Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne
Published: 14th, November 2025 GMT
Kwanan baya, firayim ministan Japan Takaichi Sanae ta yi ikirari a fili cewa, “lamarin Taiwan lamari ne na Japan”, kuma tana da alaka da aiwatar da ikon kare kai na gama kai, inda a karon farko hakan ya nuna tsoma baki cikin batun Taiwan ta hanyar amfani da makamai, kuma a karon farko ya yi barazanar yin amfani da karfin tuwo kan kasar Sin.
Kalaman Takaichi game da Taiwan sun tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma sun saba wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin asali na dangantakar kasa da kasa, da lalata tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, kana sun saba wa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da ruhin takardu hudu na siyasa tsakanin Sin da Japan, kazalika sun lalata tushen siyasa na dangantakar Sin da Japan, kuma sun cutar da jama’ar Sin.
Ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” ta samu amincewa a tsakanin daukacin al’ummun duniya. Taiwan wani yanki na Sin da ba za a iya ware shi ba, kuma al’amuran Taiwan cikakkun al’amuran cikin gida ne na Sin, sannan wannan gaskiya ce da duniya ta amince da ita, kuma wani muhimmin bangare ne na tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu.
ADVERTISEMENTKalubalantar ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” tamkar wasa da wuta ne, kuma tabbas kaikayi zai koma kan mashekiya, don haka ya kamata Japan ta yi waiwaye a kan tarihi, ta janye kalaman da ba su dace ba! (Mai zane da rubutu: MINA)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kyautata harkokin masana’antu. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta ba da taimako wajen shigar da mambobin WTO su 130 cikin yarjejeniyar samar da sauki a ayyukan zuba jari domin neman ci gaba, ta yadda kowa zai cimma moriyar sakamakon dunkulewar duniya cikin adalci. (Mai Fassara: Maryam Yang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA