Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Matakin Amurka Na Dakatar Da Ka’idar Fadada Jerin Wadanda Kasar Ta Takaita Fitar Wa Kayayyaki
Published: 12th, November 2025 GMT
Amurka ta dakatar da ka’idar fadada jerin wadanda kasar ta takaita fitar wa kayayyaki a kwanan nan, wani muhimmin mataki ne da Amurkan ta dauka a fannin cimma matsayar da aka amincewa, yayin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin Sin da Amurka a Kuala Lumpur. Kuma kasashen biyu za su ci gaba da tattaunawa kan shirye-shirye bayan dakatarwar shekara guda.
Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin ya bayyana hakan ne kan tambayar da ’yan jarida suka yi masa game da matakin na Amurka na dakatar da ka’idar fadada jerin wadanda kasar ta takaita fitar wa kayayyaki, a yayin taron manema labarai na jiya Talata.
Kakakin ya kara da cewa, Sin tana son yin aiki tare da Amurka, ta hanyar bin ka’idojin girmama juna, da kuma gudanar da shawarwari bisa daidaito, don karfafa tattaunawa da musayar ra’ayi, da warware sabanin ra’ayin ta hanyar da ta dace, da kuma samar da yanayi mai kyau na inganta hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasashen biyu, da kuma tabbatar da tsaro, da kwanciyar hankali na tsarin masana’antun samar da kayayyaki na duniya.
ADVERTISEMENTAmurka ta sanar da dakatar da ka’idar ne tun daga ranar 10 ga watan Nuwamban 2025 zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba na 2026. Kuma a wa’adin, kamfanonin da Amurka ta ayyana a “Jerin Sunayen Kamfanoni” da ta kakabawa takunkumi, da kamfanonin da suka yi alaka da su, masu rike da fiye da kashi 50% na hannun jari, ba za su fuskanci karin takunkumin fitar da kayayyaki ba. (Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Jihar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Kan Laifin Rashin Ɗa’a
An umarci shugaban karamar hukumar da ya mika harkokin majalisar ga mataimakiyarsa, Mrs Victoria Okolo, har sai an kammala binciken.
Majalisar ta bai wa kwamitin binciken wata daya don kammala aikinsa tare da bayar da rahoto kan matakin da ya dace.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA