Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
Published: 13th, November 2025 GMT
Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi da kuma samar da nagartattun hanyoyin warkarwa ta yadda jami’an lafiya za su nakalci sahihin zabin da za su yi amfani da shi wajen magance matsalolin rashin haihuwa mabambanta, da kuma tabbatar da cimma muradun samun haihuwar.
Tabbas, kamar yadda kasar Sin take da sa kwazo cikin abubuwan da take yi, ina da yakinin za a zurfafa wannan bincike domin cike gibin da aka gano don taimaka wa share hawayen iyaye masu neman haihuwa ruwa a jallo. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Ban da wannan kuma, game da batun cewa kasashen kungiyar EU suna shirin cire na’urorin kamfanonin sadarwa na kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin suna aiwatar da ayyukansu bisa doka a nahiyar Turai na dogon lokaci, wadanda suka samar da kayayyaki da hidimomi masu inganci ga jama’ar Turai, tare da samar da muhimmiyar gudummawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da samar da ayyukan yi a nahiyar. Kasar Sin ta kalubalanci kungiyar EU da ta samar da yanayin gudanar da ciniki cikin adalci da rashin nuna bambanci ga kamfanonin kasar Sin don magance wargaza amannar da kamfanonin suka yi wa nahiyar Turai kan zuba jari. (Zainab Zhang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA