Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya
Published: 15th, November 2025 GMT
Bangaren sauka na kumbon Shenzhou-21, dauke da ‘yan sama jannatin na kumbon Shenzhou-20 wato Chen Dong, da Chen Zhongrui, da Wang Jie ya sauka doron duniya cikin nasara.
Sundukin ya sauka ne a yau Jumma’a a yankin Dongfeng na jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai, dake arewacin kasar Sin, kamar dai yadda aka tsara.
Rahotanni na cewa, dukkanin ‘yan sama jannatin suna cikin koshin lafiya. Kafin dawowarsu doron duniya sun shafe kwanaki 204 a sararin samaniya, lokaci mafi tsayi da ‘yan sama jannatin kasar Sin suka taba shafewa a samaniya, kamar dai yadda hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati ta Sin ko CMSA ta sanar.
ADVERTISEMENTKwamandan ‘yan sama jannatin Chen Dong, shi ne ya fara fitowa daga sundukin bayan saukarsa doron kasa. Kawo yanzu, Chen ne dan sama jannatin kasar Sin daya tilo da ya shafe jimillar sama da kwanaki 400 a sararin samaniya. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: yan sama jannatin
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Filin Jirgin Sama Na Kano
Shugaban Hukumar Gudanarwa Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na dawo da tsohon martabar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
Dakta Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai filin jirgin a Kano.
Ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi ta jami’an FAAN domin tantance halin da filin jirgin yake ciki yanzu, ciki har da ayyukan da ake gudanarwa da kuma waɗanda aka bari da nufin samar da cikakken tsari na zamani da dorewar ci gaba.
Ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin tsofaffin filayen jiragen sama masu tarihi a Najeriya da yankin Yammacin Afirka, wanda a da yake ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin tashi da saukar jirage da ke haɗa Najeriya da sauran sassan duniya.
“Mun zo ne mu gani da idonmu, tsoffin ayyuka da sababbi, domin mu tsara sabuwar hanya ta farfado da wannan fili tare da dawo da matsayinsa cikin fitattun filayen jiragen sama na yankin,” in ji Ganduje.
Ya jaddada cewa hukumar FAAN za ta tabbatar da inganta jin daɗin fasinjoji, kiyaye ƙa’idodin tsaro, da kuma haɓaka ingancin aiki bisa ka’idodin ƙasa da ƙasa.
Dakta Ganduje ya tabbatar da cewa abubuwan da tawagar ta gano a yayin ziyarar za su zama ginshiƙi wajen tsara sabuwar manuniya ta dabarun sake farfado da filin domin ya zama abin koyi a harkar gudanar da filayen jiragen sama da kuma abin ƙarfafa tattalin arzikin Arewa.
Tawagar ta ziyarci sassa daban-daban na filin jirgin, ciki har da zauren sauka da tashin fasinjoji, hanyar tashi da saukar jirage, da kuma rukunin jigilar kaya, domin gano wuraren da ake bukatar gaggawar gyara.
ABDULLAHI JALALUDDEEN, Kano.