MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa
Published: 12th, November 2025 GMT
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), ta ayyana Najeriya ɗaya daga cikin jerin ƙasashen da za su fuskanci matsananciyar yunwa.
Ta kuma yi gargaɗin cewa ƙarin mutane a duniya na iya fuskantar yunwa saboda ƙarancin kuɗin tallafi.
Rahoton da Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da WFP suka fitar, ya nuna cewa rikice-rikice da tashin hankali ne ke jawo matsananciyar yunwa a ƙasashen da ke cikin hatsari.
Rahoton ya bayyana ƙasashen Haiti, Mali, Falasdinu, Sudan ta Kudu, Sudan da Yemen a matsayin waɗanda ke cikin mafi munin hali inda jama’a ke fuskantar barazanar yunwa mai tsanani.
Haka kuma, Afghanistan, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Myanmar, Najeriya, Somaliya da Siriya sun shiga jerin ƙasashe masu matuƙar damuwa.
Rahoton ya kuma ambaci Burkina Faso, Chadi, Kenya da kuma yanayin ’yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh.
Darakta Janar na WFP, Cindy McCain, ta ce, “Muna fuskantar matsalar yunwa da za a iya kauce mata gaba ɗaya, amma idan ba a ɗauki mataki ba, hakan zai haifar da ƙarin rikici da rashin kwanciyar hankali.”
Rahoton, ya ce kuɗin agajin jin-ƙai yana raguwa sosai, inda aka samu dala biliyan 10.5 kacal daga cikin dala biliyan 29 da ake buƙata don taimaka wa waɗanda ke cikin hatsari.
Saboda ƙarancin kuɗi, WFP ta rage tallafa wa ’yan gudun hijira da waɗanda aka raba da muhallinsu, sannan ta dakatar da shirye-shiryen ciyar da ɗalibai a wasu ƙasashe.
Hukumar FAO kuma ta yi gargaɗin cewa harkar noma na cikin hatsari, wanda shi ne ginshiƙin samar da abinci da hana matsalolin yunwa sake faruwa.
An bayyana cewa tallafi ake buƙata don samar da iri da kula da dabbobi kafin lokacin shuka ko wani sabon rikici ya sake ɓarkewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya Najeriya Ƙasashe yunwa
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci
Tafarkin samun ci gaba mai karfi da inganci, da karuwar kuzarin kirkire-kirkire da ci gaba da fadada bude kofa, su ne suka hadu suka samar da wani sabon matsayi ga tattalin arzikin kasar Sin a taswirar tattalin arzikin duniya. Ci gaba mai inganci da fadada bude kofa, ba muhimman jigon ne dake ingiza tattalin arzikin Sin kadai ba, har da nuna yanayin sauyawar abubuwan dake haifar da ci gaba a duniya. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ta kafar intanet, ya nuna yadda masu bayar da amsa daga fadin duniya suka yi imanin cewa, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba ta kowace fuska ba tare da tangarda ba, lamarin da ya samar da tabbaci ga tattalin arzikin duniya.
Karfin tattalin arzikin Sin ya dagora ne da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi da ke samun ci gaba cikin sauri, wadda ake ganin saurin ci gabanta ta hanyar kirkire-kirkire. Nazarin ya nuna cewa, kaso 93.6 na wadanda suka bayar da amsa, sun yi imanin cewa, kirkire-kirkire na taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki mai inganci na Sin. Wasu kaso 96.6 kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin na jagorantar manyan sauye-sauye a tsare-tsaren tafiyar da masana’antu da na tattalin arziki ta hanyar kirkire kirkiren kimiyya da fasaha.
A matsayinta na kasa ta biyu mafi yawan masu sayayya, kasar Sin ce ke da mutane masu matsakaicin kudin shiga mafi yawa a duniya, inda take da gagarumin karfin sayayya da na zuba jari. Nazarin ya nuna cewa, kaso 82.3 na masu bayar da amsu sun yi imanin cewa, kamfanonin kasashen waje za su iya amfani da fa’idojin da suke da shi wajen shiga kasuwar kasar Sin domin kara samun karfin takara a duniya. (FMM)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA