Matan sojojin da suka mutu na neman agaji
Published: 11th, November 2025 GMT
Ƙungiyar Tsofaffin Sojoji ta Najeriya ta bukaci gwamnati da ta ɗauki matakai na gaggawa wajen inganta rayuwar mata zawarawan sojojin da suka mutu a bakin aiki tare da ba su goyon bayan da ya dace.
Sabon shugaban ƙungiyar a Jihar Bayelsa, Mista Baratuaipre Allison-Alamini, ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan rantsar da shi.
Ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙari ganin cewa muryar zawarawan sojojin da suka rasu ta isa inda ya kamata, ta yadda za a inganta rayuwarsu da kuma tabbatar da samun tallafin da suka cancanta.
Allison-Alamini ya kuma sha alwashin ba da muhimmanci ga walwalar tsoffin sojoji a jihar, tare da gode wa mambobin ƙungiyar bisa yadda suka ba shi amanar shugabanci.
Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata ’Yan bindiga sun sace mata 5 a KanoZaben ya gudana ne ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya, ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanar Bello Kaya, tare da wakili daga ofishin sakataren gwamnatin jihar.
A yayin zaben, Odon Alfred ya sake lashe mukamin mataimakin shugaban kungiyar ba tare da hamayya ba, yayin da Mista Amiekumo Angozi ya zama ma’ajin kungiyar.
Shugaban kwamitin zaɓe, Mista Aghomo Samson, ya bayyana zaɓen a matsayin mai cike da kwanciyar hankali, gaskiya da amana. Ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa halin natsuwa da suka nuna kafin, yayin, da bayan gudanar da zaben.
Ya ya buƙaci sabbin shugabannin da su jagoranci ƙungiyar cikin adalci ba tare da rikici ba, tare da hada kan dukkan matakan kungiyar a cikin dukkan al’amuransu.
Wakilin sakataren gwamnatin Jihar Bayelsa, Ogori Raymond, ya buƙaci sabbin shugabannin su gudanar da mulki mai inganci, gaskiya da gaskatawa, wanda zai ƙarfafa zumunci, hadin kai, adalci da daidaito a tsakanin mambobin kungiyar.
A nasa bangaren, wakilin shugaban kasa na majalisar ƙungiyar tsoffin sojoji ta Najeriya, Mista Toye Dele, ya sake tabbatar da ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ci gaba da kula da walwalar tsoffin sojoji da kuma kiyaye gado da tarihi na rundunar sojojin Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: zawarawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC
Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar.
Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan AnambraOyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar.
“Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko siyasa ba ne. Abin da muke buƙata yanzu shi ne haɗin kai don kare ƙasarmu,” in ji shi.
Ya shawarci ’yan adawa da su yi hattara da kalamansu, tare da kira ga manyan hafsoshin soji da su tabbatar da amincewar da aka ba su ta hanyar yin aiki tuƙuru wajen murƙushe ’yan ta’adda.
Oyintiloye, ya kuma roƙi gwamnatin Amurka da ta taimaka wa Najeriya da bayanan leƙen asiri da kayan yaƙi maimakon turo sojojinta, inda ya ce hakan na iya ƙara dagula lamarin.