Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand
Published: 14th, November 2025 GMT
Da safiyar yau Juma’a 14 ga watan Nuwamba, a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sarkin Thailand Maha Vajiralongkorn wanda yake ziyarar aiki a nan kasar Sin.
Yayin ganawar tasu shugaba Xi ya ce, sarkin ya sanya kasar Sin a matsayin babbar kasa ta farko da ya kai ziyara. Hakan ya tabbatar da kasancewarsa sarkin Thailand na farko da ya taba ziyartar kasar Sin, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Thailand, wanda hakan ya shaida muhimmancin dangantaka tsakanin kasashen biyu, da kuma dankon zumuncin dake akwai tsakanin Sin da Thailand.
A nasa tsokacin kuwa, sarkin ya ce Thailand na fatan koyon darussa daga kwarewar ci gaban Sin, da fadada hadin gwiwa a fannoni daban-daban da Sin, da kuma habaka huldar al’adu, don kara karfafa abota tsakanin Thailand da Sin. (Amina Xu)
ADVERTISEMENTShareTweetSendShare MASU ALAKA
এছাড়াও পড়ুন:
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15 November 11, 2025
Daga Birnin Sin Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa? November 11, 2025
Daga Birnin Sin Jakadun Kasashen Waje: Shirin Raya Kasa Na 15 Na Sin Na Dauke Da Kyakkyawan Sako November 11, 2025