Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika
Published: 15th, November 2025 GMT
Kyaftin ɗin tawagar ƴan wasa matan Nijeriya ƴan ƙasa da shekara 17 (Flamingos), Shakirat Moshood, na cikin jerin ƴan wasa uku da suka kai matakin ƙarshe domin lashe ƙyautar Matashiyar Ƴar Wasan CAF ta 2025. Sauran ƴan wasan da ke fafatawa da ita su ne Moha El Madani daga Morocco da Adji Ndiye ta Senegal.
Moshood ta yi fice a manyan wasanninta a gasar cin kofin Duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 ta FIFA a 2025, ko da yake tawagar da Bankole Olowookere ke jagoranta ta tsaya a zagaye na 16. A duk tsawon gasar, ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan da suka yi ƙwazo a tawagar da kyakkyawan salon wasa.
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da DuniyaShakirat, wadda ke taka leda a Bayelsa Queens, ta kuma haskaka a gasar Premier ta mata ta Nijeriya (NWFL), inda ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar wa ƙungiyar nasarar lashe kofin a watan Mayu. Haka kuma ta kasance cikin manyan ƴan wasan da suka zura ƙwallo a wasan neman shiga gasar zakarun mata ta WAFU B a ƙasar Cote d’Ivoire.
ADVERTISEMENTZaɓenta cikin jerin ƴan wasa uku na ƙarshe ya ƙara tabbatar da tasirinta a ƙwallon ƙafa, tare da mayar da ita daya daga cikin fitattun matasan ƴan wasa da ke tasowa a nahiyar Afrika.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne
Kwanan baya, firayim ministan Japan Takaichi Sanae ta yi ikirari a fili cewa, “lamarin Taiwan lamari ne na Japan”, kuma tana da alaka da aiwatar da ikon kare kai na gama kai, inda a karon farko hakan ya nuna tsoma baki cikin batun Taiwan ta hanyar amfani da makamai, kuma a karon farko ya yi barazanar yin amfani da karfin tuwo kan kasar Sin.
Kalaman Takaichi game da Taiwan sun tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma sun saba wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin asali na dangantakar kasa da kasa, da lalata tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, kana sun saba wa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da ruhin takardu hudu na siyasa tsakanin Sin da Japan, kazalika sun lalata tushen siyasa na dangantakar Sin da Japan, kuma sun cutar da jama’ar Sin.
Ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” ta samu amincewa a tsakanin daukacin al’ummun duniya. Taiwan wani yanki na Sin da ba za a iya ware shi ba, kuma al’amuran Taiwan cikakkun al’amuran cikin gida ne na Sin, sannan wannan gaskiya ce da duniya ta amince da ita, kuma wani muhimmin bangare ne na tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu.
ADVERTISEMENTKalubalantar ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” tamkar wasa da wuta ne, kuma tabbas kaikayi zai koma kan mashekiya, don haka ya kamata Japan ta yi waiwaye a kan tarihi, ta janye kalaman da ba su dace ba! (Mai zane da rubutu: MINA)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA