2025-11-12@07:51:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8930
«yi wa Kiristoci»:
Babban Sakataren Hezbollah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa “Amurka, ta hanyar wakilanta na Isra’ila, tana neman kawar da karfin gwagwarmayar Lebanon da kuma ba sojojin kasar makamai don fuskantar Hezbollah,” yana mai jaddada cewa manufar wannan matakin shine “kawar da karfin soja da duk wani karfi fadin Lebanon domin Isra’ila ta ci gaba da cin karenta babu babbaa duk inda ta ga dama a cikin kasar.” Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa “An kafa Hezbollah ne bisa ka’idojin jihadi, kare mutunci mutunci, da alfaharin Lebanon, da goyon bayan Falasdinu,” yana mai cewa “daga 2000 zuwa 2023, mun kasance cikin yanayi na tsoro.” Ya bayyana cewa yakin baya-bayan yana a matsayin shinge ga mamayar Isra’ila, wanda ya tsayar da...
An kama diraben da ke jan motar Shafiu Sharp-Sharp, domin yi masa tambayoyi. “An riga an fara bincike. Ana yi wa direban tambayoyi, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke duba bidiyon CCTV,” in ji wata majiya. “An miƙa bayanan motar ga jami’an tsaro domin su gano motar da kuma kama ɓarawon.” Kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bai amsa kiran waya da saƙonnin da aka tura masa ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025 Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya,...
“Dukkanin bayanan da ake da su sun nuna cewa babu wani kisan gillar da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya… Wannan labarin ƙarya ne da ƙungiyoyi suka ƙirƙira, wanda Shugaba Trump ke ƙoƙarin yaɗawa. “Wannan magana za ta iya ƙara tayar da hankali a Nijeriya… ‘Yan ta’adda suna kai hare-hare a kasuwanni, coci-coci, da masallatai, kuma suna kashe kowa ba tare da bambance tsakanin Musulmi da Kirista ba,” in ji Bukarti yayin wata hira da gidan talabijin na Al-Jazeera. Masana da dama sun yi gargaɗin cewa irin wannan kalamai daga shugabanni na iya haddasa tashin hankali a ƙasar. Martanin Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Tarayya ta kuma mayar da martani ta hanyar ƙaryata batun cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a...
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana yadda wasu ’yan majalisa suka haɗa kai suka daƙile yunkurin tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio. Yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a Majalisar Tarayya da ke Abuja, Sanata Kalu ya tabbatar da cewa akwai yunkuri daga wasu ’yan majalisa na tsige Akpabio daga mukaminsa, wanda bai yi nasara ba. Babu wani gwamna da zai yi ƙorafin ƙarancin kuɗi a mulkin Tinubu — Sanwo Olu Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe Kalu wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Abia ne ya ce, “Kodayake an yi yunkuri, amma ba mu bari hakan ta faru ba. Shi ya sa kullum nake...
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Najeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda)”, inda aka haɗa...
Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da niyyar haɗa kai da hukumar wajen inganta jin daɗin ‘yan sanda da kyautata yanayin ayyukansu. Ya ce, “Gwamnatina na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa an kula da walwala da jin daɗin ‘yan sanda. Wannan ne dalilin da ya sa muke gyaran hedikwatar ‘yan sanda ta Zamfara a halin yanzu. “Haka kuma, muna gina wasu muhimman gine-gine a hedikwatar rundunar ‘yan sanda na Moble. Mun samu nasarori da dama a wajen, kuma muna da ƙarin shirye-shirye na gaba. “Na ji daɗin yadda sakataren hukumar ya ambaci batun ginin sabon unguwar ma’aikatan ‘yan sanda. Idan ka duba halin da barikin ‘yan sanda ke ciki yanzu, za...
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15
An gudanar da taron karawa juna sani game da aikin watsa shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15 ta hanyar talabijin ta zamani, wato taron karawa juna sani na hada fasahohin yada labarai, a jiya Litinin a birnin Guangzhou dake lardin Guangdong na kasar Sin. A yayin taron, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da sabbin manhajoji guda 10 da ya kirkiro ta hanyoyin kimiyya da fasaha don watsa gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15. CMG zai yi amfani da sabbin fasahohi, kamar kirkirarriyar basira ta AI da fasahar tsimin makamashi da kyautata ingancin hotuna da rediyo da dai sauransu, ta yadda zai samar da...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin. “Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu...
Shugabannin jam’iyyar APC a matakin unguwanni 35 da sakatarorinsu a faɗin Jihar Kuros Riba, sun nemi a tsige shugaban jam’iyyar na jihar, Mista Alphonsus Eba, bisa zargin badaƙala da kuɗaɗen jam’iyya da kuma nuna son kai wajen gudanar da harkokin jam’iyyar. Wannan buƙatar ta fito ne a cikin wata sanarwa da shugabanni da sakatarorin jam’iyyar suka rattaba wa hannu bayan taron da suka gudanar a garin Kalaba, babban birnin jihar, a ranar Talata. Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a Borno Shugabannin sun bayyana cewa idan ba a ɗauki mataki kan shugaban ba, akwai yiwuwar rikicin cikin gida ya durƙushe jam’iyyar a jihar. Da yake jawabi...
Kungiyar kasashe da cibiyoyin kasa da kasa ta fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ta yi Allah wadai da manyan laifukan da aka aikata a ƙasar Sudan bayan kwace El Fasher daga dakarn (RSF) suka yi, da kuma ƙaruwar tashin hankali a yankin arewacin Darfur da Kordofan. Wannan sanarwar, wadda ministocin harkokin waje da manyan jami’ai daga Australia, Belgium, Kanada, Denmark, Estonia, Hukumar Tarayyar Turai, Jamus, Iceland, Ireland, Luxembourg, New Zealand, Netherlands, Norway, Slovakia, Slovenia, Spain, Sweden, da Birtaniya, tare da goyon bayan Austria, Croatia, Cyprus, Czechia, Finland, Latvia, Poland, Romania, da Switzerland suka yi, ta nuna damuwa sosai game da rahotannin ta’asar da aka aikata a kan fararen hula. Wannan sanarwar haɗin gwiwa ta yi nuni da...
Wannan shi ne baje koli na farko bayan taron kwamitin kolin JKS da ya amince da shirin raya kasa na shekaru 5-5 karo na 15, wanda ya jaddada kudurin Sin na fadada bude kofarta. Halartar kamfanoni da adadinsu ya kai 4,108, daga manya da matsakaita da kananan kasashe ya tabbatar da cewa, kofar Sin a bude take ga kasa da kasa su shigo, su yi cudanya da hadin gwiwa domin samun ci gaba na bai daya. Karuwar adadin mahalarta tamkar kira ne cewa, duniya ta amince kuma tana goyon bayan manufofi da tsare-tsaren kasar Sin. Haka kuma, goyon baya ne ga kiran kasar Sin na dunkule tattalin arzikin duniya da bunkasa cudanyar bangarori daban-daban domin samun ci gaba tare. Bugu...
Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe. Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta. John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a Borno Mutumin da ake zargi da wannan aika-aikar mai suna Rabilu Sani, ɗan kimanin shekara 22, an gano cewa yana ɗauke da cutar kanjamau (HIV), kamar yadda mahaifin yarinyar ya tabbatar wa manema labarai. A wata hira da aka yi da mahaifin ta ta wayar tarho, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin Jakusko tare da wanda ake zargi, inda...
A shekarar 2023, Ronaldo, wanda ke taka Leda tare da Al Nassr ta Saudiyya, ya tabbatar da maganar da ya yi na cewa, zai rataye takalminsa nan ba da jimawa ba, “Idan ina nufin nan ba da jimawa ba, watakila shekara daya ko biyu zan ci gaba da kasancewa a wasan,” in ji shi. Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar yana da burin buga Kofin Duniya na shida a shekara mai zuwa, ya kusa lashe kofin a shekarar 2006, lokacin da Portugal ta sha kashi a hannun Faransa a wasan kusa da na karshe, a halin yanzu, Portugal ba ta sami gurbi a gasar 2026 ba, wadda za ta gudana a Amurka, Kanada, da Mexico, amma...
Shugaban tsaron kasar ta Iran ya yi watsi da rahotannin da ake yayatawa cewa iran ta bude wasu hanyoyin tuntuba da Washington, yana mai jaddada cewa ba a isar da wani sabon sako ga Amurka ba. Ali Larijani ya jaddada cewa fifikon Iran a koyaushe shi ne dage takunkumin da aka kakaba mata, wanda ya bayyana a matsayin kokarin diflomasiyya na gwamnatin kasar. Duk manufofin gwamnati da kokarin diflomasiyya suna mai da hankali ne kan kawo karshen takunkuman,” in ji shi. Ya bayyana ce sakon da ake yayatawa ya samo asali ne daga shawarwarin da akayi a baya, amma Amurka ba ta nuna sha’awar cimma yarjejeniya ba. Wannan bayanin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da...
Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita. Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu sama da 620, wanda hakan ya zama keta dukkan ka’idoji da kudurori na kasa da kasa da aka amince da su. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna Allah wadai da karya wannan yarjejeniya da aka yi akai-akai kuma muna daukar ‘yan mamayar da alhakin sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro da na jin kai. Muna jaddada cewa ci gaba da wannan lamari yana barazana ga yarjejeniyar...
Ministan Harkokin Wajen Sudan Mohieldin Salem ya yi Allah wadai da shirun da kasashen duniya suka yi game da ci gaba da cin zarafin dan Adam da Rundunar Taimakon Gaggawa ta (RSF) ke yi a yankunan El-Fasher, Darfur ta Arewa, da Bara, da Kordofan ta Arewa. Ya yi wadannan kalaman ne a lokacin wani taro a Port Sudan da Darakta Janar na Kungiyar Kula da kaura ta Duniya (IOM), Amy Pope, wacce ta isa Sudan don ziyarar kwanaki biyar, a cewar kamfanin dillancin labarai na SUNA. Salem ya yi Allah wadai da shirun da kasashen duniya suka yi game da ci gaba da take hakkin dan adam da RSF ke yi a El-Fasher da Bara. Ya jaddada bukatar hada karfi...
Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500. Wannan shi ne karo ba adadi da wannan gidauniyar ta Kogunan Kasar Hausa kuma shugaban hukumar Samarda Lantarki a yankunan Karkara Alhaji Abba Aliyu ta gudanar. An raba kayan Solar guda 500 da kuma kudin fara sana’o’in hannu ga wadanda suka sami horo a karkashin wannan gidauniya. Mataimakin Shugaban wannan gidauniya Suleiman Aliyu Abubakar ya bayyana cewa sama da shekara suna rana kyayyakin sun hada da solar domin kawo karshen matsalar wutar lantarki. Suleiman Aliyu Abubakar wanda ya wakilci MD Abba Aliyu a wajen taron yace Kayayyakin sun hada da fanka da kayan caji da na...
Daga Usman Muhammad Zaria Ministan Yada Labarai Alhaji Mohammed Idris, ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa jagoranci na gaskiya da tsari, yana mai cewa Jihar Jigawa ta zama abin koyi wajen gudanar da mulki da kuma ingantaccen aiki a ma’aikatu. Ministan ya yi wannan yabo ne lokacin wata ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan a Gidan Gwamnati da ke Dutse. Muhammad Idris ya tuna da wata ziyarar da ya taba kaiwa Jigawa a baya, lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin duba harkokin noma. Ya ce yadda ya ga ana yin noman rani ya sa shi shauki game da irin ci gaban da ake samu a jihar. Ya kuma bayyana godiyarsa kan kyakkyawan tarba...
Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa. Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron dan adam , kuma ya bayyana cewa an shirya harba tauraron dan adam guda uku na: Zafar, Paya, da Kowsar a farkon hunturu. A cewar Pars Today, ya yi Ishara da hadin gwiwar da Iran ke yi da wasu kasashe a fannin sararin samaniya, yana mai ambaton ayyukan hadin gwiwar da China kan ayyukan hadin gwiwar bincike da kasashen mambobin ECO. Wannan ayyukan hadin gwiwar...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori. Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin yana cikin shirin “Gwamnati da Jama’a” wanda ke karfafa al’umma, rage matsalolin sufuri da kuma karfafa harkokin kasuwanci. Ya ce shirin ya kunshi gina manyan hanyoyi guda shida a sassan jihar, masu tsawon kilomita 179 gaba daya, a kan kudin da ya haura Naira Biliyan 81. Hanyoyin sun hada da Mallam Madori zuwa Gari Uku zuwa Kanya Babba zuwa Malorin Kasim, ta ratsa ta...
Shahararren ɗan wasan wrestling, John Cena, ya samu nasarar lashe kambun Intercontinental a karon farko a tarihinsa. Cena ya lashe kambun ne da yammacin jiya Litinin, bayan ya doke Dominic Mysterio a birnin Boston, ƙasar Amurka. Sanata Jarigbe ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP Da wannan nasarar, yanzu John Cena ya cika burinsa na lashe dukkan manyan kambuna da ake bugawa a gasar wrestling. Ɗan wasan mai shekaru 48, wanda ake sa ran zai yi ritaya a watan Disamba mai kamawa, ya zuwa yanzu ya lashe kambuna 17 a gasannin daban-daban da ya shiga. Tuni dai Cena ya bayyana cewa bayan ritayarsa zai mayar da hankali wajen fitowa a fina-finan Hollywood,...
Alƙalin ya jaddada cewa wajibi ne a bi doka da oda domin kare tsarin dimokuraɗiyya, inda ya yi gargaɗin cewa karya doka na iya jefa ƙasa cikin ruɗani. A baya, Mai shari’a James Omotosho, ya taɓa bayar da irin wannan umarni, inda ya dakatar da PDP da INEC daga gudanar ko amincewa da sakamakon taron saboda rashin bin ƙa’idojin doka, ciki har da gaza bayar da sanarwar kwanaki 21 kafin gudanar da taron kamar yadda doka ta tanada. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya November 11, 2025 Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025...
DSP Aliyu ya gargaɗi jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya, inda ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin aikata hakan za a hukunta shi. Ya kuma roƙi mutane su dogara da sahihan bayanai daga hukumomi, tare da tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan ƙarƙashin CP Bello Shehu tana ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL November 9, 2025 Wasanni Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya November 9, 2025 Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025
Sanata Jarigbe Agom Jarigbe, mai wakiltar Arewacin Jihar Kuros Riba, ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Sanatan ya bayyana sauyin shekarsa ne a wasiƙar da Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya karanta a zauren Majalisar ranar Talata. Sauyin shekar ta kara yawan mambobin APC a Majalisar Dattawa zuwa 77
An kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin amfani da wannan tattaunawa wajen ƙarfafa dangantaka da Birtaniya, musamman wajen harkokin shari’a, musayar bayanan tsaro, da kula da ‘yan Nijeriya da ke fuskantar matsaloli a ƙasashen waje. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025 Manyan Labarai Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika November 11, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina November 11, 2025
’Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa, inda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a. Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, mai taken “Barazanar Rayuwa da Tsaron Ƙasa.” Ya ce matsalar tsaro a Arewa ba sabuwa ba ce, domin ta wanzu tsawon sama da shekaru 20. “Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da kuma hare-haren ’yan bindiga. “Mun kai wani matsayi da ’yan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yayin da tattaunawa kan makomar ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ke ci gaba da ɗaukar hankali, batun yadda za a haɗa jami’o’i masu zaman kansu cikin tsarin ƙungiyar ya sake tasowa. Wasu na ganin wannan sabon yunƙuri zai iya zama sabuwar hanyar ƙarfafa hadin kai tsakanin malamai, yayin da wasu ke gargadin cewa hakan na iya kawo tsaiko ga karatun wasu dalibai dake kauracewa jami’oin gwamnati sakamakon yawan yajin aiki da suke tsunduma lokaci zuwa lokaci. NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi...
A wajen taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro. Obasanjo ya ce, “Ku ne shugabannin yau, domin idan kuka bar gobe a hannun shugabannin yau, za su lalata komai, kuma ba za ku samu gobe mai kyau ba. Ku duba ƙasar Kamaru, shugabanta Paul Biya yana da shekara 92, to me za a ce game da matasan ƙasar?” Tsohon shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su tashi tsaye su jagoranci nahiyar Afrika domin makomarsu ta dogara da abin da suka yi a...
Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi. Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi. Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya samu rakiyar Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya miƙa kayan ne a hukumance a ranar Litinin ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, a Bulasa Warehouse da ke kusa da Birnin Kebbi. Sarkin Argungu, wanda ya yi jawabi a madadin Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa wannan kyauta na cikin manufofin Gidauniyar Sarkin Musulmi na inganta ilimi da...
Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba. Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike. Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da...
Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni 9 Da Aka Zartarwa Da Hukuncin Kisa Shekaru 30 A Baya
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa. “Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da kamfanin man fetur na Shell yake yi. Wannan kiran daga kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron kare muhalli na duniya a kasar Brazil. Shugaban kungiyar ta “Amnesty International” a Nigeria, Isa Sunusi ya bayyana cewa; Duk da cewa afuwar da gwamantin ta yi musu ci gaba ne,amma masu rajin kare muhallin na...
An kammala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na takwas (CIIE) a yau Litinin, inda aka samu daddale kulla cinikin dalar Amurka biliyan 83.49 a cikin yarjejeniyoyi da aka cimma na shekara guda, wanda adadin da aka samu ya karu da kashi 4.4 cikin dari idan aka kwatanta da na baya kuma ya kai wani sabon matsayi, kamar yadda hukumar kula da bajen kolin na CIIE ta bayyana. Dandalin baje kolin ya kai fadin murabba’in mita 367,000, inda ya jawo hankulan kamfanoni 4,108 daga kasashe da yankuna 138, lamarin da ya karya tarihin yanayin girma da adadin mahalartan na baya da aka gudanar. Baje kolin na tsawon kwanaki shida ya kunshi sabbin kayayyaki, da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa November 10, 2025 Daga Birnin Sin Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin November 10, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo November 10, 2025
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya EFCC ta ayyana neman tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva ruwa a jallo. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo mai ɗauke da hoton tsohon gwamnan da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin. Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP Hukumar ta ce tana neman Mista Sylva ne bisa zargin wata badaƙalar kuɗi da yawansu ya kai dala miliyan 14.8. EFCC ta ce tana zargin tsohon gwamnan da karkatar da kuɗin da aka yi niyyar amfani da su wajen gina matatar man fetur a ƙasar. Hukumar ta ce wata kotu ce a Jihar...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump November 10, 2025 Manyan Labarai Rundunar Sojin Sama Ta Kai Hari Kan ISWAP Da Ƴan Bindiga A Borno, Kwara Da Katsina November 10, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya ta yi tsananin gargadi game da kisan da ake yi a El-Fasher dake arewacin Darfur na kasar Sudan, ya bayyana birnin da cewar yana cikin mummunan yanayi da kuma karuwar hare-hare mafi muni a kwanaki 10 da suka gabata, Yankin El-Fasher yana kasancewa daya daga cikin garuruwan dake fuskantar mummunan yanayi na zubda jinni a fadin kasar Sudan, da kuma rikice-rikicen kabilanci da kai harin kan fararen hula, kuma yana barazanar karuwar rarrabuwar kai a kasar da tsawaita yakin da jawo kashe dubban mutane da kuma raba miliyoyi da gidajensu, Tun a watan aprilun shekara ta 2023 sojojin Sudan da dakarun sa kai na kungiyar RSF suka...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar, inda ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen kara inganta nukiliyar masana’antu, kuma yace kasarsa ba za ta taba yin watsi da shirin ta na nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba. Haka zalika ya jinjinawa iran game da irin gagarumin ci gaban da suka samu a fasahar nukiliya, inda suka shiga bangare masana’antu da ya yadu zuwa wasu bangarori daban daban. Hukumar kula da makamashin nukiliya...
Gwamnatin Tarayya ta nemi ƴan Nijeriya da su ƙwantar da hankali duk da tutsun diflomasiyya da ya taso tsakanin Nijeriya da Amurka. Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar gaisuwa ga Gwamna Umar A. Namadi. Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya “Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da tsaron Nijeriya daga duk wata barazana da zata kawo ruɗani, da kuma gyara duk wani tarnaki a dangantakar mu da abokan hulɗarmu na ƙasa da ƙasa, don haka, ƴan Nijeriya su samu nutsuwa,” in ji Idris. Ministan ya ziyarci...
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa. Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia. An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP ’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan...
Hukumar kula da jin daɗin alhazai ta birnin tarayya (FCT) ta saka ranar 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe da za a biya kuɗin Hajji na shekarar 2026, wanda aka tsara a N7,696,769.76. Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin hukumar a yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda jami’in hulɗa da jama’a, Muhammad Lawal Aliyu, ya buƙaci duk masu niyyar zuwa Hajji daga Abuja su bi ƙa’idojin da aka shimfida. An bayyana cewa tabbataccen kuɗin Hajjin ya samu ne bisa ƙayyadadden tsari daga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), sannan duk biyan kuɗin za a yi ne ta hanyar Banki, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, ba tare da karɓar kuɗi a hannu...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanya da kudinta ya kai Naira Biliyan 14 a Karamar Hukumar Malam Madori, wanda ke nuna jajircewar gwamnatinsa wajen bunkasa ababen more rayuwa1 karkashin shirin sabunta kudurori na gwamnatin tarayya wato “Renewed Hope Agenda.” A yayin taron kaddamarwar, an kuma gabatar da sabbin motoci ga shugabannin jam’iyyar APC guda takwas da masu tallata jam’iyyar a mazabar Arewa maso gabashin jihar, wanda Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya dauki nauyi. Wannan mataki na da nufin karfafa hadin kai a jam’iyyar da kuma tallata hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadin jihar. A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar Sanata Ahmed Malam Madori...
Maiyaki ya ce, “Gwamna Uba Sani kwanan nan ya ba da izinin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a karkashin rukunoni daban-daban. “Za a ci gaba da yin hakan a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin inganta harkar lafiya a jihar.” Maiyaki ya ci gaba da cewa, Gwamna Sani ya fifita harkar kiwon lafiya a gwamnatinsa, inda take gaba-gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5 November 10, 2025 Labarai Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta November 10, 2025 Labarai Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC November 10,...
Mazauna Millennium City a Jihar Kaduna sun zargi kamfanin wutar lantarki na Kaduna Electric da tilasta musu sanya mita da kuma ƙara farashin wuta ba tare da tuntuba ba. Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da MPH Estate, TUC Estate, Urban Shelter Estate, Yardan Allah Estate, Highfield Estate, Rahusa Estate, Danbushiya, Sabon Gari, Keke da Doka. Mazauna sun bayyana cewa an katse musu wuta na makonni saboda ƙin karɓar mitocin da kamfanin ya kawo. Sun ce matakin Kaduna Electric ya saba da umarnin Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC), wadda ta tanadi cewa dole a tattauna da al’umma kafin a yi canjin mita ko a sauya tsarin biyan kuɗin wuta. Mazauna sun kuma yi ƙorafi cewa kamfanin...
Kamaru: Jagoran ‘yan Hamayya Chiroma Ya Bai Wa Gwamnati Sa’o’i 48 Da Ta Saki Dukkanin Wadanda Aka Kama Bayan Tsabe
Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.” Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira ” Nuna wariya ta kabilanci.” Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.” A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%. Shi dai...
Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya ambaci cewa, Mutum daya ya kwanta dama, sadaniyyar harin wani jirgin sama maras matuki na HKI akan wata mota a garin al-yasariyyah,dake gundunar Saida, a kudancin kasar. Majiyar tsaro ta fada wa kafafen watsa labaru cewa, jirgin saman maras matuki ya harba makamai masu linzami guda 3 ne akan motar da hakan ya yi sanadiyyar konewarta baki daya. Dama dai ma’aikatar lafiya ta Lebanon din ta sanar da shahadar wasu mutane biyu sanadiyyar hare-hare biyu da Isra’ilan ta kai a kudancin kasar, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Tun da aka tsagaita wutar yaki a watan Nuwamba 2024, HKI take ci gaba da keta ta, ya kai dubbai. A wani labarin daga...
Kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana matukar damuwarta akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a cikin kasar Mali, tana mai yin Ishara da yadda ‘yan ta’adda su ka killace iyakokin kasar da hana shigar da muhimman kayan bukatun rayuwa na yau da kullum. Tarayyar Afirka ta kuma yi tir da yadda ake kashe farafen hula a kasar ta Mali da hakan yake haddasa rashin zaman lafiya da tsaro. Bugu da kari, tarayyar Afirkan ta nuna cikakken goyon bayanta ga al’umma da kuma gwamnatin kasar Mali da iyalan wadanda aka kashe. Kungiyar ta Afirka ta kuma nuna cewa a shirye ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukatuwa da shi a kasar ta Mali domin samun zaman lafiya. Kungiyar “Jama’atu Nusratul-Islam Wal Muslimin”...
Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027. “A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025...
’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa. Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa dandazon maharan sun yi dirar mikiya a garin ne ɗauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe tare da shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane. “Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska suna karya ƙofofi. Sun tafi da mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji majiyar. Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2...
Pars Today – Kimanin masu jefa ƙuri’a miliyan 1.3 na Iraki sun je rumfunan zaɓe jiya, Lahadi (9 ga Nuwamba). An gudanar da wannan zaɓen na musamman kwanaki biyu kafin babban zaɓen ‘yan majalisar dokoki na Iraki, wanda za a gudanar a ranar Talata ta wannan makon (11 ga Nuwamba). An ci gaba da gudanar da zaɓen har zuwa ƙarfe 6 na yamma agogon ƙasar, bayan haka aka rufe akwatunan zaɓe ta hanyar lantarki. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar da cewa an shirya cibiyoyin zaɓe 809, ciki har da akwatunan zaɓe 4,501, a faɗin ƙasar don ranar zaɓen musamman. A wannan zagayen zaɓen, ‘yan takara sama da 7,744 daga ƙungiyoyin zaɓe 31 sun tsaya takarar kujeru...
Pars Today – Jakadan Iran a Rasha ya sanar da cewa Tehran da Moscow sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Kazem Jalali, jakadan Iran a Rasha, ya rubuta a ranar Lahadi a dandalin sada zumunta na X cewa an cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Rasha don kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Ya kara da cewa wannan yarjejeniya ta samo asali ne daga tarurrukan da aka gudanar a ranakun 6-7 ga Nuwamba a Makhachkala tsakanin shugabannin tashoshin jiragen ruwa da na ruwa, manyan jami’an gwamnati, da daraktocin manyan kamfanonin kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen biyu. A cewar Pars Today, ya kara da cewa a lokacin wannan taron, an amince da tsarin da tsarin hadin...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi. A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a zaɓen 2027. Abdulmumin Jibrin ya sanar ta shafinsa cewa sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa. “Na samu kyakkyawar tarba daga dubban al’ummar mazaɓata ta Kofa, Bebeji, da ke Jihar Kano. “Taron ya yi ittifaƙin ficewa daga NNPP/Kwankwasiyya, mu koma APC, tare da goyon bayan Shugaba Tinubu ya yi wa’adi na biyu. An ƙara rage kuɗin aikin Hajjin...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu na musulmi. Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada muhimmancin inganta hulda da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da rabon ruwa daga kogin Harirud. Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza a watan da ya gabata, inda aka kashe mutane da dama a tashin hankali mafi muni tun bayan da Taliban ta kwace iko...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar a ranar Lahadi cewa adadin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen da aka gudanar ya kai kashi 82.42%, wanda ya tabbatar da sahihanci da kyakkyawan tsarin gudanar zaɓen, a cewar hukumar. Shugaban Hukumar Omar Ahmed, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa hukumar ta nuna daidaito da adalaci ga dukkan ‘yan Takara. Ahmed ya bayyana cewa hukumar ta sa ido kan tsarin zaɓe a duk faɗin jihohin ƙasar ta hanyar ƙungiyoyin da ke aiki, yana mai jaddada cewa sakamakon ya nuna jajircewar masu kaɗa ƙuri’a da kuma tafiyar da harkokin zaɓe cikin sauƙi da kuma sahihin tsari. A cikin wannan yanayi, mai ba da shawara kan harkokin shari’a na hukumar...
Ministan Lafiya na Lebanon Rakan Nasser Eddine ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, musamman a kudancin kasar, sunakara tsananta, yana mai jaddada cewa rikicin ba wai kawai ya takaita ga wani yanki ɗaya ba ne, lamari ne da ya shafi kowace gida a Lebanon.” A lokacin ziyararsa a birnin Hermel da ke arewa maso gabashin Lebanon, Nasser Eddine ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi shahada ya karu daga 23 zuwa 28 a cikin watan da ya gabata, yana mai jaddada cewa waɗannan shahidai suna da iyalai da dangi da ‘yan uwa, kuma dole ne ƙasa ta tsaya musu. Ya ƙara da cewa: “Dangane da wannan hari na Isra’ila a kan ƙasarmu, sojojin Lebanon ba...
Gwamnan yankin Darfur na Sudan, Bahreldin Adam Karamah, ya bayyana cewa shugabannin mayakan RSF sun aikata laifuka a El Fasher, yana mai jaddada cewa “ba za su iya ɓoye su ba.” A cikin wata sanarwa da ya fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Sudan (SUNA), Karamah ya fayyace cewa shawarar da Majalisar Tsaro ta Sudan ta yanke, wacce shugabanninta suka goyi bayanta baki daya, ta tabbatar da cewa “babu wani sulhu da masu kisan gillar al’ummar Sudan.” Ya kara da cewa, “Ba za mu yi sulhu a kan wannan kasa ba, kuma ba za mu bari a sauke tutarta ko a lullube ta a cikin laka tare da ta wulakanta ta ba.” Gwamnan Darfur ya nuna cewa rikicin da ake...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma. Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar. Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani. Ranar Foliyo Ta...
Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin Olympics. Ya ce, gasar wasanni ta kasa ita ce babban bikin wasanni mafi girma a kasar Sin. Kuma yankunan Guangdong, Hong Kong da Macao ne suka hada hannu wajen shirya gasar wasannin ta kasa karo na 15. Ana kyautata zaton cewa, wannan gasar wasannin ta kasa ba wai kawai za ta bayyana sabbin nasarorin da kasar Sin ta samu a sabon zamani ba ne, har...
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji November 9, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15 November 9, 2025 Daga Birnin Sin Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba November 9, 2025
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
Gwamna Namadi Ya Bukaci Asibitin Koyarwa Na RSUTH Ya Bada Fifiko Ga ‘Yan Asalin Jihar Yayin Daukar Ma’aikata
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
’Yan ta’addan Lakurawa sun kai hari sansanin Hukumar Kwastam da ke Maje, a Ƙaramar Hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi, inda suka kashe wani jami’i guda ɗaya. Wani mazaunin yankin ya ce ’yan ta’addan sun zo da yawa, inda suka fara harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, sannan suka ƙone sansanin jami’an kwastam. Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Ya ce, “Lakurawa sun zo da yawa, suna harbe-harbe ta ko ina. Sun ƙone sansanin kwastam tare da kashe wani jami’i.” Mai magana da yawun hukumar Kwastam a Jihar Kebbi, Muhammad Tajudeen, ya tabbatar da faruwar harin. Ya ce jami’an hukumar suna asibiti suna...
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu. Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Kangiwa. Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga “Na zo ne don jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici, amma dole ne mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu,” in ji shi. Gwamnan, ya ce gwamnati ta fara bincike don gano musabbabin rikicin,...
Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin da ke tsakanin Pakistan da Afghanistan wanda ya kara ta’azzara kwanan nan bayan fadan kan iyaka mai muni da ya faru. Abass Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, Mohammad Ishaq Dar, yau Lahadi, inda suka tattauna dangantakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Mista Araghchi ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yanzu tsakanin Afghanistan da Pakistan, yana mai jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, tare da taimakon kasashen yankin masu tasiri, don sasanta takaddamar da rage tashin hankali. A watan da ya...
Ministocin tsaro na kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun yunkuri anniyar kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa, wacce zata tunkari magance barazanar ta’addanci mai nasaba da kungiyoyin JNIM da ISIS a yankin Sahel. Kasashen sun bayyana hakan ne bayan wani taro da suka gudanar a Niamey karkashin jagorancin shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani da ministocin tsaron kasashen da ke kungiyar kawacen sahel ta (AES). Ministocin tsaro na Mali, Sadio Camara; Burkina Faso, Célestin Simporé; da Nijar, Salifou Mody, sun sanar da shawararsu ta hanzarta aiwatar da aikin rundunar hadin gwiwa ta AES. Shawarwarin da aka amince da su sun tanadi musayar bayanan sirri, da kuma hadin guiwa ta fanin ayyukan soji. Kasashen na fuskantar barazanar kungiyoyin ta’addanci da suka...
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da mummunan ta’addancin da aka aikata kan fararen hula a yankin El-Fasher na Sudan. Ofishin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ya yi gargadin cewa El-Fasher ya zama birnin makoki a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare masu muni, wanda hakan ya haddasa wahalhalu marasa misaltuwa. A cikin wani bidiyo da aka wallafa a dandalin sada zumunta na X, Li Fung, Wakiliyar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ta ce: “A cikin kwanaki goma da suka gabata, yankin El-Fasher ya kasance wurin da ake samun karuwar hare-haren ta’addanci. A cewarta, “an kashe daruruwan mutane, ciki har da mata, yara, da wadanda suka...
Shugaban reshen Akure na NBA, Mr. Friday Umar, wanda ya yi wannan kira, ya lura cewa “wani lokacin, yanke hukuncin masu karo da juna, suna tasowa ne daga bambance-bambancen ra’ayoyin alkalai” kuma ya amince cewa Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) tana ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yanayi. Ya ƙara da gargaɗin cewa, ya kamata a riƙa shigar da ƙara a inda aka yi laifi don kiyaye mutuncin shari’a. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Labarai Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9,...
Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati
Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar. Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su karbi albashi ba, idan su ka yi aiki alhali ayyukan gwamnati suna a rufe. Hukumar filayen jiragen sama ta tarayyar Amurka ce ta sanar da cewa masu aikin kula da zirga-zirgar jiragen sama a hasumiyoyin dake cikin filayane jiragen sama 25 sun dakatar da aiki. Daga cikin garuruwan da tsaikon aikin ya shafa da akwai Chicago, Sanfarancisco, New York, New Rock da kuma Atalanta. Tashar...
Wasu Karin kasashe takwas sun yi kira da a kama Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamine Netanyahu saboda laifukan yakin da ya aikata. Kasashen Turkiya, Norway, Italiya, Canada, Slovenia da Lithuania, sun bayyana cewa a shriye suke su kama fira ministan na haramtacciyar Kasar Isra’ila. A kasar Turkiya mai shiga da kara na birnin Istanbul ya fitar da sammacin kamo mutane 37 masu hannu a kisan kiyashin Gaza daga cikinsu da akwai Netanyahu, ministansa na yaki, Kats, da babban hafsan hafsoshin sojan ‘yan sahayoniya Iyal Zamir. A ranar 21 ga watan Nuwamba 2024 ne kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar da sammacin kamo Fira minista Netanyahu da tsohon ministansa na yaki Yoav Gallant saboda amfani da yunwa...
Shirin Majalisar Dinkin Duniya Na Samar Da Abinci ( WFP) ya fitar da gargadi akan cewa, yankin gabashin DRC yana fama da matsananciyar yunwa. Daraktar cibiyar ta WFP a kasar ta DRC Cynthia Jones ce ta yi wannan gargadin yana mai kara da cewa; Da akwai iyalan da suke tsallaken cin abinci, bayan da su ka sayar da kayan gidansu da kuma dabbobin da su ka mallaka.” Hukumar da yake kula da wadatar abinci ( IPC) ta ce da akwai mutanen da adadinsu ya kai miliyan 25 da suke cikin matakin karshe na yunwa, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3 da suke cikin hatsari. Hukumar ta MDD ta kuma ce, a halin yanzu mutane suna ta mutuwa saboda babu...
Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi. Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na Bagudo. ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu Sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Tafida, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar. Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin na zuwa ne daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin neman zaman lafiya...
Babban mai tattara zaɓe da hukumar ta turo, Farfesa Edogah Omoregie, kuma shugaban jami’ar Benin, shi ne ya karanta sakamakon na karshe a hedkwatar zaɓe da ke Awka. Nasarar Soludo ta nuna cewa APGA na ci gaba da daƙile siyasar yankin, tare da samun cikakken goyon bayan jama’ar jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9, 2025 Labarai Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza November 8, 2025
Charles Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA, ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba. Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi. Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445. George Moghalu na jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401. Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban...
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana. Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin...
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu. Da yake magana bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan ranar Juma’a, ya ce, “Idan aka habaka kasuwannin kan iyaka kuma ciniki da Pakistan ya ci gaba da bunkasa, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da kalubalen kan iyaka tsakanin kasashen biyu, domin mayar da yankunan kan iyaka zuwa cibiyoyin manyan ayyukan tattalin arziki zai rage fasa-kwauri da rashin tsaro, haka nan kuma zai share fagen...
‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan zaben makon da ya gabata. Hukumomi sun sanar da sunayen wasu mutane 9 da ake nema ruwa a jallo dangane da abubuwan da suka faru. Jam’iyyar Chadema da wasu mambobi na kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin dan adam da dama sun yi ikirarin cewa, jami’an tsaro sun kashe mutane sama da 1,000 yayin da suke tarwatsa zanga-zangar, alkaluman da gwamnati ta yi watsi da su a matsayin marasa tushe, amma kuma gwamnatin ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba. ‘Yan sanda sun sanya Gologowa da wasu mutane tara a cikin jerin...
Tsohon Shugaban Amurka Biden ya yi dirar mikiya kan shugaba Trump cewa; Ba wai kawai yana lalata Fadar White House ba ne har ma da dukkan al’ummar kasar Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya kan magajinsa Donald Trump, yana mai cewa: Shugaban na yanzu ba wai kawai ya kawo wani abin kunya ga Fadar White House ba ce, har ma ga dimokuradiyyar Amurka. CNN ta ambato Biden yana cewa: A lokacin wani taron Jam’iyyar Democrat a Nebraska a yammacin Juma’a a Omaha: “Biden na cewa, ya san Trump zai kawo wani abin kunya a kasar, amma bai sani ba shin dole ne ya amince cewa akwai wani abin kunya da ya riga ya faru.” Biden yana magana...
Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da masu ƙara suka zayyana sun haɗa cewa, ya danganta halittar Annabi SAW da ƙasƙantun halittu (‘Ya’yan Tumkiya, da Karya, da Ƙwarƙwata), sannan kuma ya taɓa alfarmar iyayen Annabi SAW wanda a cewarsu, hakan bai dace ba a alfarmarsa fiyayyen halitta. Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba tare da ɓata lokaci ba, ta miƙa koken ga Majalisar Shura ta jihar domin fayyace gaskiyar lamari. Majalisar Shura, ta bakin Sakatarenta, Shehu Wada Sagagi, a wani taron manema labarai da ta gudanar, ta tabbatar da cewa, za ta gudanar da cikakken bincike akan zargin da aka yi wa Malamin (Abubakar Triumph). Sannan kuma, za ta gayyaci masu ƙorafe-ƙorafe da kuma Malamin domin sauraron bayanansu....
Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin ƙasar nan. Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara don duba yadda aikin ke gudana, domin tabbatar da cewa ana sa idanu sosai, kuma ‘yan kwangila suna gudanar da aikin cikin inganci da nagarta. Ministan ya fara duba aikin tun daga Tungan Maje, Madalla, Zuma Resort, Sabon Wuse, Jere, Abuja Junction, Gwanin Gora, sannan ya ci gaba zuwa Zaria har zuwa Kano, inda aikin ke ci gaba yadda ya dace. Haka kuma,...
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun yi tattaunawa ta wayar tarho game da batun halin da ake ciki a yankin, inda suka mayar da hankali kan batun tsagaita wuta a Gaza da kuma yakin da ake yi a Sudan. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar a ranar Asabar, Abdelatty ya yi nazari kan ci gaba da kokarin da Masar ke yi na karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden da yarjejeniyar ta kunsa. Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniya zuwa mataki na biyu na shirin tsagaita wuta, wanda zai magance matsalolin siyasa da ayyukan jin kai domin samun...
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi November 8, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025
Kazalika, duk dai a jiya Jumma’ar, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da taron, Chen Binhua, mai magana da yawun Ofishin Harkokin Taiwan na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ya ce taron wanda ya gudana shekaru goma da suka gabata ya karfafa muhimmiyar rawar da Yarjejeniyar 1992 ta taka a matsayin ginshikin siyasa ta bunkasa zaman lumana a dangantakar bangarori biyu na mashigin tekun, kana matukar an ci gaba da amincewa da Yarjejeniyar 1992 kuma aka nuna adawa da batun “‘yancin kai na Taiwan”, to dangantakar bangarorin biyu za ta iya bunkasa cikin lumana kuma za a iya kara inganta muradun ‘yan kasa da ke bangarorin biyu na mashigin tekun. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga...
Wasu ’yan bindiga da Bello Turji ke jagoranta sun kai hari ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato da safiyar ranar Asabar. Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe mutum biyar, tare da jikkata wani ɗan sa-kai, sannan suka sace wasu mutum tara waɗanda mafi yawansu mata ne. Ban ɓata zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Kafin faruwar harin, wani mai ɗan gwagwarmaya a yankin mai suna Basharu Altine Guyawa, ya wallafa a kafafen sada zumunta inda ya yi gargaɗin cewa Bello Turji da tawagarsa suna shawagi a yankin Fadanar Tursa da Dorawar Madugu zuwa Dan Huntuwa ta gadar...
BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”. Somalia (1992–1994) Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s. A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya. Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida. Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen...
Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi ya zo na daya a duniya da maki 170.80 kuma yana mataki na 4 a bangaren Olympic, A gefe...
Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa. Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025 Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin
A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin. ’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP...
Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida. Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri. Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu A yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu. Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025 November 7, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku November 7, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka November 7, 2025
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci. Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock Barau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame...
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano: Haduwa da kawayen banza da kuma kuntatawa da wasu malaman suke nuna musu, saboda kin amincewa da su na bukatun da suke nema a wajensu. Da yawa iyayen ba sa tsayawa su saurari matsalolin ‘ya’yansu kan abin da ke damunsu a makaranta, da kuma rashin bibiyar karatunsu da abokansu. Iyaye su tabbatar da suna bawa yara kudi da kayan abincin da zai ishesu idan a makarantun kwana suke, sannan su tabbatar da tarbiyyar malaman da za su kai yaran nasu. Sunana Aisha Isah Gama (Mai Waka), Jihar Kano: A gaskiya abin da ke janyo wa baya wuce gurba tattun abokai, har da lefin malamai saboda malami ne za ka ga ya kulla...
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi. Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.” Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...
Kotun koli ta tarayyar Najeriya ta tsayar da ranar 20 ga watan nan na Nuwamba domin zama shari’ar shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara Nnamdi Kanu. Zaman shari’ar da za a yi zai mayar da hankali akan tuhumar ayyukan ta’addanci da ake zargin shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara din da aikatawa. An bai wa Kanu kwanaki shida a jere domin ya kare kansa akan zargin ta’addancin, sai dai bai iya yin hakan ba. A jiya Juma’a Kanu ya gabatar da nashi bayanin akan cewa; Ai daina daukar ta’addanci a matsayin laifi a Najeriya, domin an yi wata sabuwar dokar da ta maye gurbin tsohuwar da ake da ita akan hakan. Har ila yau Kanu ya ce babu wata madogara ta doka...
Yanda ake amfani da shi: A dan dumama man zaitun a wuta, kar ya yi zafi da yawa yanda zai kona fata. Sai a shafa a gurin da nankarwar ta ke. A yi hakan da safe da yamma a kullum. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ado Da Kwalliya Yadda Za A Magance Amosanin Baki October 4, 2025 Ado Da Kwalliya Hadin Tsumin Baure September 27, 2025 Ado Da Kwalliya Gyaran Fuska Da Laushin Fata August 30, 2025
Bisa ga imanin da yake da shi ya bayyana cewa “Ba za ka iya samar da zaman lafiya da bama-bamai ba; sai dai ka gina shi da amana,” ya kaddamar da abin da yanzu ake kira ‘Samfurin Zaman Lafiya na Kaduna’. Tsarin Hadin Gwiwa:r Gwamnatin Kaduna Da ofishin ONSA A tsakiyar wannan sauyi akwai hadin gwiwa mai karfi a tsakanin Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Gwamnatin Jihar Kaduna. Tare suka kafa kwamitin fasaha na hadin gwiwa wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki, masana halayyar dan’Adam, da shugabannin kananan hukumomi, wannan tawaga ba ta zo da tankoki ko jiragen yaki ba, ta zo da tausayawa, tattaunawa da bayanai. A babban aikinsu na farko, ’yan...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: A bayyane yake cewa Amurka tana da hannu dumu-dumu wajen wuce gona da iri kan kasar Iran Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya mayar da martani ga amincewar da shugaban Amurka ya yi na daukar alhakin harin da sojojin Sahayoniyya suka kai wa Iran, yana mai cewa: “Tun daga farko a bayyane yake cewa Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran.” Baqa’i ya rubuta a shafinsa na X-Platform: “Shin kuna tuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 cewa: Amurka ba ta da hannu a harin da ‘yan Sahayoniyya suka...