HausaTv:
2025-11-13@07:09:29 GMT

MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya

Published: 13th, November 2025 GMT

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun yi gargadi a jiya Laraba cewa, miliyoyin mutane a yankuna akalla 12 da ke fuskantar rikici a duniya, ciki har da Sudan da zirin Gaza, na fuskantar barazanar yunwa, tare da gabatar da bukatar gaggawa na samar da kudade don magance gibin tallafin abinci, sakamakon raguwar tallafin da kasashen duniya ke bayarwa.

A cikin wani rahoto na hadin gwiwa, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) da Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) sun sanya kasashen Haiti, Mali, Sudan ta Kudu, da Yemen cikin kasashen da ke fuskantar barazanar yunwa.

Rahoton ya kuma bayyana halin da ake ciki na yunwa a wasu kasashe shida wato Afganistan, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Myanmar, Najeriya, Somaliya, da Syria, a matsayin mai matukar tayar da hankali.

Kungiyoyin biyu sun yi gargadin cewa rashin samun kudade na agajin jin kai na nuni ne Babbar matsalar da za a iya matukar dai ba a dauki matakan gaggawa ba.

Hukumar samar da abinci ta duniya da FAO sun yi kira da a kara samar da n tallafi daga gwamnatoci da masu hannu da shuni, tare da lura cewa kudaden da aka samu har zuwa karshen watan Oktoba sun kai dala biliyan 10.5 ne  daga cikin dala biliyan 29 da ake bukata domin taimakawa masu fama da matsaloli irin wadannan a duniya.

Rahoton ya yi nuni da cewa, Amurka wadda ita ce kasar da ta fi bayar da tallafi ga kungiyoyin biyu a bara, ta rage yawan taimakon da take ba wa kasashen waje karkashin jagorancin shugaba Donald Trump, sannan wasu manyan kasashe ma sun rage ayyukan ci gaba da taimakon jin kai, ko kuma sun bayyana aniyarsu ta rage yawan taimakon da suke bayarwa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Shugaban Iran Ya Aike Da Wasika Ta Musamman Zuwa Ga Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya November 12, 2025 Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki November 12, 2025 Iran Da Pakistan Sun yi Kira Da Yin Aiki Tare Don Tunkarar  Makiyansu November 12, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Rikicin Yankin November 12, 2025 Gabon: An Daure Mata Da ‘Dan  Tsohon Shugaban Kasa Bongo Shekaru 20 A Gidan Yari November 12, 2025 Tanzania: MDD Ta Yi Kira Da A Yi Bincike Akan Daruruwan Mutanen Da Aka Kashe Sanadiyyar Rikcin Zabe November 12, 2025 Iran Ta Zama Memba A Kungiyar Tattara Bayanai Na  Ilimomi Da Kere-kere Ta Duniya ( ISKO) November 12, 2025 Iran: Ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin November 12, 2025 Araghchi: Matsalar Yammacin duniya ita ce ci gaban kimiyyar Iran ba makaman nukiliya ba November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar

‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Kimanin ‘yan kasar miliyan 21 ne aka tantance domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar dokoki 329, Wadannan za su zabi shugaban kasa kuma su amince da sabuwar gwamnatin, wadda sabon firaminista zai kafa.

A cewar jami’an zabe, za a sanar da sakamakon cikin sa’o’i 24 bayan kammala zaben.

Firaminista Mohammed Shia al-Soudani ya bayyana zaben a matsayin wanda ya gudana “a cikin yanayi mai aminci da kwanciyar hankali,” yana yabon jami’an tsaro saboda kiyaye tsarin.

Al-Soudani, wanda aka zaba a shekarar 2022, yana neman wa’adi na biyu kuma zai bukaci samun rinjaye a majalisar.

A Iraki, doka ta bukaci a gudanar da zaben ‘yan majalisa akalla kwanaki 45 kafin karshen wa’adin majalisar da ke tafe.

A kasar Iraki, ana rarraba rassan gwamnati a bangarori guda uku bisa ga addini : shugabancin kasa daga bangaren Kurdawa, mukamin Firaminista daga ‘yan Shi’a sai kuma Kakakin Majalisa daga ‘yan Sunni, domin tabbatar da wakilcin dukkan bangarorin al’umma a cikin gwamnati.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita November 11, 2025 Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar November 11, 2025 Hamas ta soki kudurin Isra’ila na yin dokar hukuncin kisa kan laifin ta’addanci November 11, 2025 Iran Za Ta Harba Taurarin Dan Adam Guda Uku Zuwa Sararin Samaniya November 11, 2025 Lebanon: An Saki Hannibal Kaddafi Bayan Zaman Kaso Na Shekaru 10 November 11, 2025 An Sake Bude Gidajen Mai Da Makarantu Da Aka Rufe A Kasar Mali November 11, 2025 Trump Ya Yi Wa Ma’aikatan Filayen Jiragen Sama Barazana November 11, 2025 Donald Trump Na Amurka Ya Karbi Bakuncin Shugaban Rikon Kwaryar Kasar Syria Ahmad Shar November 11, 2025 Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni 9 Da Aka Zartarwa Da Hukuncin Kisa Shekaru 30 A Baya November 11, 2025 Hukumar Alhazai Ta Kasa A Nigeriya Ta sanar Da Rage Kudin Farashin Aikin Hajji Na Bana November 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki
  • Iran Ta Zama Memba A Kungiyar Tattara Bayanai Na  Ilimomi Da Kere-kere Ta Duniya ( ISKO)
  • Iran: Ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin
  • Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar
  • Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar
  • Trump Ya Yi Wa Ma’aikatan Filayen Jiragen Sama Barazana
  • Hukumar Kare Hakkin Bil Adama Ta M D D Ta yi Gargadi Game Da Abin Da ke Faruwa A El-Fasher
  • ‘Yan Jarida 44 Ne Su Ka Yi Shahada A Sansanonin Hijira Na Gaza
  • Tarayyar Afirka (AU) Ta Yi Gargadi Akan Tabarbarewar Harkokin Rayuwa A Kasar Mali