare da ku don ci gaban jam’iyyarmu.”

A nasa jawabin, Gwamna Buni ya nuna farin cikinsa da shigowar Yarin Fika da magoya bayansa.

Ya ce za su ci gaba da ƙoƙari wajen ci gaban jam’iyyar APC a Potiskum, da kuma dukkannin faɗin jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Buni Sauya Sheƙa Yarin Fika

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu.

Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Kangiwa.

Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga

“Na zo ne don jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici, amma dole ne mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu,” in ji shi.

Gwamnan, ya ce gwamnati ta fara bincike don gano musabbabin rikicin, inda ya ƙara da cewa an riga an kama wasu, kuma kotu za ta hukunta masu laifi.

Ya kuma sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 150 ga iyalan waɗanda lamarin abin ya shafa a ƙauyukan Fulani, Zabarmawa da Arewa.

“Babu wani dalili da zai sa rikici ya shiga tsakaninsu, tun da kun shafe sama da shekaru 100 kuna rayuwa tare cikin zaman lafiya,” in ji shi.

Gwamnan, ya kuma yi alƙawarin neman taimakon Gwamnatin Tarayya domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa, tare da yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya a yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yarin Fika ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a Yobe
  • Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar
  • Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar Yayin Daukar Ma’aikata
  • Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci
  • Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu
  • Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
  •  Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan