Aminiya:
2025-05-01@10:03:03 GMT

Bom ya fashe a Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri

Published: 1st, May 2025 GMT

Ƙarar wani abin fashewa mai ƙarfi ya girgiza Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri a Jihar Borno da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan.

Tashin abin fashewan ya jefa mazauna unguwannin Polo, Fori, GRA da Jami’ar Maiduguri cikin tashin hankali.

Ƙarin bayani na nan tafe.

.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: abin fashewa Barikin Sojoji na Giwa

এছাড়াও পড়ুন:

Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno

Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.

Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47 An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal

Majiyoyi, ciki har da wani babba soja, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da harin na baya bayan da safiyar ranar Talata.

Sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta tafiya Gamboru Ngala ne daga Rann lokacin da suka isa inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka ɗana bam ɗin.

Bayanai sun ce baya ga mutum 26 da suka mutu, ƙarin mutum uku sun ji munanan raunuka.

“Mun tura wasu masu ba da agajin gaggawa inda lamarin ya auku domin kwashe mutane tare da tabbatar da tsaron sauran fararen-hula a wurin,” kamar yadda wata majiyar sojin da ba ta yarda a bayyana sunanta ba ta shaida wa Anadolu.

Ali Abass, wani ganau wanda ke tafiya a kan hanyar a lokacin da lamarin ya auku, ya ce sojojin da ‘yan sa-kai sun kai waɗanda suka jikkata wani asibiti. Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ‘yan’uwansa na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Harin yana zuwa ne yayin da hare-hare ke ƙara ƙaruwa a yankin Tafkin Chadi, inda ‘yan ta’addan Boko Haram ke ƙara ƙaddamar da hare-haren bama-bamai da kwanton-ɓauna kan motocin fararen-hula da na sojoji.

An ba da rahoton hare-hare irin wannan a ranakun 21 ga watan Maris da 12 ga watan Afrilu. Kawo safiyar ranar Talata dai, jami’an tsaro a Borno ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara Ta Tashi A Barikin Sojoji A Borno, Bama-bamai Sun Fashe
  • Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
  • An kashe mafarauta 10 a Adamawa
  • Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran
  • Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato 
  • Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno
  • Sojoji Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu 32 A Katsina
  • Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno
  • Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal