2025-09-17@22:14:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4401

«yan kasuwa»:

    Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar.   Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin...
    Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙara kuɗi zuwa Naira miliyan 1,000 (wato miliyan 500 da aka ware a baya da ƙarin miliyan 500) domin magance matsalar yunwa a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa ‘yan jarida  biyar a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai a zirin Gaza, yana mai bayyana wannan laifi a matsayin shaida ta yanke kauna daga  gwamnatin da duniya ta juya mata baya saboda munanan laifukanta. A...
    Ministan tsaron kasar Italiya Guido Crosetto ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila ta fita hayyacinta a yakin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, yayin da kuma yake nuni da cewa Italiya a shirye take ta bi sahun kasashen duniya wajen kakaba wa Isra’ila takunkumi. A cikin wata hira da jaridar La Stampa ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Samun matasan da ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’ummominsu abu ne da ba kasafai ake samu ba a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bayar da gudunmawarsu wajen ci-gaban al’ummarsu. NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce yaki da talauci muhimmin mataki ne na hanzarta ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Ya bayyana haka ne a lokacin shirin gwamnatin jihar mai taken “Gwamnati da Jama’a” wanda aka gudanar a karamar hukumar Ringim. Malam Umar Namadi ya jaddada muhimmancin horas da matasa...
    Yanzu haka mutane huɗu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya, bayan sun jikkata a wani mummunan haɗarin da ya haɗa da tankoki biyu a ƙauyen Kake, yankin Dan Magaji, kan hanyar Zariya–Kaduna. Haɗarin ya jawo mummunar gobara bayan haɗuwar motocin. Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa...
    Sojoji sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki kan maboyar ’yan ta’addan da suka addabi manoma da mazauna wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya. Bayanai sun ce dakarun sojin na sama da ta ƙasa, waɗanda ke ƙarƙashin rundunar Operation Fasan Yamma da ke sintiri a Arewa maso Yamma domin kawar...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma. Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fitaccen masanin tattalin arziki dan kasar Birtaniya John Ross, ya ce ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin ya karu da kaso 5.3 bisa dari a mizanin shekara, cikin rabin farko na shekarar nan ta 2025, wanda hakan ke nuni ga ingancin tushen tattalin arzikin kasar. Ross, wanda ya bayyana hakan a baya-bayan nan,...
    A safiyar wannan Litinin ɗin ce aka wayi gari da wani mummunan hatsarin tankoki biyu na dakon iskar gas a Zariya, inda direba ɗaya kacal ya tsira da rai, yayin da wasu da dama suka ƙone ƙurmus. Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safe, a kusa...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya. Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga...
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da haɗin gwiwar Gavi da ke taimakawa wajen samar da rigakafi, sun mika na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana g Gwamnatin Jihar Kano domin amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 28 da nufin ƙarfafa rigakafin yara da...
    Birnin Karbala mai tsarki na sa ran karbar bakwancin masu ziyara sama da miliyan 4 daga kasashen ketare domin gudanar da juyayin Arbaeen Jama’a masu dimbin yawa na tururuwa zuwa birnin Karbala mai tsarki daga Najaf domin halartar yuyayin ranar Arbaeen a cikin tsauraran matakan tsaro da na hidima. Wakilin Al-Alam da ke kan titin...
    Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa...
    Wani mutum ya ba da kyautar motarsa da ita kadai gare shi ga wani mai jan baki (alaramma) saboda ƙwarewarsa a haddar Al-kur’ani. Malam Yusuf Ɗan-Birni, ya kyautar da motar ce a taron wa’azin wata-wata da Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta shirya a garin Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya....
    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe wani fitaccen dan jarida na kafar yada labarai ta Al Jazeera Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa hudu a wani hari da ta kai Gaza. Isra’ila ta zarge shi da kasancewa wani jagora na Hamas sannan ta ce ta hallaka shi saboda irin rahotannin da yake bayarwa masu...
    ’Yan ta’adda sun kashe mutum 24 tare da sace wasu akalla 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara. Kungiyar Al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hare-haren da suka kai kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban. Ta bayyana...
    A ci gaba da gudanar da bukukuwan makon shayarwa da nonon uwa na duniya, asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya shirya tarurruka a Kano tare da hadin gwiwar U-Reporters da sauran kungiyoyin matasa domin wayar da kan al’umma kan amfanin shayarwa.   An gudanar da gangamin a lokaci guda a...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane shida da ake zargin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Doma da ke jihar.   Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai...
    Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare.   Kungiyar AGILE da ke Jihar...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta karfafa matakan tsaro a yankin Babanla biyo bayan harin da wasu da ake zargin mahara ne suka kai musu, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda Adejumo Wasiu.   A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun...
    Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen ruwan sama mai karfi da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 15 na Arewacin Najeriya da wasu wurare 68, a cikin kwanaki biyar masu zuwa. Wannan gargadi ya fito ne daga Cibiyar Lura da Gargadin Ambaliya ta Kasa, karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, inda aka bukaci hukumomi da al’umma...
    Sanarwar ta zayyana wasu fitattun garuruwa da al’ummomin da ka iya fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da suka hada da Jimeta, Mubi, Keffi, Kafanchan, Birnin Kebbi, Minna, Gusau da Sakkwato.   A cikin jihohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa da aka fi tsammanin ambaliyar za ta yi kamari, ga su guda...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Damina lokaci ne da ɗan Adam yake matuƙar bukata. Da za ta yi jinkiri, sai a ga hankalin kowa ya tashi. A lokaci guda kuma, yadda damina kan hana wasu harkoki gudana kan jefa wasu mutane cikin wani irin yanayi. NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya  yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.” A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar  Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada...
    “Na taɓa zama abar kwatance, musamman a ɓangaren da shafi kuɗi, suna, girmamawa, amma kuskuren da na yi ya zama dalilin da yasa masana’antar ta juya min baya, sakamakon babu abin da na iya ko na sani face; harkar ta fim. Halin da ake ciki yanzu, babu wani tallafi, babu aikin yi, akwai lokacin da...
    Rahotanni daga sojojin da ke mulki a Mali, sun ce sun kama wasu sojoji kusan 30 da ake zargin suna shirin kifar da gwamnati ƙasar. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa cikin waɗanda aka kama akwai Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti da ke tsakiyar ƙasar. Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno...
    Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk Lokaci wani abu ne da yake nuna yanayi a kodayaushe, sannan yake bada damar aiwatar da abubuwa masu kyau da mararsa kyau a rayuwa. Haka kuma yanayi ne da yake bada damar rayuwa a cikin daƙiƙu, mintuna, da kuma, awowi, ranaku, makonni dakuma shekaru. Ana amfani da lokaci...
    Sojojin HKI sun shiga yankuna da dama a lardin Qunaitara na kasar Siriya a Jiya Asabar. Inda ta kafa shingaye a kan tituna a wasu garuruwa a lardin suka yi ta binciken ababen hawa, kafin su janye daga baya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, HKI tana shirin mamayar wadan nan...
    Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza, ba ni da mota ko ɗaya; ya sa idan na yi waccan maganar sai wasu su riƙa nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai, domin kuwa da a ce sun san wane ne Mai Dawayya a shekarun da suka gabata, da ba su yi wannan magana...
    Hukumar Shari’a ta Jihar Borno ta ƙara wa ma’aikatanta 97 girma bayan wani taro na kwanaki huɗu da ta gudanar a Maiduguri. Muƙaddashin sakataren hukumar, Saleh Khala Jidda ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa cewa ma’aikatan sun samu ƙarin girma ne saboda ƙwazonsu. EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo  ’Yan bindiga...
    Wakilan LEADERSHIP sun lura cewa yanzu ana amfani da wasu daga cikin waɗannan ofisoshin hulɗa da jama’a na Jihar Legas a matsayin matsugunin ‘yan kasuwa na da masu safarar barasa. Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa jami’an tsaro da masu kula da waɗannan gidaje suna hayar wasu sassan gine-ginen da daddare don yin...
    Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman...
    An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu...
    Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba...
    A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League. Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan...
    Gwamnatin jihar Kano ta amince da korar wasu manyan mataimaka na musamman (SSAs) ba tare da bata lokaci ba, sakamakon zarge-zargen da wasu kwamitocin bincike suka yi na gudanar da bincike kan wasu laifuka.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar.   A wani...
    Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birnin Tel Aviv na Isra’ila ranar Asabar, domin yin kira da a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin Isra’ila ta lashi takobin faɗaɗa rikicin tare da ƙwace birnin Gaza. Masu zanga-zangar da ke riƙe da hotunan waɗanda har yanzu ake garkuwa da su a...
    Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ta dauki dan wasan gaban Liverpool, Darwin Nunez, kamar yadda kungiyoyin biyu suka tabbatar ranar Asabar. Masu ruwa da tsaki a harkar tamaula na ganin wannan matakin za bai wa zakarun Premier League damar sake mika tayin neman dan wasan gaban Newcastle, Alexander Isak. ASUU na shirin sake tsunduma yajin...
    Wani lokacin, yanayin shekaru da Jinsin Jini ne ke fayyace irin girma ko ƙantantar Ƙwan da Kajin za su yi. 2- Wajen Kwana: Kajin na buƙatar a tabbatar da ana samar musu da wadataccen ruwan sha a ɗakunan kwanansu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutuka da rage musu wahala da cunkoso da...
    Kyari ya ce, a yanzu ana noma Waken Soya da ya kai kimanin tan miliyan 1.35, wanda kuma buƙatar da ake da shi a ƙasar ya wuce tan miliyan 2.7. Ya sanar da cewa, wanan tsari zai kuma amfani tattalin arziƙin ƙasar da ƙara samar da ayyuakn yi da kuma ƙara haɓaka samar da wadataccen...
    Yayin ziyararsa a kasar Indiya kwanan nan, shugaban kasar Philippines ya bayyana cewa, idan Sin da Amurka suka yi taho-mu-gama kan batun yankin Taiwan, Philippines ba za ta iya killace kanta daga ciki ba. Irin wannan furucin nasa yana da ban mamaki, wanda ya saba da alkawarin da Philippines ta yi na tsayawa ga manufar...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), ta yi gargaɗi cewa za ta iya sake tsunduma yajin aiki saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗauka. Shugaban ƙungiyar, Christopher Piwuna, ya ce gwamnati ba ta kula da walwalar malamai, ba ta samar da kuɗaɗen gudanar da jami’o’i yadda ya kamata, kuma ba ta aiwatar da...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar.   Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai...
    Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno. A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann. Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya yabawa yan jarida musamman a khidimar da suka gabatar a yakin kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a lokacinda ya kai ziyarar ganin ido a cibiyar hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a nan birnin Tehran....