2025-11-13@12:52:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8984

«Caleb Muftwang»:

    1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo  Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari...
      Daga karshe Tanimu Akawu ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim da su kasance masu hakuri kada suyi hassada kuma su dage da addu’oi, Harkar fim sana’ace da ake samun rufin asiri da daukaka, kuma fim sana’ace wadda sai dai kai ka barta ba dai ta barka ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nishadi...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa...
    Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta dakatar da wani Hakimi da Dagaci a ƙaramar hukumar Funakaye bayan barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin. Rahotanni sun ce rikicin dai ya yi sanadin mutuwar ɗan sanda ɗaya tare da jikkatar wasu jami’an tsaro da dama. Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur...
    Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aiwatar da harajin shigo da man fetur da dizal na kashi 15, wanda a baya aka amince da shi domin daidaita farashin shigo da kayayyaki da yanayin kasuwa. Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NMDPRA) ce, ta sanar da hakan a wata sanarwa da Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a, George...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar. Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa...
    A ci gaba da aikace-aikacen yaki da ta’addanci da laifuffuka a fadin Jihar Taraba karkashin Operation Lafiya Nakowa, sojojin Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya / Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu nasarar kama wani wanda ake zargin dillalin makamai, tare da kwato makamai da harsasai daga hannunsa. Wannan na kunshe ne...
    Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa hangen nesansa na ƙarfafa masana’antu a jihar shi ne domin ƙirƙirar ayyukan yi da kuma inganta rayuwar jama’ar jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a Fadar Gwamnati ta Lafia, yayin da yake karɓar bakuncin sabbin shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu aiko rahotann dake Jihar (Correspondents’ Chapel)....
    A wani sabon yunƙuri na inganta haƙƙin yara da walwalarsu, Hukumar kula da kananan yara ta MDD wato UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Wayarda kan jama’a da ta Ƙasa (NOA) da Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC), da Hukumar Kula da katin zama dan Ƙasa (NIMC), sun kaddamar da shirin wayar da kai na...
    Gidauniyar  fadakar da al’umma akan dokoki da ka’idoji ta Nijeriya ta kaddamar da kwamiti a jihar Nasarawa domin aiwatarwa da sa ido kan shirin mata, zaman lafiya da tsaro, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen gina zaman lafiya a cikin jihar. Daraktan gudanarwa na gidauniyar, Mista Peter Maduoma, ne ya bayyana hakan a Lafia yayin...
    LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ministan FCT ya je filin mai lamba 1946 a ranar Litinin inda ya zargi sojoji da hana jami’ai daga Ma’aikatar Kula da Ci Gaban FCT aiwatar da umarnin dakatar da aiki a filin.   Ana zargin cewa, filin yana da alaka da tsohon Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu...
    Wani babban ɗan Kasuwar Singa da ke Jihar Kano, Alhaji Salisu Abdullahi, ya ce ya yi asarar kaya da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 120 a gobarar da ta auku da safiyar ranar Alhamis, wadda ƙone shaguna da yawa. “An kira ni da misalin ƙarfe 6 na safe, na garzaya zuwa kasuwa, sai kawai na...
    Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar.   Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na...
    Ministocin harkokin wajen Iran da na Rasha sun tattauna ta  wayar tarho gabanin taron kwamitin gwamnonin IAEA A yayin tattaunawar Araghchi da Lavrov, sun yi musayar ra’ayi kan batutuwa daban-daban, ciki har da rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan, tare da jaddada muhimmancin yin shawarwari don warware batutuwan da ba su dace ba. Babban...
    A yammacin jiya  ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar 2025, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci ta hanyar amfani da na’urorin lantarki. A taronta na manema labarai, Hukumar ta bayyana cewa...
    Gwamnan Sule ya ce irin wannan jaridar da ke kan gaba ta zaɓo shi a matsayin gwarzon gwamna, abun farin ciki ne sannan ya yaba wa kamfanin bisa tabbatar da sahihancin labarai da daidaitasu wanda hakan yasa ta bambanta ta da takwarorinta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu...
    Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun yi gargadi a jiya Laraba cewa, miliyoyin mutane a yankuna akalla 12 da ke fuskantar rikici a duniya, ciki har da Sudan da zirin Gaza, na fuskantar barazanar yunwa, tare da gabatar da bukatar gaggawa na samar da kudade don magance gibin tallafin abinci, sakamakon raguwar tallafin da...
    A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu...
    Kungiyar Kare Muradun Musulmai (MURIC) ta bukaci a gaggauta tsige Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), saboda matsayinsa kan batun rashin tsaro a Najeriya. Aminiya ta rawaito cewa, a cikin wani rubutu a baya, Amupitan wanda a lokacin malami ne a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya ce “abu ne...
    Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025. Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar. Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a...
    Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar...
    Kasar Sin ta bukaci Japan da ta daina yi wa masu fafutukar neman “‘Yancin kan Taiwan”, ingiza mai kantu ruwa, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun ya bayyana a yau Laraba. An ruwaito cewa, gwamnatin Japan a ranar Talata ta ba da wata lambar girmamawa ga tsohon “wakilin Taiwan...
    Aƙalla mutum 12 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani turmutsutsu da ya faru yayin jarabawar ɗaukar aikin soja a Filin Wasa na El-Wak da ke Accra, babban birnin ƙasar Ghana. Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da ɗaruruwan matasa masu neman aikin suka kutsa cikin filin wasan ba...
    Taron ya hada bijiman masana, da masu tsara manufofi, da masu ilimi,da masu bincike, da abokan hadin gwiwa na haɓaka harkar ilimi daga Afirka, Kudancin Asiya, da Birtaniya don tattauna dabarun inganta ilimi ta hanyar harshe.   Dr. Alausa, ya jaddada cewa, yayin da kiyaye harsunan asali har yanzu yana da mahimmanci ga al’adu, amma...
    Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi...
    Tawagar matan Najeriya ’yan ƙasa da shekaru 20, Super Falconets, ta lashe gasar Yammacin Afirka ta bana WAFU B U-20, bayan ta doke Black Princesses ta Ghana da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a safiyar Talata. An fafata wasan ne a filin Stade Omnisports da ke Jamhuriyar Benin, inda Akekoromowei, Alaba Olabiyi...
    Wakil ya ce, bayan samun rahoton, tawagar ‘yansanda karkashin jagorancin jami’in ‘yansanda na sashin, CSP Holman Simon, sun ziyarci wurin nan take domin tantance irin barnar da aka yi.   Ya bayyana cewa, binciken farko ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Alhassan Jibrin, wanda aka fi sani...
    ’Yan sanda a Jihar Kano sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux mallakar ofishin mataimakin gwamnan jihar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wadda aka sace kwanan nan a harabar gidan gwamnati. Majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano sun ce an sace motar ce cikin dare, lamarin da ya kai ga tsare direban da motar ke hannunsa, Shafiu...
    A shekaru fiye da 20 da suka gabata, birnin Wenzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin ya yi suna domin samar da takalma, kuma kayayyakin da ya samar sun samu karbuwa a duniya domin suna da araha. Amma ma’aikatan kamfanonin samar da takalma sun yi aiki har na tsawon awoyi 14 a kowace rana, inda...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko...
    Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya gargaɗi ’yan wasan ƙasar da su guji tafka kura-kurai a wasan da za su buga da Gabon a ranar Alhamis. Ekong ya yi wannan gargaɗi ne kafin fara atisayen ’yan wasan a safiyar Talata, a yayin da suke ci gaba da shirin fafatawar neman gurbin...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka tana shirin kafa sanssanin soji  don aikewa da dubban dakaru zuwa iyakar Isra’ila da yankin Gaza, adaidai lokacin da ake fargabar wata sabuwar kasada da kuma sha’awar taimakawa gwamnatin mamaya wajen karbe ikon kula da yankin a nan gaba. Masharhanta na ganin wannan shirin yana zuwa ne saboda irin...
    Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya  Mohammad Bin Salman a wata ziyara da suka kai birnin Riyadh a baya bayan nan. Wannan sakon yana nuna irin kokarin da ake yi ne na ganin an daidaita da kuma  kara yin aiki tare...
    Ministan Tsaron nageriya, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa tare da shugabancin rundunar soji za su kare kowane jami’i da ke bakin aikinsa bisa doka. Badaru ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ma’aikatar tsaro kan bikin tunawa da Sojojin Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka gudanarwa a Cibiyar...
    Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tare da shugabannin Rundunonin Sojin Najeriya, za su ci gaba da kare duk wani jami’i da ke gudanar da aikinsa bisa doka. Badaru, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a taron da aka shirya domin bikin tunawa da Sojojin Najeriya na...
    A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.”   “Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira...
    Mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da jawabi yayin taron kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu da aka gudanar jiya Talata, inda ya yi kira da a inganta mika mulki cikin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu. Sun Lei ya ce, Sin ta bukaci dukkan bangarorin kasa da kasa da...
    Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), ta ayyana Najeriya ɗaya daga cikin jerin ƙasashen da za su fuskanci matsananciyar yunwa. Ta kuma yi gargaɗin cewa ƙarin mutane a duniya na iya fuskantar yunwa saboda ƙarancin kuɗin tallafi. Rahoton da Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da WFP suka fitar, ya nuna...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar. Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse. Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada...
    Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse....
    Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya. Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga...
    Daga Khadijah Aliyu Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Jagorancin Shirin Ilimi da Ƙarfafa Matasa a Arewa maso Yammacin Najeriya (EYEPINN) wanda kungiyar  Tarayyar Turai ke daukar nauyinsa domin fadada damar samun ingantaccen ilimi da kuma karfafa gwiwar matasa a yankin. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Kano, karkashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na...
    Ya bayyana cewa mutanen sun fita da sassafe don wani aiki, amma ‘yan bindigar suka tare su suka kashe su tare da tserews da babur ɗinsu . Mista Ajeh, ya roƙi hukumomin tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu. Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin...
    A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a watan karshe. Wannan kiran na MDD ta zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Tanzania su ka tuhumi wasu daruruwan mutane da cin amanar kasa saboda Zanga-zangar  kin...
    Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya. Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka...
    Hukumar Kula da jin dadin mahajjan Jihar Taraba ta bayyana 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe ga masu niyyar yin hajji don kammala biyan kuɗin tafiyar hajji ta shekarar 2026. A cewar wata sanarwa da Sashen Bayani na Hukumar ya fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Hamza Baba Muri, an ƙayyade sabon kuɗin hajjin...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe. Gwamnan ya ce...
    A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati,...